Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗebi sperm daga cikin na daddyn Lion da suka killace ya dasawa matar tasa idan ya aureta ba. Kai na ce akwai cakwakiya babba, dik mommynsu Lion ce silar komai, da bata karɓi kuɗi ta masu hanya sun kama daddyn Lion ba, da ba'a ɗebi sperm ɗinsa an ajiye ba. Yanzu dai a taƙaice Zinta da Maya kannen Lion ne daga kyankyasar kwalba, sun haɗa uba, uwar ce dai ba'a san daga in da aka samo eggs ɗinta ba. Kai Dr James ya zarce shaiɗani wlh, wannan irin kaifin ƙwaƙwalwa da ɗan banza basirar, kuna ga wata plan na ban mamaki!. ALLAH sarki shiyasa Maya da Zinta suke son junansu sosai, ashe ubansu ɗaya, uwar ce dai bamu sani ba ko eggs ɗin mace guda ne ko kuwa kowacce da uwarta! "Ku daina yi mana maganar Muhammad a nan". Dr Mark ya faɗa tare da miƙewa, ya nufi hanyar fita yana faɗin zaman ya kare tin da za'a tuna baya, daga haka ya fice zuwa office ɗinsa. Su ma su Dr James ɗin fita suka yi kowannensu ya nufi office ɗinsa. After some days da faruwar wannan abin. Sister Zinta and sister Maya ne zaune a ɗakin da suke haɗa Chemicals ɗin nasu, abin duniya dik ya ishesu, waɗan nan chemicals da sune haɗawa ya yi mugun tsaya masu a rai, sun gagara tursasa zuƙatansu su cigaba da aikin, sun kuma rasa ya zasu yi, dan basu isa su ce ba zasu yi wannan aik ba, ba mai ja da 3D, sannan ita Zinta zuciyarta ta mace a kan soyayyar Dr James, ba zata iya kin yin aiki idan ya sanyata ba. Dik da basu san ne za'ayi da chemicals ɗin ba amma zuƙatansu sun yi muguwar karaya da tsorata, musamman sister Maya da ta fi Zinta rauni, wani lokaci ma idan tana aiki kuka sosai take yi, saboda haɗarurrukan chemicals ɗin sun zarce yadda kuke tinani, sai ta yi ta kuka tana jin kamar wasu za'a cutar, kamar abin sharri ne, ta rasa dai gane dalilin da yasa take kuka idan tana haɗawa. Yanzu haka kuka take yi hawaye bibbiyu tana tace sabbin chemicals da aka shigo da su yanzu, masu haɗarin da suka fi na baya. Haka ta tacesu, ta cire masu karfin ciki, ta zare matattun ciki, sannan ta je ta haɗa cikin waɗan can chemicals da suka haɗa a cikin wani katon drom mai zurfi, ta zuba a ciki. Tsayawa ta yi a kusa da drom ɗin tana kallon yadda miyagun chemicals ɗin suke juyawa a cikin drom ɗin suna haɗewa da juna. Sister Zinta ce ta matsa wajen, nata chemicals ɗin da ta gama haɗawa ta juye a ciki, sannan ta ce. "Sister Maya lafiya?"....... "Sister Zintata hankalina ya gagara kwanciya a kan wannan aiki, ina jin tamkar sharri ne". Dafata Zinta ta yi, juyowa Maya ta yi suka rungumi juna, Zinta ta ce. "Babu wani abu, yanzu bari in je office na Dr James in bashi report na yau sai in zo mu koma SECTION A mu tattauna a can ko?".......... Kai kawai Maya ta iya gyaɗa mata....... "Je ki kaiwa Dr Kamal naki rahoton kin ji? Mu haɗu a gate na SECTION A". Nan ma kai kawai Maya ta gyaɗa mata. Raba jikinsu ta yi tare da wucewa ta ɗauki result na aikin yau, ta nufi waje cike da zumuɗin zata ga Dr James, yarinyar nan ta haukace a kansa sosai, ita ko iya ganin face ɗinsa ta yi ba ƙaramin daɗi take ji ba, bare ace ya yi mata magana, ooooo, kwanar farinciki take yi. Hannunta rike da file ɗin ta shigo arear 3D office. Tin daga nesa sister Lazy ta hangota, da sauri ta mike ta tareta bata bari ta kariso kusa da office ɗin nasa ba. A gabanta ta tsaya tare da miƙa mata hannu tana faɗin. "Bani rahoton in kai mashi!". Babu wasa a tattare da ita