baiwa mata a matsayin wani magani na karin lafiya, ko idan mace ta zo ta ce tana ciwon ciki yayin period sai su bata shi a matsayin maganin warkar da ciwon cikin, idan kin sha zaki yi ta fama da ciwon cikin ne, amma fa a farko in kin sha zaki ji saukin ciwon cikin, daga baya bayan kwanaki sabon ciwon ciki zai ɓallo maki mai zafi, da kin zo asibiti zasu ce maki mahaifarki ta samu matsala sai dai a yanke! Ba zaki kawo komai a ranki ba, zaki aminta a cire maki mahaifarki saboda a rabaki da ciwo.
Ministern da aka baiwa wannan kwamgila a kan Miliyan tamanin aka sayi kowani mahaifa a wajensa, shi kuma ya cewa likitoci in sun samu mai sayar da mahaifar ya saya miliyan hamsin, su kuma Dr ɗin suna saye miliyan 30 idan kin yarda zaki sayar, kasuwanci kan kasuwanci kuke ji.
To wasu matan fa mazansu ake magana da su, wani da ya kawo matarsa asibiti za'a jasa jefe, a shirya a kuma kwaɗaita mashi kuɗin, idan likitocin sun ga ɗan kauyene ma basa ce mashi saya zasu yi, sai su ce ciwo ne, ya aminta a cire maki, wani mijin kuma azzalumi ne, bai gama sauke maki hakkinki na aure ba, zai cutar dake ya sayar maki da mahaifa ba tare da kin sani ba, idan ya shirya da likitocin kan zai sayar masu zai karɓo wannan maganin ya baki, da kinsa zaki fara ciwon ciki, idan zai kaiki asibiti wannan asibitin da suka gama cinikin zai kai, already ya karɓi kuɗin mahaifarki 30 million baki sani ba, sun san komai Doctors ɗin, kina zuwa zaace aiki za'ayi maki, daga nan a cire maki mahaifa ba tare da kin sani ba, sai dai ki ga kin daina haihuwa, kuma ba zai taɓa barinki ki je wani asibitin ba, sai dai ya dinga cewa ki je wannan asibitin da aka maki aiki sun fi kwararrun likitoci, dan bakinsu ɗaya.
Ya ilahi, sun fi yi wa matan kauye da basu san komai ba hakan, kun san dai manya matan masu kuɗi basa zuwa asibitocin gwannati ai, a kan mu talakawa abin yake karewa, babu abin da ya fi taɓa mun zuciya irin mazan dake zaluntar matansu su sayar masu da mahaifa ba da izininsu ba, ya ilahi, wlh da babu lahira akwai matsala, amma Alhamdulillahi tin da akwai hisabi, amma bin da ciwo.
Meyasa yanzu abu kaɗan mahaifar mace ya samu matsala? Why? Meyasa zata haihu ace ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai a mata Cs? Why? Meyasa ciwon da bai zo a da ba sai yanzu za'a ce mahaifarta ta lalace ba zata sake haihuwa ba gara a cire mata? Meyasa dikka hakan sai a kanmu mata? Me laifinmu? Wani irin cutarwa ne wannan?.
Idan an samu miji mara imani ya sayar dana matarsa bata sani ba, wani ma yaya ne mara imani yake sayarwa kanwarsa, matan kauye basu san komai ba haka za'a cutar da su daga zuwa asibiti, ace basu da lafiya sai an masu aiki, daga nan a sace masu mahaifa, AVARIS suna cikin musifa babba, ƴan mata ma ba tsira suka yi ba, wani saurayin mataccen zuciya ne da shi, ya yaudareki ya kaiki a cire maki mahaifa, ya sayar ya yi kuɗi ya gudu ya barki ya nemi wata budurwar wacce take da mahaifar da zata haifa mashi yara in sun yi aure! Ya ilahil alamina, sabuwar musifar dake danno kai a AVARIS kenan.
Jama'a ku ji tsoron ALLAH, maza ku tina akwai lahira, akwai mutuwa, meyasa zaku sayar masu da abin da ALLAH ne ya basu ba ku ba? Meyasa zaku cutar da rayuwarsu ta haka? Mata masu sayarwa da kansu ku ji tsoron ALLAH, ku tuna cewa ALLAHN da ya baku a ranar lahira sai ya tambayeku komai da ya baku, wani amsa zaki bawa UBANGIJINKI ranar lahira? Dama ya baki dan ki sayar ne? Kin san me za'ayi da mahaifar ne da kike sayarwa? Kuɗin banza mai karewa, baki san kuɗin haram bashi da albarka ba ko? Maza! Maza! Maza!!.
