kafin ya miƙe tare da kashe wayar tasa, sannan ya dawo cikin ɗakin. Still dai idanun Leo biyu yana karance-karance da nazartan makaman da aka koyar da su yau. Ko ɗago kai bai yi ya kalli Zaynash ba, yana cigaba da abin da yake yi. Shi kuma Zaynash sai kallonsa yake yi har ya isa saman bed ɗinsa, ya kwanta tare da jawo bargo zuciyansa cike da tinanin yadda zai rayu a GIDAN SOJA. Ya so ya ɗan yi karatun abin da aka koya masu ɗazun kafin ya yi barci, sai dai ina, gajiyar wahalar da suka yi tasa barci ta yi awon gaba da shi. Shi kuwa Leo ya yi karatu har 1 na dare, kafin ya miƙe ya ɗauro alwala, ya zo ya yi nafilfilinsa, daga karshe ya rufe da shafa'i da witiri kafin ya kwanta dan ɗan rintsawa shi ma!.
4:30 ASUBA.
Wannan busa ta jiya ita ta tada su, sun sha mamakin ganin yau ma Leo idanunsa biyu yana zaune a tsakiyar gado yana duba waya. Tambayar kansu suka shiga yi wai shi wannan baya barci ne?. Basu san yanayi ba, amma tin 4 yake farkawa, kuma sai 1 yake kwanciya, barcin 3h yake yi.
Da wani irin ciwon jiki Vash ya farka, ga in da aka zane shi jiya ya yi ruɗu-ruɗu ya kumbura, idaninsa jajir, jikinsa dik babu kwari. Da kyar ma ya iya tashi, intently ya diro kasan bed ɗinsa, cikin wani irin matsanancin hali ya nufi toilet ba tare da ya yi wa kowa magana ba, shi kaɗai ya san me yake ji.
Dirowa ƙasa Zaysh ya yi ya nufi toilet shi ma, jikinsa dik tai tsami. Noor kam komawa ya yi ya kwanta, har da kukan shi jikinsa ciwo yake yi mashi, dan haka wlh ba zai iya tashi ba. Wanka su Zaysh suka yi tare da fitowa suka shirya. Leo already ya yi wanka ya shirya, dan tim 4 ya tashi, yanzu kuma 4:30, wannan 30 mins sun ɗaukesa shiryawa.
Bayan sun kammala shiri ne Vash ya ce bari ya tashi Noor. Zaysh dake ƙoƙarin ɗaure jakansa ya ce. "Ka kyalesa ba, zai tashi da kansa ne"....... "No brother, kasan halinsa, bari in tashesa kada a mashi duka"........ Cigaba da abin da yake yi Zaysh yai bai sake yin magana ba.
Slowly Leo yai switch off na wayarsa tare da ajiyeta a saman bed ɗin, ya ɗauko littafin karatun makamansa na jiya ya diro ƙasa da shi, jakansa ya buɗe tare da mai da book ɗin, sannan ya shinfiɗa bed ɗinsa da kyau, ya naɗe bargonsa, ya ɗauko army p-cap sabuwa daga cikin jakan ya sanya a kansa, daga nan ya nufi waje ba tare da ya kalli in da suke ba.
Da kallo suka bishi har ya fita. Vash ya ce. "Awww ashe fita ta kofa yake yi, all though ɓacewa yake yi"........ Harararsa Zaysh yai tare da cewa. "Baka da hankali, dama fita yake yi mana, wani hanya yake bi shi ne abin mamakin". Ya kai karshe tare da karisa ɗaure jakan nasa, ya ciro biscuit guda ɗaya, sannan ya nufi waje.
"Wait for me". Vash ya faɗa yana nufar bed na Noor. "Yi sauri". Cewar Zaysh da ya tsaya ta waje a bakin door...... Yana tsaye a wajen sai ga makwaɓcinsu Unays ya dawo zai shiga cikin ɗaki da gudunsa. Binsa da kallo sosai ya yi, a nan ya fahimci dik yadda aka yi daga wajen motsa jiki yake, watau dan ya zo na farko a daren ma baya barci? Fita yake hora kansa? Tab lallai ya fisu zalama wannan, kai kai kai, ya zo da sabon salo fa.
Shiru ya yi yana tinani anya shi ma ba zai fara hora kansa ba kuwa? Da daddare idan kowa yai barci. A daidai lokacin Vash ya dafasa tare da cewa. "Let's go, Noor yaki tashi"....... "I already told you that ba zai tashi ba, just leave him, bodynsa zai faɗa mashi".