ta faɗa. Tsoronta yasa Zinta ta miƙa mata hannayenta suna ƴan kerma. Fisga ta yi da karfi tare da juyawa tana cokala wannan takalmin nata mai uban tsawo ta nufi office ɗin nasa. Idanun sister Zinta ne ya cicciko tab da kwallah, ta ɗan turo baki kafin ta juya cike da takaicin yau bata kallesa ba, ɗazun da safe ma da zata kai mashi rahoton wani chemicals cikin wanda suka kawo ya faɗi kwalbar ta fashe ya zube su sake kawo irinsa Lazy ta hanata shiga, sai dai ta karɓi rahoton da ta rubutan ta shigar mata da shi, ta kuma karɓo amsar ta dawo mata da shi, abin ya yi mugun bata takaici. Tsaye sister Lazy ta isko Dr James a tsakiyar office ɗinsa yana kokarin haɗe takardun dake kan table ɗinsa, sun tashi kenan, yana tattare rahotonni masu muhimmanci saboda in ya natsu a gidansa cikin dare ya dubasu. Cikin wani irin karuwan yanga da yauni tana wani kwas-kwas ta shigo office ɗin. A gabansa ta tsaya tare da miƙa mashi result ɗin, tana wani karairaya ta ce. "Should I escort you?"....... Shiru bai yi mata magana ba, bai ma ɗago ya kalleta ba, sai da ya gama shan kamshinsa kafin yasa hannu ya karɓi takardan hannun nata. Ɗan duba takardan ya yi, a natse ya ce. "Ina mai wannan aiki ɗin da ba zata kawo rahotonta da kanta ba?". Ɗan tsuke fuska ta yi, sai kuma ta ce. "Ban san meyasa bata son shigowa office ɗinka ba, amma ranar na ji tana cewa da ta shiga office ɗinka gara ta shiga cikin wuta, shiyasa idan ta zo take bani result ɗin ta ce in miƙa maka, ni dik tinanina ma kai kake cewa ta bani in baka ai". ......... Shiru ya yi bai sake yin magana ba, sai dai ya miƙo mata result ɗin alamar ba zai karɓa ba, idan kuma bai karɓa ya sanya hannu ba to fa aikin sister Zinta na yau an yi cancel ɗinsa, idan dama aikin 30 days zata yi to sai ta kara maimaita wannan aiki da aka yi cancel ya zamana kenan 31 days zata yi. Abin ya yi mugun yi wa sister Lazy daɗi na yadda ta ga ta lalata mata aikinta na yau, cike da yanga ta juya ta fita. Kai tsaye room na su sister Zinta ta nufa, tana wani irin makirin murmushi. Tana zuwa ta iskosu a ɗaki, isowarsu kenan suna ƙoƙarin cire kaya zasu shiga wanka. Jefawa sister Zinta file ɗin a kan fuskanta ta yi tare da cewa. "Ya soke aikin yau! Kuma ya ce dik in kika zo kawo mashi rahoto ki ajiye a PA office". (Office na PA office ɗinta kenan, kunga ta samu damar kullum ta dinga ɓata mata aiki, tana shirga mata karya a wajen Dr James har ya fusata ya fara hukuntata. Cike da tashin hankali ta ɗauki file ɗin, tamkar zata yi kuka ta ce. "Meyasa ya soke aikin? Akwai in da na yi mistake ne? Ko dai akwai abin da yakamata in saka wanda ban saka bane? Aunty Lazy please help ki basa hakuri, zan sake duba komai in gyara". Dogon tsaki Lazy ta ja tare da juyawa ta fita, tana fita Zinta tasa kuka tana faɗin ta shiga uku, dan tasan idan ya soke aiki fa mutum ya shiga uku, bayan sake aikin sai ya bashi hukunci mai tsanani. Jikinta na rawa ta ce. "Sister Maya me abin yi?"........ Maya da gabaɗaya jikinta ya yi mangaribar jemage ne ta amsa da. "Ina ganin mu yi wanka sai mu je gidansa ki bashi hakuri, ki ƙara gyara rahoton, ki duba da kyau ko akwai in da baki yi daidai ba". Na'am ta yi da wannan shawara, cikin rawar jiki ta buɗe file ɗin ta zaro paper, a gefen gadonsu ta zauna ta hau dubawa a natse. Ita kuma Maya ta wuce cikin toilet dan yin wanka. Me kuke tinanin zai faru? Cakwakiyar asibitin nan dayawa take!. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. STEP 1🔥 2025-12-3.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 36 & 37 Har Maya ta kammala wanka ta fito Zinta bata ga wani mistake ba a wannan result ɗin da ta duba, miƙawa Maya ta yi game da cewa. "Sister tayani dubawa ko dai ban gani da kyau ba, bari nima in yi wanka in fito". Karɓa sister Maya ta yi, ta ɗaura saman bed kafin ta wuce ta hau shiryawa. Da alama daddynsu Leo ne yake da irin design na idanun nan nasu mai shegen kyau da ɗaukar hankali wanda a hausance ake cewa mai idon shinkafa, zaku ga idanun yana da tsawo kamar shinkafa a kwance, ga shi ya ɗan yi kamar zanen kifi, kuma idanun a buɗe suke manya-manyan, na su Maya farare kal-kal, amma nasu bai yi kalar sanyi watau jade eyes sosai kamar nasu Lion ba, su idan nasu ya ɗan yi duhu kaɗan, while na su Lion yana da haske jade ɗin. Cikin wani crazy jeans and top Maya ta shirya, kayan ya zauna ɗas a jikinta, ta gyara hair ɗinta da ya kai har tsakiyar baya, ta tara ta ɗaure a tsakiya tare da sake jelar a baya, ta yi matuƙar kyau sosai, a gefen gadonsu ta zauna tare da jawo paper ta fara dubawa. Ita ma ta yi iya dubanta bata ga wani mistake ba, sai kawai ta naɗe takardan ta mayar. A haka Zinta ta fito ta sameta, shiryawa ita ma ta yi cikin irin kayan Maya sai dai kowa da kalar tasa, na Maya blue jeans and white top, nata kuma black jeans and milk top. Sai tashin kamshi suke yi, ta ɗauki paper ɗin, suka kama hannun juna suka fito. Kai tsaye haɗaɗɗen gidan 3D suka nufa, dikkansu suna cike da tsoro da fargaba, dan sun san halinsa, yanzu yana iya hukuntasu ta hanyar kara masu ayyuka da sauransu. Abin mamaki kuma a wannan hospital ɗin ayyuka basa taɓa karewa fa, kullum Dr James yana da ayyuka bila adadi da yake sanya nurses ɗinsa. Guards biyar ne ke gadin gate na gidan, da suka yi knocking sai sister Maya ta ɓuya a bayan Zinta, saboda ita mayyar tsoro ce, bata son haɗa ido da waɗan nan shaggun samudawan masu gadin nasu. Zinta kuwa ta yi karfin halin tsayuwa har aka buɗe masu. Su kansu guards ɗin sai da suka haɗiyi yawu na ganin kyan su Maya, yaran sun haɗu. Dik cikin hospital ɗin su ne kawai idan an gansu sai an sake juyowa an gansu. Babu alamar annuri a kan fuskan guards ɗin ya tambayi lafiya. Sister Zinta ce ta kora mashi jawabin cewa sun zo ganin Dr James ne, zasu bashi rahoto. To da yake yasansu sosai, sai ya basu hanya. Kama hannun sister Maya dake laɓe a bayanta ta yi, ta jata suka wuce ciki, Maya jikinta sai kerma yake yi har suka karisa kofar babban parlonsu. Tsayuwa suka yi suna tinanin ya zasu yi su buɗe kofar nan yau? Dole sai da fingerprint na mamallakan gidan yake buɗewa, to ya zasu yi. Ana haka sai ga Dr Kamal ya fito rike da waya, yana sanye da short zuwa cinya, daga sama single farare kal-kal, sumar kansa bakinkirin tana wani irin sheki a kwance luff. Wani musulmin ajiyar zuciya suka sauke kafin su tsugunna har ƙasa su ɗaga mashi gaisuwa. Amsawa ya yi tare da cewa lafiya?. Yana magana yana kallon Maya take ta faman kankame sister Zinta. Dik sun yi ƙasa da kai, suna da kunya sosai, basu son ɗagowa su gansa a cikin wannan yanayi da yake na rashin wadataccen tufafi, dama dai dogon wando da singlet ne a jikinsa to da sauki, amma ɗan wannan shorts ɗin kai ina. Sister Zinta ce ta ce. "Mun zo ganin master ne".......... Hanya ya basu kan su wuce shi kuma ya karisa fitowa waje. Da sauri suka