Ni ban ce komai ba, amma shawara da kirana ga mata, dan girman ALLAH dik asibitin da zaki je, kome aka ce za'ayi maki ki ɗauki waya ki kira ɗan uwanki namiji, ya zo ya tsaya maki, duniya ba abin yarda bane, idan kina da wa ko kani ya tsaya a kanki dik abin da za'ayi a yi a gabansa, ba ruwanki da cewa mijinki da ƴan uwansa suna nan, ke baki da ƴan uwa ne? Idan ta kama an ce lallai sai an cire maki mahaifar ne to idan an cire ki ce su baki kayanki ki tafi da shi, kada ki yarda ki barshi a asibiti, ko sun ce maki jefar da shi zasu yi dan ciwo ne ki ce e su baki kayanki, wlh gara ki je ki tona rami a gidanki ki binnesa kina ganin ramin kullum akan ki bar masu, baki san me suke yi da shi ba, dik abin da aka yi da shi ba zai canza daga sunan mahaifarki bane!
Ban faɗa haka dan rashin yarda ya shiga tsakaninku da mazajenku ba! Ku yi hankali ne kawai, kada ki yarda da zuwa asibiti guda ɗaya ana duba lafiyarki, idan an yi maki aiki ne bayan kin samu lafiya jeki wani asibitin daman a maki scanning ki tabbatar da lafiyarki, duniyar yau ta zarce dik yadda kuke tinanin, abin ya fi karfinmu ya fi karfin shuwagabannin AVARIS! Dan abin daga sama yake, ALLAH ne kawai zai iya dafa mana ya kawo mana karshen wannan musifa, amma hakan ba zai faru ba sai mun tashi tsaye, mu kare kanku sai mu nemi UBANGIJINMU da ya taimaka mana.
Gabaɗaya WS-HOSPITAL ina typing ɗin labarin ɓangaren ina kuka, wlh har cewa mahaifiyata na yi zan jingine labarin nan saboda tausayin dake cikinsa ya yi yawa, mamana ta ce idan na rubuta zata yi farinciki da hakan, kuma ta umarceni da kada na rage ko A daga cikun ilimi da sanin da ALLAH ya bani, ta ce in daure taimakon alumma zan yi, alƙalami ya fi takobi! ALLAH yana tare dani, ta kara mun kwarin gwiwa sosai, kullum idan ina typing part ɗin sai na ce mata ina jin kamar ba zan iya ba zan jingine labarin, ta ce ta sanni zan iya in dage! The thing is very touching heart, emotional, har tsoron shiga cikin labarin in zayyana komai nike ji! I need your prayers.
Mutanen AVARIS suna buƙatar addu'arku, yadda aka horasu da yunwa da wahalar nan kuna tunanin ba zasu karɓi wannan aiki gadan-gadan bane tin da kowa yana son lallai sai ya yi kuɗi? Matan AVARIS yanzu kuma sun shiga uku, mahaifarsu ya zama kuɗi, shikena a kuma, yanzu kowa asibiti ka leƙa za'a ce aiki ake mata, ALLAH ka shige mana gaba ka karemu daga dikkan wata musifa.
Wannan shi ne hanyar da su Dr James suke bi dan samun mahaifar mata, tin da kuma kuka ga sun tsuga mashi kuɗin har kimani miliyan tamanin a wajen sayensa fa to ku sani bakaramin abu suke yi da shi ba, ba karamin kuɗi suke samu ba, amma koma menene idan muka shiga cikin labarin zaku sani.
Yanzu sai kewaye duniya suke suna raba wannan buƙata tasu ta a kawo masu mahaifa zasu saya, nasan maza masu matattun zuciya tuni zasu karɓa, matanma wasu da basu san ciwon kansu ba da kansu zasu karɓi kuɗin, ni damuwata shi ne idan aka basu mahaifar abin da zasu yi da shi, kun dai san ba zasu zuba makudan kuɗi a ƙan karamin abu ba ko? Babba abu ne!.
---------------------------
Dr Kamal ne ya ce. "Yunwa ya cinye kowa ba dole su sayar ba, gwamnatin Avaris bata son biyan ma'aikatan lafiyar government hospital ɗinta albashinsu, basa son sauke hakkinsu, kasar ga yunwa da wahala dole su sayar a".