Vash yana da tausayi ne sosai, sai ya ɗan yi jim, fuska da alamar tausayi ya ce. "But bai kamata mu kyalesa ba ai"..,........ "Saboda kai ne ubansa?". Zaysh ya faɗa. Da sauri Vash ya girgiza kai. "No, amma a nan we're brothers, mun zama ƴan uwa tin da babu iyaye".
Gaba Zaysh ya yi tare da cewa. "Ai sai ka tsaya kada ka tafi tin da Noor bai farka ba, kai waye ma ya ce maka a gidan soja lokacin horo ana taimako ne? Ko da yake kai sabon zuwa ne, bari ka fara gogewa a nan ne ina ga in ka taimaki wani aka baka horon da sai ka kwanci mutuwa zaka gane me nike nufi". Yana tafiya yake wannan magana. Da sauri Vash ya rufa mashi baya zuciyansa cike da tausayin Noor.
Kai tsaye masallaci suka nufa, a lokacin har an kira sallah, ana shirin tada kabbara ma.
Bayan sun yi sallah sun fito, kowannensu sai miƙa yake yi, saboda wahalar da aka sha jiya, jiki dik tsami, daga masu cewa wash, sai masu cewa ash, sai kuma masu cewa bayana, abinku da farin shiga.
A gabansu Captain ya tsaya cikin tsantsar jarumta da nuna dakan jiya ne shi, cikin kakkaifar murya ya ce. "1, 2, 3 start!" Cikin ɗaga murya.
Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA...... "We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom's call, for justice true, Our oath is strong, we'll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle's won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!".
Suna kai ƙarce ba tare da ɓata lokaci ba ya ce."Yau ce ranarku ta biyu a GIDAN SOJA, yau ma zaku sake maimaita horon jiya ne har na tsawon sati biyu, amma na yau za'a fara karfafa maku horon ne domin juriya da jajircewa wahalarku ta karu, horon yau ba kamar ta jiya bace ba, da ɗan banbanci, a yau dole zaku yi gudun kilo mita biyar ne saɓanin na jiya biyu, kuma a yau akwai lokaci, lokacinku zai fara kirgawa ne daga yanzu, dan haka ku bada himma, ku ɗauki waje, ku shirya!!!". Ya faɗa da karfi alamar su karfafa zuƙatansu, sannan ya ɗan dakata da maganar yana bin fuskokinsu da kallo. Can ya tsayar da kallonsa a kan Noor dake tsaye a karshen line ɗin jikinsa jike da ruwa, yanzu ya iso wajen sai haki yake yi, irin ta jiya aka sake maimaitawa, yaki tashi, da Commander ya taka shi kuma ya firgita ya sume masu a wajen, aikuwa Commander yasa aka kaisa wajen tap aka mashi wanka da ruwan sanyi, irin dai jiya. Ga shi bawan ALLAH dik ya yi tsuru-tsuru kamar anwa akuya wanka da ruwan ƙanƙara, gwanin ban tausayi wlh.
Shiru Captain ya ɗan yi, ya kalli Noor ya kuma saci kallon Leo dake gefensa ya zura hannaye a aljihu kamar mai tinanin wani abin ya yi shiru.
"Na sake maimaitawa. Yau ba kamar jiya ba, yau zaku yi gudu na tsawon kilomita biyar ba tare da tsayawa ba, dan kuna da lokacin dake kirgawa wanda in ya cika baku kai madakata ba, to dik wanda ya rage a baya, sai ya sake farawa daga farko kuma a wannan adadin lokacin ba karawa, ya sake gagara iyawa zai sake farawa, dole sai ya yi a wannan lokaci da aka ɗeba mashi ko kwana zai yi a nan, kuma babu juyawa!"........ Ya sake maimaita jawabinsa ne saboda Noor, saboda ya kalli gabaɗaya yaron hankalinsa baya a kansu, yana firgice sosai.
"Ready!". Ya sake faɗa in a hash way.
A take suka kara kamewa suna ɗaukar harama. "Go!!". Cikin ɗaga murya ya faɗa, cikin zafin nama suka bazama da gudu suka nufi hanya. Da farko-farko su Noor an zage sosai, dan yana sahun ƴan gaba-gaba. Da gudu ta yi gudu kamar kilo mitna uku haka, sai ga shi ya fara baya-baya.
Ba shi kaɗai ba, dayawan sojojin sun ja da baya daga wannan gudu, bayan kamar mintuna 10 suna gudun, gwiwowinsu sun fara kerma, amma ba wanda ke da damar tsayawa, dole su yi gudu in ba haka ba su faro daga farko, a wannan waje ne ake cewa BA SANI BA SABO!.
A daidai wannan lokaci matasa uku suka zube gwiwowinsu a kasa, sun gaji ba zasu iya cigaba da gudu ba! Cikin waɗan da suka zube gwiwowinsu har da Noor, saboda bai taɓa yin gudu haka ba, ba zai iya jura ba, jiya ai tafiya ce ba gudu ba!.
