wani abu ne mai kama da jelly da ke cikin ɓargon ƙashin jariri wansda sai sun firgita jariri jikinsa ke sakin wannan sinadarin ta yadda in sun kashesa zasu iya samu, wannan sinadari yana ɗauke da hyaluronic acid da collagen, a yanzu ba zan faɗa maku me suke yi da sinadaran nan ba, dan tashin hankalin zai maku yawa, amma gaba zaku ji komai In Sha ALLAH.
To bayan wannan sinadari na wharton's akwai glycosaminoglycans, da kuma chondroitin sulfate, sannan akwai exosomes, da umbilical cord stem cells da dik suke amfani da shi daga cikin ɓargon ƙashin jariri, wanda in muka natsa cikin labarin zaku ga komai dallah-dallah da idanunku, zan daure in rubuta maku komai, ba zan rage koda abu ɗaya ba In Sha ALLAH! Yadda na tsara labarin nan, dik taɓa zuciyansa ba zan canza ba, na sha kuka wajen rubutasa tamkar raina zai fita, amma haka na daure, ina typing ina kuka saboda tashin hankalin ya kai tashin hankali, ace da jinin jariri suke haɗa wasu magunguna, jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, ba imani ka ɗauki jariri kasa inji ta marƙaɗa shi, ya rab, wai wani irin zuciyace a kirjinsu 3D?.
Ga wasu sinadaran da suke cirowa daga ɓargon ƙashinsu, ya ALLAH, ko waɗan nan sinadaran kuma me suke yi da su? Alƙalamina zai waware maku komai.
Kwashe komai tas suka yi, suka fita da jinin izuwa wani ɗaki dake kusa da wajen, a nan suka ajiyesu cikin wani katon freezer, sannan suka fito daga cikin wajen, sai gobe za'a fara ƙoƙarin haɗa magunguna, dama kashe jariran kawai suke yi cikin tsakiyar dare yadda babu ma wanda, zai gansu.
Suna fitowa SECTION D Dr James ya koma. Su Dr Kamal kuma suka koma gidansu, wlh bawan ALLAHN nan Dr James tamkar ba jarirai rai biyar ya danna cikin inji ta niƙasu ba, ko kaɗan bai damu ba, ya shiga cikin ɗakin da su Zinta suke, tana barci ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya fito, kai tsaye gidansu ya koma, dama in baku manta ba ɗazun ya ce mata anjuma zai sake yin abin da ya yi da ita ai, to shi ne ya zo ɗaukarta.
Ya ilahi, me suke yi da waɗan nan sinadaran da suke cirewa daga ɓargon ƙashin jariri? Mesuke yi da sinadarin cikin jinin jaririn? Daga gani abubuwa masu muhimmanci da tsadar gaske suke yi da su, ki tsaya ki karanta abin da suke yi da sinadaran. Watakila kema kina amfani da wannan abin bisa rashin sani! Sai ki san me kike amfani da shi!.
Tambaya shin idan su Maya suka farka zasu gane an ɗauki jarirai guda 5? Ko ba zasu gane ba? Idan suka gane me zasu yi? Wani mataki zasu ɗauka? Ya rabbi, idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba, ya ALLAHU ka kawo mana karshen dik wata fitina, ALLAH ka dubemu da idanun rahama.
Likes comments and share fisabilillah.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-12.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E_____________ 49 & 50
WS-HOSPITAL.
Kai tsaye room ɗinsa Dr James ya wuce da ita, bai direta a ko'ina ba sai a saman bed ɗinsa. Toilet ya wuce, sai da ya yi wanka saboda wajen jini da suka je, ya tsabtace jikinsa fes, sannan ya dawo cikin ɗakin, jikinsa sanye da bathrobe ya haye saman bed ɗin, jawota jikinsa ya yi, ya fara sarrafata cikin salon kwarewa.
Can cikin barci ta ji ana taɓa mata jiki, a hankali ta waro idanunta, kai tsaye sai saman face ɗinta, dik da cewa dim light ne a kunne, amma tana iya ganin fuskansa sosai. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Sir"......... Ɗan kwantowa kanta kaɗan ya yi. "Da sir yakamata ki dinga kiran mijinki ne?". Ya faɗa yana shafe cikinta.
Kai ta girgiza mashi, fuska ɗaure da kyakkyawan murmushin nan nata da bana fatan in daina ganinsa a kan fuskanta ta ce. "Sorry oga".
Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, yana jin wani irin azababben sonta na ƙara shigarsa matuƙa, shi kaɗai yasan irin matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa, ita ma ita kaɗai tasan irin son da take yi mashi.
"My oga please ka kaini in ga darling ka ji?". Ta faɗa cikin raunin murya, da alama da yaron nan a ranta ta yi barci, sun gagara mancewa da shi ko na second ɗaya ne....... Ɗan rintse idanu ya yi, ya ji haushi, tana neman ɓata mashi darensa mai daɗi. Can ƙasa ya ce. "Zuwa da gobe idan muka tashi aiki zan kaiki ki gansa". Ya faɗi hakan ne kawai cikin tsananin mayen sonta da yanayin da yake ciki, amma batu na gaskiya ba zai iya kaita in da darling yake ba, dan izuwa yanzu cutar ta gama yawace gangar jikinsa, dik wanda ya kusancesa zai kamu ne, suma 3D sai sun yi using care overall da oxygen dan kada su shaƙi iskar numfashinsa a ɗakin da yake a ciki, suna shaƙa zasu kamu a cutar ne suma.
Jin cewa zai kaita wajensa gobe ne yasa ta fara murna tana farinciki, nan ta saki jiki, ta bashi haɗin kai, sosai ya yi romancing ɗinta, ya gigitata ya sanya ta har da kuka, amma kamar ɗazun ne, bai tare da ita ba, iya wasa ya yi har ya yi realizing abin dake damunsa, ya samu natsu sosai.
Ɗaukarta ya yi suka shiga toilet, kun sansu da kunya sosai, sai faman ɓoye fuska take yi, shi kuma shugaban marasa kunya na duniya, wai ta mashi wanka, ta ce a'a ita kam ba zata iya ba.
Suna shiga cikin jaccuzi ya jawota jikinsa, daga shi sai shorts, ya so cire shorts ɗin ma ta dinga mashi magiya kada ya cire, saboda son da yake yi mata ya hakura ya shiga cikin ruwan da shi.
Mara kunya dik ya cire mata kaya, yasa dik ta takure waje guda, tana ta faman dukunkunewa, ya jawota jikinsa, haka ya dinga wasa da ita a cikin ruwan nan, sai da ya sake realizing round 2, sannan ya ce su yi wanka, dare ma ya yi.
A natse suka gudanar da komai, ya bata bathrobe ɗinsa ta sanya, yau tana jin tamkar wacce akaiwa kyautar duniya da abin dake ciki, sai murna take yi. Ɗaukarta ya yi, sai kan gado ya direra, tana ce mashi zata sanya kaya a jikinta, ai ina, jawota jikinsa ya sake yi, ya ja masu bargo. Can ƙasan maƙoshi ya ce ta yi barci sai da safe in zata koma wajen babies ta sanya kayanta, yanzu taka tare da mijinta ne, ya hutar da ita sanya wani sleeping dress.
Soyayya, soyayya shegiyar aba ce, sai ta kwanta luff a jikinsa, yana ɗan shafa bayanta har barci tai awon gaba da ita, shi ma ba jimawa barci ta ɗaukesa. ASUBA TA GARI.
---------------------------🔥
Washegari da su sister Zinta suka zo basu fahimci an ɗauki jarirai guda biyar ba, saboda in baku manta ba Dr Mark ya cire gadan babys ɗin ai. Kamar kullum, shirye-shiryen yi wa dikka jariran wanka suka fara yi. Zama sister Zinta ta yi a gefen gado tana ɗan dafe mararta dake murɗa mata a hankali.
A kusa da ita sister Maya ta zauna tana faɗin. "Sis lafiya kika zauna?"..... Tana ɗan dafe ciki ta amsa da. "Cikina na ciwo, ina ganin menstruation ɗina ne, dama tin daren jiya nike expecting ɗinsa"..... Siririn murmushi sister Maya ta yi kafin ta ce. "Na ƙosa nima in fara wannan period ɗin dan in ji me kike ji da kullum kike kukan ciwon ciki idan zaki yi"........ "Uhm da kin fara zai isheki ne, ga ciwo ga wahala". Ta kai karshe tana ɗan kwanciyar rigingine ko zata ji sauƙin ciwon da cikin nata yake yi mata.