Sipping na drink ɗinsa Dr Mark ya yi tare da cewa. "Basu da zaɓi ne, dole su sayar"....... Dr James dai rufe files ɗin ya yi tare da ɗauko wani file ɗin..... "Muna da contract har uku fa a shekarar nan, dole mu mayar da hankali, sannan batun project na PC ɗin nan, daga sama an hura mun wuta sosai, yakamata mu mayar da hankali, a nan da wattanni shidda zuwa takwas mu kammala project ɗin nan mu ci kuɗinsa"................... Miƙewa Dr Kamal ya yi tare da cewa. "We have to go to section D dan duba wancan project ɗin, yanzu ɗayar project ɗin nan zamu kammala, na bawa Maya document na aikin, 24h garesu, dan haka mu bar wannan zancen sai jibi idan mun samu feedback daga garesu".
Na'am suka yi da zancensa, ajiye cup na drink ɗinsa Dr Mark ya yi, kusan a tare suka miƙe suka fito ta kofar office na Dr James, daga nan suka fito izuwa section D. Suna tafiya a natse amma cikin zafin nama. Dik in da suka wuce sai nurses sun duƙa sun gaidasu.
Kai tsaye cikin section D suka shiga, rabuwa suka yi, suka fara kewaye a wajen suna duba dashen da suka yi! Suna bi suna ɗaukar rahoto da kansu, komai na tafiya daidai, halittar da suka dasa cikin mahaifar har sun fara motsawa tamkar yaro na motsi a cikin uwa, karku manta sai da ya zama embyro suka dasa shi a cikin mahaifar.
Bari in ɗan yi maku karin haske a wannan waje kafin mu wuce gaba dan kada ruɗewar tai maku yawa, naga dayawa sun fara ruɗewa tin ba'a je komai ba, to zan buɗe maku haske kaɗan. Nasan kun fahimci cewa waɗan nan kwayaye da suka dasa a cikin mahaifa a page ɗin jiya kun fahimta yara aka dasa, to yara suke kyankyasa da waɗan nan mahaifa, suna haɗa sperm na ɗah namiji da kwayayen mace su kyankyashe yara. Sai dai kuma idan suka kyankyashe waɗan nan jarirai basa wuce watanni uku a wannan asibiti, wasu jariran a ranar da aka fito dasu daga cikin mahaifar a ranar ba'a sake ganinsu, wasu suna kai wata ɗaya a wajen, wasu suna kai wata biyu har su fara wayau suna shan madara maimaikon nonon uwa, amma basa taɓa haura wata uku iya wuya, kuma abin mamaki kullum suna cikin kyankyasan yaran ne, dik wata suna cire kwan halittar mace ai kun gani, to me suke yi da uban yawan jariran da suke kyankyasar nan? Ina ake kaisu?.
Baku yi mamakin yadda na ce maku nurses na asibitin dik shekarunsu ɗaya ba, watau 18 years ba? To ai dik ta wannan hanya aka kyankyashesu, suka renesu, suka basu ilimin likitanci, sannan waɗan nan ƴan mata da ake cire kwan haihuwarsu dik wata ku sani suma a nan aka kyankyashesu musamman aka killacesu dan a rinƙa cire kwayayyensu.
Na ji wasu readers suna cewa basu da hankali suka yarda ana cire masu kyan haihuwa, to jama'a a lafa haka nan, suma ƴaƴan kwalbar haihuwa ce da aka kyankyasa ba ƴaƴan mama da baba ba, basu da kowa sai ALLAH, suna dai da azzaluman ubanunsu da suke bada sperm ɗinsu a kyankyashesu, dik namijin da zai bada sperm ɗinsa a wanna harka shi ne babban azzalumi kwai ba zai bada yaro ba sai an haɗa da sperm, to masu bada sperm nasu sun fi kowa laifi, su suna can suna jin daɗi cewa maniyinsa ma saya ake yi a basu kuɗaɗe, a yaudaresa da cewa ai man shafawa ake yi da maniyin, su yarda su yi ta sayarwa, basu san bataliyar ƴaƴa ake kyankyasa masu ba.
Sannan dole zaku ga nurses ɗin suna ɗan kamanceceniya, kada ku manta a jikin matan nan dai na page ɗin jiya ake ciro kwayayyen halittarsu, gara maniyin na maza daban-daban ne, amma kunga ana iya ciro kwai goma a jikin mace ɗaya, kunga yara goma kenan! Dole wasu su yi kamanceceniya.