miƙe suka shiga ciki suna zuba mashi godiya. Like wow, main parlon nan nasu ya matuƙar haɗuwa, ga wani sahihin kamshin dake tashi. A tsakiyar parlon suka tsaya kallonsu a sama suna hangosa tsaye a saman bene rike da wani haɗaɗɗen cup mai ɗauke da hot green tea yana sha. Shi ma daga shi sai shorts and single irin na Dr Kamal. Ƙasa suka zube gwiwowinsu suna kallon saman, murya a sanyayye cikin girmama sister Zinta ta fara bashi hakuri tare da nuna mashi result ɗin nata. Shiru yai masu for almost 10 mins, har sun gaji da durkuso, tamkar Maya zata yi kuka, har sun fidda ran zai amsa sai suka ji ya ce. "Get out of my house!". Yadda yai maganar ya yi balain girgizasu, jikinsu na rawa suka miƙe a zabure, kenan ya tabbata ba zai karɓi wannan aikin ba, ya soketa!. Juyawa suka yi, idanunsu ya ciko tab da kwallah, suka nufi kofar fita. Bayansu ya bi da kallon wanda tin da suka shigo bai ɗaga ido ya kallesu ba, sai da suka juya zasu fita ne slowly ya ɗago eyes ɗinsa a kansu. Kurawa mazaunan Zinta eyes ya yi, take ya ɗan shanye har da lumshe idanu kafin ya sauke ajiyar zuciya, yadda surarta take it melt his heart. Ji ya yi tamkar ya miƙa hannu ya jawota ya rungume, da alama da gaske yake sonta, iskanci ne kawai ya cika mashi ciki, dik wani step ɗaya idan ta taka sai ya ji zuciyansa ya amsa, yana jin tamkar yau ba zai iya barinta ba, kamar kawai ya ci amarcinsa tin da ya mallakawa kansa ita, amma bai motsa daga in da yake ba har suka isa bakin kofar parlon. Tsayuwa cirko-cirko suka yi suna tinanin yadda ake buɗe kofar, basu iya ba. Slowly suka juyo da kallonsu a kansa, da sauri ya ɗauke kansa daga kallonsu kamar wani mara gaskiya. Sister Zinta ce ta sake Maya tare da dawowa in da suka tsugguna ɗazun ta sake tsuggun nawa. Hakuri ta hau bashi game da neman alfarman ya zo ya buɗe masu door. Hallau sai da ya yi good 10 mins shiru kafin ya yi mata alama da hannu a kan ta tafi. Da sauri ta miƙe tana zuba godiya, tana juyawa ya ɗago da eyes ɗinsa a kan mazaunanta. Zuba mata ido ya yi har ta kai bakin door ɗin. Suna tsaye sai gani suka yi kofar ta motsa ta ɗan buɗe kaɗan. Ya buɗeta ne ta wayarsa. Handle suka kama suka ja, kofar ta buɗe, da sauri suka fita suna jan numfashi. Suna fitowa Maya ta ci karo da Dr Kamal da yake ƙoƙarin komawa ciki. Karo suka yi kanta ya bugu da kirjinsa baya ta ja kamar zata faɗi yasa hannu ɗaya ya damki wuyar rigarta, ya jata ta tsaya a kan kafafunta. Ɗan zuba mata ido ya yi kafin ya wuce ya basu waje. Zazzare idanu a kansa ta yi tare da sauke ajiyar zuciya na ganin ya wuce. Rikota Zinta ta yi suka wuce. Slowly ta juyo dan ta ga ko Dr Kamal ya shiga ciki, ai tana juyowa suka yi 4 eyes, dan yana tsaye a bakin kofa yana karewa albarkatun jikinta ta baya kallo. Tana juyowa ya ɗauke kallonsa tare da wucewa ciki, wucewa ita ma ta yi da sauri tana kara waigo kofar har suka fita........ Suna fito sister Zinta ta ce. "Sister Maya i wonder ooo"...... "Wonder for what?"