Nasan yanzu tambayoyi sun gama cika maku kai kan cewa ya aka yi sister Maya bata fara period ba kuma bayan shekarunsu ɗaya da sister Zinta ko? Kuma ace 18 years old bata fara ba, abin da mamaki ko? To haka ne, yadda kuka ji ne, Maya bata period, bata taɓa yi ba, bata san ya yake ba. Kun tina cewa Dr James ya ce zai auri sister Zinta, ita kuma sister Maya zai mai da ita PA ɗinsa? Kun tina wannan magana?.
To ba Maya kawai ba, dikka nurses dake cikin wannan hospital ɗin basa period! Zinta ce kawai take yi! Amma saura nurses ɗin dikka shiru ne, ga shi dai shekarunsu ɗaya watau 18 years, amma basa yi. To dikkansu 3D sun cire masu mahaifa ne, babu mahaifa kuma ai kunga babu zancen period ko? Su dama dan su yi aiki 3D suka kyankyashesu ba dan su haihu ba, shiyasa 3D ɗin suka cire mahaifansu gabaɗaya, to sister Maya na daga cikin waɗan da aka cirewa Mahaifan.
Ita kuma sister Zinta ya bar mata mahaifanta ne dalilin abu ɗaya, in baku manta ba ya ce zai haɗa eggs ɗinta da sperm na Haiza'an watau daddynta, yai mata dashen cikin dan ta haifa mashi yara masu kwakwalwa irin na daddynsu Lion ko? To saboda wannan dalili yasa ya barta da mahaifarta tsinanne, kuma karin wani abin takaici bafa sperm ɗinsa zai dasa mata ba, shi da yake matsayin mijinta ai yakamata da nasa zai yi dashen, a'a, dana ubanta zai yi mata saboda tsinanne ne shi! Annoba! Ya ci alwashin sake haifo Muhammad Haiza'an bayan sun kashe na asali! Yana da hanyar da zai yi dashen sperm ɗin Haiza'an ya kyankyashe ƴaƴan da yake ikirarin nasa wanda zasu gajesa ɗin ba sai a jikin sister Zinta ba, amma saboda kudurinsa na son ya ga ya haifi magaji wanda ya fi Haiza'an kaifin ƙwaƙwalwa shi ne zai dasawa ƴar cikinsa, kai wannan abu da bakinciki yake.
Sister Maya ta fi sister Zinta tsananin son yara, shiyasa ta sanyawa wannan ƙanin nasu suna darling, saboda tsananin son babys, ga shi kuma ita ce ba zata taɓa haihuwa ba har abada, dan har ovaries ɗinta basu bari ba, ba halin ai mata dashen wani mahaifan, kun tina na faɗa maku dik karshen wata akwai drugs da 3D suke basu suna sha? Ai saboda cire masu mahaifa da suka yi ne.
ALLAH sarki su bama su san ana yi ba, bama su san ana haɗa eggs da sperm a kyankyashe jarirai a hospital ɗin ba, su dai suna aiki kawai, kuma tsabar 3D azzalumai ne basu barsu sun yi karatu ɓangaren lafiya kai tsaye ba, sai suka turasu suka yi ilimi ɓangaren chemicals, sun san da cewa jinin Muhammad Haiza'an ne su, muddin suka koyar dasu ilimin lafiya to sai sun ci ubansu ne, dan dik wata badaƙala da suke yi zasu ganosu, shiyasa suka haɗasu da tace chemicals da banbantasu, sannan su zubasu cikin kwalabe su shirya, kunga wannan Dr James ɗin ba zai ga Annabi ba tsinanne............😭
A irin brain na baiwar da suka gado kuna ganin alluran da Dr James yai wa darling na wancan cuta har sun gano ba magani bane cuta ce dik da basu da ilimi kan ɓangaren 3D, me kuke tinani zai faru da ace ilimin lafiya aka koyar dasu ba ilimin sanin chemicals ba? Kuna tinanin izuwa yanzu da basu gano abin dake binne ba ne? Da sun gano cewa kowani shekara sai an kyankyashi jarirai sama da 500, kuma a fitar dasu izuwa black market! Wlh da zasu gano dik abin da ake yi, har SECTION E da sai sun gano balai da fitinar game da tashin hankalin dake ciki, amma an barsu da aiki a SECTION C na hidimtawa chemicals ɗin da bama su san me ake yi da shi ba. A zuƙo sinadaran dabbobi kawai a haɗasu da tacesa da gyarawa..........😭
"Ni nasan ba wani wahala, kawai ragonta ne irin naki". Sister Maya ta faɗa tana ɗan murmusawa. Already saura nurses ɗin har sun fara yi wa jariran wanka....... "Ina ganin abin da my oga ya mun daren jiya nema ya hana period ɗina zuwa". Cewar sister Zinta. Zazzare fararen idanunta a kanta sister Maya ta yi, tana ɗan sakin murmushi ta ce. "Bani labari".