Karin wani haske a wannan asibitin, basa kyankyasan mata sai maza, basu cika amfani da sperm mara karfi sosai ba sai idan an basu contracts kan kyankyasar yara mata, amma dik maza suke kyankyasa, waɗan nan nurses ɗin kawai suka kyankyasawa kansu mata, dan ba zasu yarda su kyankyashi maza su renesu ba, dan maza zasu iya basu matsala, mace halitta ce mai rauni, dik a turban da suka ɗaurata zata bi ne, musamman idan bata san komai ba.
Amma dani daku dik mun san idan suka kyankyashi maza suka renesu, suka masu ilimin likitanci to fa idan idanunsu ya buɗe suna iya cin ubansu ne, shiyasa suka ki yarda su ɗauki maza, so a takaice basa kyankyansan yara mata sai maza, kansu kawai suka kyankyawa matar nan dake masu aiki, fatan yanzu kun gane?.
Yauwa karin wani haske, daga waje wani likita baya zuwa aiki a wannan hospital ɗin, wannan amsar tambayar readers ne, in kara maku haske, babu wani mutum daga waje dake shigowa wannan hospital ɗin, ko sperm suka saya a waje ake ciniki, a ƙasa daban ma ake ciniki, in sun saya su waɗan na. 3D ɗin ne zasu fita su ɗauko sperm ɗin su kawo, dan haka wani daga waje baya shigowa, iya waɗan nan 3D ɗin ne kawai ke aiki a asibitin babu wani likita, fatan kun gane?. Mu je zuwa.
Sun jima suna kewaye a wajen, sai da suka tabbatar jariransu suna nan lafiya, suna samun rayuwa daidai da cikin uwarsu, sannan suka fito, kai tsaye office ɗinsu suka koma, dan shiryawa wannan babban project da manyan duniya suka basu aiki a kai mai suna P-C. WANI PROJECT NE WANNAN? SHI NE AINAHIN LABARIN JAMA'A.
A gefe guda kuwa sister Lazy tana can tana kuka kan abin da Dr James yai mata, ya koreta a gaban sister Zinta, wannan abu ya tsaya mata a rai matuƙa.
To mu leƙa CRYSTAL PALACE mu dawo, na fi son a kowani page ku dinga jin halin da kowani ɓangare yake ciki ko ba yawa ne!.
--------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.
Can tsakiyar dare Aryan da ya gagara barci ne ya fito ya nufi room da yake zaton guru na ciki. Ya kuwa same shi zaune daman dadduma yana sallah. A gefen bed ya zauna yana jiransa yana har ya idar, miƙewa ya yi bayan ya kammala addu'a ya nufi Aryan ɗin.
A kusa da shi ya zauna tare da cewa. "Brother lafiya?"..... Kai Aryan ya girgiza alamar a'a ba lafiya, amma bai yi magana ba, guru yasan me matsalar, basa iya kwana cikin fushin juna, idan sun yi faɗa kasa barci dikkansu suke yi, su yi ta faman kumbure-kumbure amma ba zasu iya bawa juna hakuri ba.
Shiru room ɗin ya yi, can Aryan ya ce. "Brother Lion bai ji ciwo ba ko?"...... Wani irin kallo guru ya wurga mashi kafin ya ce. "Yana second room jeka duba". Siririn tsaki ya ja tare da gyarawa ta kwanta a gadon na guru. Shiru guru ya ɗan yi yana tunanin yanzu Lion ya bar ɗakinsa fa, shi ma tin da ya farfarɗo daga alluran ya gagara yin barci, shi ne ya zo wajen guru, ya fake da cewa Aryan bai ji ciwo ba ko? Guru da iskanci sai ya ce mashi ya je ya duba, shi ne yaki zuwa ya koma room ɗinsa, yanzu haka yana tsaye a tsakiyar ɗakin, yana son zuwa duba Aryan ya ga yana lafiya bai ji ciwo baz amma girman kansu da nuna isa ya hanasa, ga abin a ransa ta hanasa sakat.
Shiru Aryan ya kwanta, zuciyansa ya gagara daurewa, sai ya miƙe game da cewa. "Mu je in duba ko ya ji ciwo"............. Hararansa guru ya yi game da cewa. "Ku dai kuka sani". Ya faɗa tare da bin bayansa suka fito waje.