....... Nisawa ta yi kafin ta ce. "Sister Lazy said that wancan babyn da ta fito da shi ranar is for Dr Kamal right?". Kai Dr Maya ta gyaɗa alamar e. "But where's his wife? Ban taɓa ganin maman baby ɗin ba, and tin da muke zuwa 3D House ban taɓa ganin mace a ciki ba, su uku suke rayuwa! Kuma tin daga wancan rana da naga jaririn ban sake ganinsa ba, ko ina yake? And kin yi tinani kan irin chemicals da muke haɗawa? Ki yi tinanin irin projects da muke yi, ki tina kullum a Section C sai mun haɗa chemicals mun shiryasu a kwalabe, kullum kuma ana fita da chemicals sama da kwalba 200 daga section C, a tinaninki me ake yi da dikka waɗan nan uban chemicals ɗin?". Nima ina son sani, dan billahil lazi ba iya cutar suke kirkira da wannan uban chemicals ɗin ba, kada ku manta project na cutar nan sun fara ne shekara uku da suka wuce, kuma sai yanzu suka iso fagen haɗa chemicals na cutar, kunga which means chemicals da ake ɗiba kullum akwai wani gagarumin abin da suke aikatawa da shi, gaskiya akwai abin da ya saɓa babba, kuma da alama gagarumin abu ne ba karami ba, dan sun ɓoye shi sosai, basu bari kowa ya sani ba, ko ita Lazy bata sani ba. Sister Maya ta ce. "Ni kaina abin ya fara ɗaure mun kai, ina suke kai chemicals da ake ɗeba kullum? Kullum ana cikin shigo da sabbin chemicals, mu tacesu su shirya a kwalba, kullum da daddare sai an ɗebi chemicals ɗin, ina ake kaisu? Me ake ayi da su? Ina babyn Dr Kamal da sister Lazy ta shigo da shi Section namu ranar? Ina mother ɗin babyn?". Sister Zinta ta ce. "Let me free my brain, leave it rest, kinga ki bari mu hutar da brain ɗinmu na ɗan lokaci, idan muka natsu sai mu tattauna a kan matsalar, dan da alama gagarumin aiki ne". Na'am Maya ta yi da batunta, dan dama kanta kamar zai fashe saboda ciwo, ba aikin wasa suke yi ba, dan ma suna da kwarewa, tace chemicals da banbantasu ba dik kai ba, dan ma dai kullum idan zasu tashi daga aiki akwai kwayar da ake basu su sha na ɗan resting brain ne, sannan a hospital ɗin na dik karshen wata akwai wasu kwayoyin magunguna guda biyar fa ake basu suna sha, dik da suke malaman lafiya basu san kwayoyin menene wannan ake basu dik karshen watar ba, su dai suna sha kawai. Kuma idan sun sha ba karamin daɗin jikinsu suke ji ba, suna jinsu da ƙarin lafiya sosai, dik wata kasala tana barin jikinsu, suna samun karfi sosai, shiyasa tin safe suna aiki har dare basa gajiya. Cike da wannan tinani a ransu suka koma room ɗinsu, suna tinanin yadda zasu ƙare wannan aiki su huta da bala'in 3D. Suna komawa room ɗinsu ta ajiye result ɗin suka yi kwanciyarsu a kan gado, suka fara hira cike da tsananin kaunar juna, suna yi suna farinciki game da daddaɗar murmushi dake kwantar masu da hankali idan suka ga ɗayansu ya yi!. -----------------------🔥 CRYSTAL PALACE. Kwance take a saman bed ɗinta tana kallon saman ɗakin, ta gagara ko motsawa, farkawarta daga barci alluran da ya yi mata kenan, idanunta sun kumbura sosai, har kamar zasu rufe saboda kuka. Tunawa ta fara yi da abin da ya faru tsakaninta da daddyn nata. Lokaci guda ta ji kunyansa ya yi mugun shigarta, sai a yanzu ta fahimci ba abu bane mai kyau, sai kuma yanzu ta gane abin da kunya. Tana tsaka da tinani sai ji ta yi an turo kofar. Slowly ta kai kallonta a kan door ɗin. Madam ce ta shigo hannunta rike da cup and plate, a saman side sofa ta zauna tare da cewa. "Kin farka ne baby?".... Da kallo kawai ta bita, lips ɗinta sun manne da juna, bata ce komai ba, ta zubawa Madam ido kawai........ "Tashi ki sha tea mai zafi ki ɗumama cikinki". Ta faɗa tana kamo hannunta. Dogon nunfashi ta ja, sai a lokacin ta iya motsa lips ɗin nata, da ɗan karfi ta buɗe shi, da kyar ta iya cewa. "Mom ina daddy?"........ Madam dake ta faman jujjuya mata tea da spoon dan ya yi sanyi ne ta amsa da. "Tin da ya dubaki daren jiya yai maki allura ya fita bai dawo ba"...... Shiru ta yi tana tinanin ba dai ya sake yin fushi da ita ba, in kuwa haka ne ta shiga uku, ALLAH sarki zuciyata, ita ba damuwarta dukan da ya yi mata bama, damuwarta kada ya yi fushi da ita, wlh tana tsananin son Aryan, ta kuma karɓi laifinta, a shirye take da ta bada hakuri. Muryan Madam ne ya katseta da cewa. "Seraphina"........ Ɗago ido ta yi ta sauke a kan Madam...... "Meyasa da aka baku waɗan can littafan a makaranta baki nuna mun ba? Meyasa dik abin da su Aana suke yi a room ɗinku baki taɓa faɗa mun ba?"........ Idanunta ne suka cicciko da kwallah, da kyar ta yunkura zata miƙe Madam ta yi saurin ajiye cup ɗin hannunta a ƙasa ta taimaka mata, ta miƙe zaune game da jingina da jikin headboard na bed ɗin. Zuba mata ido Madam ta yi tana tinanin irin birkice mata da Aryan ya yi jiya, kai jiya ta ga bala'i, yana barin gidan Abba gidan ya dawo, yana zuwa ya kwashi takardun na Seraph ya nufi room na Madam. Tana zaune a kan bed tana tinanin meyasa ya rufe kofofin gidan nan ya daki Seraphina bayan kuma ya sanar mata cewa ta kula da Seraph baya son ko kuda ya taɓata, saboda ta kula da ita yasa ta bar karantarwa a school ta dawo ta zauna da ita, ya ce Seraphina rayuwarsa ce, amma yanzu da kansa yake dukanta haka? To me ya yi zafi. Tana tsaka da wannan tinani ne sai ta ji an buɗe kofa, kafin ta motsa ya faɗo cikin room ɗin. Yana wani irin huci ya watsa mata waɗan nan takardun a kan fuska, a fusace ya ce ta faɗa mashi yadda aka yi Seraphina ta samu waɗan nan littafai a school?. Hakika ta tsorata sosai, jawo littafan ta yi, ba karamin gigita ta yi da ganinsu ba, da sauri ta ɗago kai tana faɗin subhanallah. Muryarta na rawa ta fara faɗin. "Wlh bani da masaniya a kan wannan abin, sai dai mu tambayi director, ban sani ba... ....". Wani irin gigitaccen tsawar da ya daka mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar. "Bana son nonsense! A matsayinki na malamar dake kula da sashen ɗaliban kwana da hostel ɗinsu ne zaki ce baki da sani a kan waɗan nan littafai? Okey na ji, amma ai kina da sanin cewa maza suna shigowa hostel na mata ko? Kina da sanin cewa ƴaƴan mutane suna aikata zina ko? Kina da sani kan cewa har family planing drugs ake baiwa yaranmu suke sha! Kina kuma da sanin cewa ana ɗaukar yaranmu a fita da su ana lalata masu rayuwa ko?!". Tin da ya fara magana ta kiɗime, hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, a razane ta sauƙo ƙasan bed ɗin, jikinta har rawa yake yi, hankalinta ya tashi da jin wannan magana, kuma ta yi tsananin razana da ganin yadda ya rikiɗe mata gabaɗaya, tsoron ta daku a hannunsa take yi!. Rantsuwa ta fara yi mashi da ALLAH kan wlh bata da sani kan dika waɗan nan tuhumar tasa. Ya fahimci tana da gaskiya bata san komai ba, ya gano daga sama abin yake, manyan makarantar su suke da sa hannu a kan wannan ɓarna, dan haka sai ya juya ya fita cikin fushi, shi ne ya dawo ya duba Seraphina ya fita zuwa makarantar tasu, dan wlh ya sha alwashin dole su yi aiki a kan nalaman makaranta, wannan ɓarna ta yi yawa. To mu koma kan labarinmu. Tamkar zata yi kuka ta ce. "Mom ban san cewa hakan laifi bane, na ɗauka tin da an bamu books ɗin ana son mu koya ne, all thoughts abu ne mai muhimmanci da yakamata mu mayar da hankali mu koya, shiyasa muke karanta littafan ni da Rimsha". Shiru Madam ta yi tana tinanin irin ɓarnar da yake cikin littafan nan ace waɗan nan ƴan

Chapter 46 of 95