Da yake shaƙuwarsu ya zarce misali sai sister Zinta ta bata labarin komai. Ƙara faɗaɗa murmushinta sister Maya ta yi, ta dinga tayata farinciki tare da ce mata ta kula sosai, ta zage ta kame zuciyar Dr James sosai, saboda taga kowa son shi yake yi, kada ta bari ya kubce mata, cike da farinciki ta amsa da zata yi hakan.
(Kada ku ga wani lokaci ina rubutu kan waɗan da basu a addinin Musulunci kuma ina saka In Sha ALLAH, ko wani abin da ya danganci sunan ALLAH ku ga laifina, bakinmu mu musulmai ya rigada ya saba da ambaton ALLAH subhanahu wata'ala, shiyasa nike mancewa in saka waɗan da basu san ALLAH ba kuma suna kama sunansa, nasan ba zan iya gyara wannan matsala ba shiyasa nai magana, ko yaya sai na ambaci sunan ALLAH, yanzu haka a karshen maganar sister Zinta har na rubuta ta ce In Sha ALLAH sai na tina na goge, dan haka in kunga irin haka ku wuce kawai, sabo da kiran ALLAH ɗin ne!.)
Cikin zolaya sister Maya ta ce. "Amma abin da ogan yai maki is it sweet?". Shiru sister Zinta bata tankata ba, ta dai dafe ciki, ganin haka yasa sister Maya sake cewa. "Da gaske cikin yake maki ciwo sosai ne?".
Kai ta gyaɗa mata alamar e, ɗan rungumota sister Maya ta yi, ta fara yi mata sannu, tana shafa kanta on a serious note, sai kuma ta ce. "Ko dai in je in karɓo maki drugs a drugs side ne?"..... Kai kawai ta gyaɗa mata alamar e tana rintse idaunta saboda azaban zafin da take ji.
A hankali sister Maya ta kwantar mata da kanta a saman pillow, ta miƙe game da nufar waje tana kallon babys dake ta faman kuka, suna son shan madara.
Dab zata fita Dr Kamal na sako kai, karo suka ci, baya ta ɗan ja tana ƙoƙarin ɗago da kallonta taga wanene, sai kuma ta risinar da kai, dan kamshin perfume na 3D ya bata amsar su waye ne.
"Good morning sir". Ta faɗa tana duƙawa. Tsayuwa Dr Kamal ya yi a dab gabanta, ya baiwa Dr James and Dr Mark hanya suka wuce ciki. "Morning babydoll, ina zaki je kike sauri haka?". Dr Kamal ya faɗa yana kallon hannayenta da ta haɗe waje guda, suna ɗan kerma.
"Dama sister Zinta ce cikinta yake ciwo, zan je sashen drugs in karɓo mata magani"......... Kai kallonsa a kan Zinta yai, sai kuma ya kalli Dr James dake tsaye gaban wani baby dake ta faman kuka........ "Meyake damunta?". Ya tambaya a natse. Haka kawai sai ta ji ta tsinci kanta da tsananin jin kunyar faɗin abin dake damun ƴar uwar tata.
Ganin haka yasa ya ce. "Jammy kana da patient". Ya faɗa yana kallon Dr James. Ɗago dara-daran eyes ɗinsa Dr James yai a kansa, yai mashi kallon wace patient kuma amma bai yi magana ba.
Da hannu Dr Kamal ya nuna mashi Zinta dake kwance saman gado, idanunta a rufe ruf. Kallon ƙasan ido Dr James yai mata kafin ya ɗan jinjina kai alamar okey, ya cigaba da abin da yake yi, shi kuwa Dr Mark ɗan air, shi fa ba ruwansa da soyayya, in kunji Dr Mark na magana to sabga ce ta cigaban aikinsu, bai san wani abu wai shi soyayya ba.
"Mu je office ki haɗa mun green tea". Dr Kamal ya faɗa, ba tare da jiran amsarta ba ya wuce gaba, bayansa ta bi tana waigo sister Zinta, ba dan 3D ne ya kirata ba da ba zata iya tafiya ta bar ƴar uwarta cikin ciwo ba.