Ɗakin da Lion yake suka shiga, yana jin sun turo kofa ya juyo da sauri, ai yana ganin Aryan wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin kuma ya ɗaure fuska. "What brought you here?". Ya faɗa har da nuna irin bai damu da su ɗin nan ba..... Banza da shi Aryan ya yi tare da wucewa ya kwanta a gado yana satar kallonsa, shi kuma guru ya shigo ya hau tausan Lion ɗin. Da yake abin da yake so kenan su yi sulhu sai ya yi saurin hakura, da haka suka wuce saman gado in da Aryan yake, babu wanda ya ce da ɗan uwan uppan, suka kwanta shiru, ba jimawa barci ya kwashesu.
Washegari suna sun mance da sun yi faɗa, suka koma kamar da, a tare suka yi sallar asuba kamar yadda suka saba, suka dawo, wanka kowannensu ya yi suka sanya hoodie iri ɗaya fari tas, sannan suka faɗa ɗakin aikinsu dan tsawaita bincike kan AVARIS.
A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya ɗauki cube yana jujjuyawa yana ƙoƙarin haɗawa. Su Aryan dake kokarin duba aikinsu ne suka samu sakon binciken Lion da ya tura masu.
Buɗe saƙon suka yi, a natse suka fara karantawa, batu ne kan dalilin da yasa ake ta faman tashe-tashen hankula a arewacin AVARIS, dik jerin tattalin arzikin da arawacin ta mallaka ya rubuto masu ajere, albarkatun ƙasa sama da 28 arewacin AVARIS ta mallaka, ciki har da uranium da ake haɗa su nuclear, arzikin gold, fetur, coal tantalite, tin, granite, asbestos graphite nickel, dik arewacin kasar tana da shi, ma'adanai masu balain tsada, batu ake na makaman nuclear fa, arzikin da manyan ƙasashe basu da shi, shiyasa abin yaiwa Avaris yawa wai shege da hauka.
Bayan sun karanta sun gama ne guru ya ce. "To tin da ma'adinan sun yi wa kasar yawa, shuwagabanninta basu iya amfanar da ƙasar da ita ba why not ba zamu shiga siyasar kasar ba? Ma'ana mu tsayar da waɗan da za su iya kwato ƙasar daga hannun ƴan sarin da ta faɗa?".
Cigaba da jujjuya cube ɗin Lion ya yi tare da cewa. "That's impossible!". Ya faɗa idanunsa a kan Aryan da gabaɗaya ya mayar da hankalinsa a kan waya, his attention isn't there. Yana can yana kallon Seraphina dake ta faman neman hotonsa da ta ɗauka jiya dan ta turawa Rimsha, a tinaninta she's smart, bata san da IRON FIST take tare ba, yama za'ayi ta ɗauki hotonsa ba zai sani bane? Ko da yake bata san gabaɗayanta ma a tafin hannunsa take ba, wai ita ma ta yi wayau.
"Rimsha i didn't see this pic, but why not ki turo mun pic na uncle ɗin naki, idan shi ne zan gane ai". Ta yi typing ta tura mata. Shi dai Aryan ganin gudun ruwansu kawai yake yi, yana son jin karshen wasan......... "Seraphina you are out of your sense! Uncle Aryan ɗin ne zan samu pic ɗinsa? Don't you that ni makiyarsa ce? Idan yana waje ma bana fitowa". Ta turo mata amsa.
Miƙewa Seraphina ta yi, zarya ta fara yi a cikin ɗakin tana tinanin yadda aka yi hoton daddyn nata ya goge a wayar, ta san dai ta ɗaukesa
Unexpected Aryan ya ji an kwace wayansa, a zabure ya ɗago kai, four eyes suka yi da Lion dake tsaye a kansa. Wani irin harara Aryan ya dallah mashi kafin ya ce. "Give me phone malam, ka wani tsaya mun a kai kamar sojan gona". Cike da fargaban kada Lion ya duba wayar ya yi maganar.
Juya gaban screen na wayar Lion ɗin ya yi dan ya ga me ya ɗaukewa Aryan hankali suna irin wannan zama kan mission ɗinsu mai muhimmanci, ai yana juyo da wayar sai..........