Sai da Dr James ya kammala duba jariran tsab, ya tabbatar da suna cikin ƙoshin lafiya, sannan ya nufi gadon da Zinta ke kwance, shi kuma Dr Mark da suka gama duba jariran sai ya wuce office ɗinsa kawai, dan bashi da lokacin ɓatawa a nan.
A kanta ya ɗan sunkuyo tare da dafa forehead ɗinta da tafin hannunsa ɗaya, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Menene yake damunki?"........ Slowly ta waro idanunta a kan face ɗinsa, idanun nata sun yi jajir saboda azaban ciwo. Muryanta na ɗan rawa ta ce. "It's time for my menstruation, cikina ne yake ciwo".
Shiru ya ɗan yi, can kuma ya ce. "Kin shirya mashi ne?"...... Kai ta gyaɗa mashi alamar ta shirya. Hannunta ya riƙo tare da cewa. "Mu je office ki sha drugs a can, hope kin yi breakfast?".
Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a bata yi breakfast ba, dan daga sashen 3D ɗin da ta fito wanka kawai ta je ta yi ta a nasu sashen, bata tsaya dafa masu abinci ba, a wannan hospital ɗin kowacce nurse tana da nata kayan abinci, su suke girkawa da kansu, kullum karshen wata ana kawo masu kayan abinci da komai da komai, kamar dai boarding school, so dayawan lokuta dama sister Zinta ɗin ke masu girki, ita da Maya komai nasu a haɗe yake, tare suke komai.
Hannunta ya riƙo ya taimaka mata ta miƙe, tana miƙewa ta koma ta zauna tana faɗin. "Wash, too much of pain"....... Nisawa ya ɗan yi, baya son wannan ragonta nata sam, amma ya zai yi? Haka take, ya so ace jaruma take tamkar sister Lazy, sai dai ita takasance mai rauni da taushin zuciya ba kamar Lazy ba!.
Rage tsawonsa yai, cak ya ɗauketa suka fito waje, ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, haka ya keta gabaɗaya cikin hospital ɗin har ya isa ga sashen 3D, ya zo ya wuce sister Lazy dake zaune tana ƴan cike-ciken wasu takarsdu.
Bakaramin tashin hankali ta shiga ba ganinsa ɗauke da ita, amma ta daure game da cizewa, a ranta ta ce zamu haɗu ne, sai na maki abin da sai kin tsani kanki kin kuma tsani duniya bakiɗaya.
Shi kuwa bai dire Zinta a ko'ina ba sai saman doguwar sofar dake cikin office ɗin, yana sauketa ya ɗan shafa kanta game da ce mata sorry. Tana kallon fine face ɗinsa ta amsa da thank you. Gaban heater dake cikin office ɗin ya tsaya. Kunnata yai bayan ya duba akwai ruwa a ciki.
Daga nan ya nufi show glass dake gefe, cup ya fitar tare da ganyen green tea, sugar da dik wani abin da zai buƙata, gaban heater ɗin ya sake komawa, da kansa ya haɗa mata tea mai zafi, ya ɗan barshi ya huce, sannan ya ɗauko ya dawo in da take a zaune.
A gefenta ya zauna tare da miƙa mata cup ɗin, ta karɓa tana yi mashi godiya. "Make sure you take it all". Ya faɗa yana miƙewa tsaye, kai ta jinjina alamar to, watau kula yana da daɗi, wlh dik zafin ciwon nan da take ji da ya nuna mata kula sai ta fara mantawa da ciwon, hankalinta gabaɗaya ya karkata a kansa da soyayyarsa a gareta.
A saman chair ɗinsa ya koma ya zauna, ya ɗauki table phone, sister Lazy ya kira, bugu ɗaya ta ɗaga, cike da bada umarni da izza ya ce ta je sashen drugs ta ɗauko mashi naproxen yanzu ta kawo mashi. Ba tare da ya jira amsarta ba ya katse kiran. Tamkar zata fashe, tana wani irin huci ta miƙe, badan bata da tabbacin ba zai zuba maganin ba idan ta kawo da wlh wani maganin daban zata kawo, dan dai tasan zai duba ne, in kuma ya ga ba wanda ya ce ba to da matsala ta sani, ga shi bai iya hukunci ba, sai yasa ka gwammaci mutuwa a kan rayuwa!.
A fusace ta miƙe ta nufi wajen tana huci, shi kuma ya jawo laptop ɗinsa ya fara duba ayyukan da suka yi jiya, wanda yakamata ya sanya hannu ya fara sanyawa, wanda yakamata yai cancel ya yi.
A can ɓangaren kuwa, Sister Maya ce tsaye gaban table na Dr Kamal tana miƙa mashi cup da ta haɗa mashi tea, karɓa ya yi, ta ɗan risina alamar girmamawa, sannan ta juya zata tafi, hannunta ya riko da sauri, cikin sanyin murya ya ce. "Ina zaki je?".
Ras ta ji gabanta ya faɗi, ɗan zazzare eyesball ɗinta a kansa ta fara yi kafin ta ce. "Zan je wajen babies ɗinmu ne, lokacin yi masu wanka yana ta ƙurewa, ga shi ba'a basu madara ba". Tana ɗan sunkuyar da kai ta faɗa. Cikin wani irin karuwan salo ya ɗan jawota ta faɗa jikinsa, ya zaunar da ita a saman laps ɗinsa, ai gabaɗaya ɗan ɗauke wuta ya yi, ita kam sai ji ta yi tamkar bata duniya, ta zaci mafarki take yi.
Haɓarta ya ɗago suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. "Kina ganin ba kamata ya yi ace yanzu naki babys ɗin kike kula da su ba? Ko ke baki son yaran kanki ne?"........ Ai muryanta na rawa, da sauri ta ce. "Ina son babys sosai, ina son nawa ma, kuma ina son waɗan can ma sosai".
Ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi, tamkar mai raɗa ya ce. "Kin shirya karɓar baby in baki? Zaki haifa mun yara kyawawa irinki?"........ Da sauri ta shiga gyaɗa mashi kai alamar e. Sumbatar cheek ɗinta ya yi kafin ya ce. "Na jima ina fatan naga kin haifa mun magada, ga shi yanzu lokaci ya iso"....…. Shiru ta yi, ta gagara yin magana.
Hannunsa ya ɗaura a saman cikinta, yana ɗan shafawa ya ce. "Wannan ɗan karamin cikin anya zai ɗauki twins kuwa?"...... Watau shi Dr Kamal yadda kuka ga Maya haka yake, akwai jarabar son yaran kansa fa amma, kuma shi a tsarinsa idan ya tashi dasa mata cikin zai yi, dashe zai yi mata, dan twins, triplets and quadruplets yake so, baya son ɗaya, shiyasa zai dasa mata.
Me kuke tinanin zai faru idan yasan Maya ba zata taɓa haihuwa ba? Dan shi bai san Dr James ya cire har da mahaifarta ba, ya saka burin haifar yara kyawawa kamarta da ita. Watau akwai wani gagarumin yaki a hospital ɗin nan dik ranar da Dr Kamal ya gano bata da mahaifa, shikenan ba zai samu magada ba, har na hango kalar guguwar da zata tashi!.
Ɓoye fuska ta fara yi a jikinsa, ta sunkuya tana ɗan murmushi, irin maganar tai mata nauyi. Haɓatar ya ɗago da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma yana shafa bayanta izuwa kan mazaunanta, ya ɗan kwanto da gefen fuskansa a kan hair ɗinta. Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin daga bisani ya ce. "Jeki kula da babys ɗinki, anjuma in mun tashi aiki ki zo mu tattauna".
Ai da sauri ta miƙe tamkar wacce ke kan ƙaya, dan dama ya sakata wani hali, bata taɓa zatan zata jita a jikinsa ba. Waje ta nufa tana ɗan kame jikinta, binta da kallo ya yi yana jin wani irin sonta na ƙara ratsa shi. Dab zata fita ta ɗan waigo dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa ido, kashe mata ido ɗaya yi, hakan yasa ta juya, da sauri ta fice tana murmushi, dimple ɗinta irin na Leo yana lotsawa gwanin burgewa.
Tana zuwa ta isko wasu babys biyu suna kuka, an masu wanka an shiryasu tsab. Ɗaukansu dikka biyu ta yi, ta ɗaura ɗaya a shoulder ɗinta, ɗaya a cinyarta, ta fara jijjiga babys ɗin, da kyar wanda yake kan cinyarta yai barci, a hankali ta kwantar da wanda yake hannunta yana ɗan kuka, ta miƙe ta mai da wanda yake saman laps ɗinta saman gadonsa, ta dawo ta ɗauki ɗayan, tana jijigasa tana zarya a cikin ɗakin, sai take jin tamkar darling ɗinta ne, da yake kunga shi ne rigimammen yaro, so wannan mai kuka na yau ta ji kamar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 61 Chapter of 95