Likes comments and share fisabilillah.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 For more information 08161390581 Whatsapp me only.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
STEP 1🔥
2025-11-28🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________30 & 31
Juya gaban screen na wayar Lion ɗin ya yi dan ya ga me ya ɗaukewa Aryan hankali suna irin wannan zama kan mission ɗinsu mai muhimmanci, ai yana juyo da wayar sai ga call ɗin Abba ya shigo. Gabaɗaya hankalin Aryan ya gama tashi, baya son su sake yin faɗa irin ta jiya, amma kuma ba zai iya jurar Lion ya yi taking wani mad reaction a kan tsakaninsa da Seraphina ba, to Abba ya kira ya raba gardama.
Miƙo mashi wayar Lion ya yi yana hararansa da wannan jade cool eyes ɗin nasa, kai ka ce Leo ne a wajen saboda tsananin kamanninsu, girman idanunsu ma ɗaya.
Sai da Aryan ya sauke wani musulmin ajiyar zuciya kafin ya karɓi wayar, ganin Abba ne yasa ya kara natsuwa tare da picking up, a H-free ya sanya wayar, cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaikum Abba"........ "Waalaikumussalam"..... "Good morning Abba".
Shiru Abba ya ɗan yi kafin ya ce. "Stop everything you're doing and come, I want to see you"....... Kallon juna Lion da Aryan suka yi kafin Aryan ya ce. "Abba lafiya dai ko?"......... Daga gefen Abba Faryan ɗan Auta ya riga Abba da cewa. "Yah Aryan wlh kada ka dawo, aure Abba zai je neman maka, wai zai kaimu gidan matan........". Ɗiff muryan Faryan ta ɗauke, da alama toshe mashi baki Abba ya yi, dan yasan idan Aryan ya ji wlh ba zai koma ba, sun fara wasan ɓuya kenan, haka suka yi a baya, ya taɓa ce mashi zasu je wani gida neman mashi mata, Aryan ya ki dawowa, sai da ta shari watatti takwas bai taka gidan ba, ko sun kira wayansa baya ɗauka, wayar Faryan kawai yake ɗauka ya ji ya gida suke, sai da Abba ya ce an bar maganar sannan ne komai ya gyaru, to wannan karon so yake ya damki Aryan ga shi ga shi suna kallon juna kafin ya umarcesa ta yadda ba zai iya bijirewa ba. Sai dai da alama Faryan ya ɓata komai.
Kuma a tsarin Abba da zarar an je an tambayo auren a wannan lokacin ake ɗaurawa, shi baya jeka ka dawo, ana bashi aure za'a ɗaura a wajen, baya bari wai bari yaran su fahimci juna, ya ce zasu fahimta a gidan aurensu, shi yake yin komai, shi dai a bashi yarinya kawai, da zarar anbashi ko tsinken iyayenta baya karɓa, sai dai ma ya basu sadaki mai tsoka, daga nan a ɗaura su ɗauko yarinya su kawota cikin family, kayan ɗaki da kayan sakawa dik zata samesu a gidan mijin, yanzu dama suna zuwa gidansu Aunty Lisa in an basu zai ɗaura masu aure ne kawai su dawo da matansu.
Jama'a kunji wani ta'addancin zuciya irin na Abba? Wannan ai ɗanyen ta'addancin zuciya ne whichs mu IRON FIST family ba zamu yarda ba ko ya kuka ce my people? Ba zamu yarda ayi wa Champion namu auren dole ba! Dole mu yi ruwa mu yi tsaki, ku zo mu je mu yi kanenen mu yi uwa mu yi makarɓiya mu taya Champion namu kwatar ƴancinsa, kada mu bari kanmu ya yi marfi, dan ma dai Abba ne sai mu ɗan raga mashi, amma ba zamu yarda ba.
Ai Aryan yana jin jawabin Faryn ya katse kiran, sai ya kira number Faryan ɗin dan ya ji ainahin meke going. Yana kira bugu ɗaya aka ɗaga, a sanyayye ya ce. "Faryan what's going on? Me Abba yake shiryawa?"....... Unexpected ya ji muryan Abba ya ce. "Abin da kake tinani shi nike shiryawa, na baka 2 hours yanzu in ganka kada raina ya ɓaci".
Ɗan ɗaure fuska ya yi, zai sake yin magana Lion ya yi saurin girgiza mashi kai alamar a'a, dan haka sai ya yi shiru, daga karshe Lion ya ce ya amsa da okey kawai, da hakan ya amsa suka yi sallama da Abba. Yana ajiye wayar Lion ya ce. "Uba wani bango ne da in babu shi babu zuri'a, ba'a ja da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 95