Suna faɗuwa Captain dake biye da su a baya yana isowa yasa wasu zaratan sojoji su ɗaukesu aka mayar da su can farko su fara. Da farko Noor ya ɗauka wasa ake yi da ake cewa in suka faɗi zasu faro, bai san a GIDAN SOJA babu wannan wasa ba! Magana ɗaya ake yi babu ƙari! Lallai shi ma a yau ya shaida cewa babu tausayi a GIDAN SOJA, nan ya fara kuka da hawayensa yana faɗin a barsu su cigaba kada su fara daga farko! Sai dai babu wanda ya saurare shi, suma sojojin da aka sanya su ɗaukesa ba imani ne da su ba, suka ɗaukesu suka mai da su farko, kuma suka tilasta masu gudun dole ko su sha zabga-zabgan bulalu. Kafafun Noor tamkar zasu ɓalle, jikinsa har yana wani irin kerma! Su Zaynash har sun kai in da madakata yake su kuma Noor yanzu suka sake farowa. TO MU BI BAYAN SU ZAYNASH MU GA NI, KAFIN DAGA BAYA MU DAWO BAYAN NOOR.
Suna isa madakata kowannensu ya dakata, masu kwara amai a gefe suka fara kwararawa, masu zubewa ƙasa dik suka zube suna nishi sama-sama. Shi da kansa Leo yau sai da ya durkusa ƙasa, saboda ya ci wahala.
Captain yana zuwa ya ce ya basu mintina uku da su miƙe su sha ruwa sannan su yi readyn cigaba da gudu dan komawa in da suka fito. BABBAN MAGANA!.
Take wasu zuƙatasu ta fara karaya da aikin soja, wasu suke jin tamkar su koma gida, ba zasu iya jurar wahalar nan ba, wai ba'a barinsu su huta. Basu san idan har za'a barsu suna hutawa to ba amfanin training ɗin ba, saboda jikinsu ba zai saba da wahalar har ya bada juriya ba, wannan hutu da zasu dinga yi zai rinƙa haifarwa da garkuwar jikinsu ƙasala da rauni! Shiyasa ba hutawa, daga wannan sai wannan har sai jikinsu ya karɓi azaban sosai!.
-------------------------🔥
A gaggauce suka sha ruwan da aka shirya masu a wajen tin kan su iso, Sannan suka dasa daga in da suka tsaya, a hanyarsu ta komawa kilomita 3 daga farkon farawa suka ci karo da su Noor suna yi, yana kuka tamkar ransa zai fita, baya ganin gabansa, gudu kawai yake yi, da alama ya sake faɗuwa aka mayar da shi daga farko, dan da ya ci ace sun wuce kilo mita 4 yanzu.
Zaynash da Vash sun yi mugun tausayawa Noor, suna jin tamkar su je su karɓa mashi, amma ba dama, Vash har idanunsa suka ciko da kwallah sosai.
Bayan sun koma sai kuma me? Crawling under fire simulation, watau rarrafe karkashin igiyar da suke wa laƙabi da igiyar wuta. Ba kamar jiya normal igiya ba! TASHIN SENSE!.
Cikin wani fili suka nufa, inda aka shimfiɗa igiyoyi masu ƙarfin gaske, inda dole su rarrafa a ƙarƙashinsu cikin ƙasar laka. Ga wasu zaratan sojoji a both side dake watsa masu ruwan kamar na sama dan ƙara wahalar rarrafen. Sannan dole su yi wannan rarrafe na tsawon mita 30 ba tare da tashi ba, suna tashi waɗan ban igiyoyin ƙayoyi ne a jikinsu, irin karafunan nan ne masu ƙayoyi, dik zai cake masu jiki, shiyasa ake danganta wajen da fire, saboda wahalarsa, idan ka yi kuskure waɗan nan kifiyoyin suka cake maka hannu da sassan jiki ka zub da jini, ko ka ji ciwo kuma dole ne ka cigaba da yin horo.
Haka suka afka wannan waje suka fara yi, a wannan lokaci matasa dayawa sun yi kuka, kuka sosai tamkar ba maza ba! Sun ji azaban da basu taɓa zata ba!. Sai dai kuma har suka kammala babu wanda aka samu ya tashi, sun jajirce, dik da suna kuka sun jure sun cinwa in da ake so!.
Bayan nan kuma sai aka ɗaukesu zuwa wani katafaren waje, aka tsaitsai da su shiru, sannan wasu sojojin suka zo suka hau ɗaɗɗaure masu idanu da hankey na sojoji. Zasu aiwatar da blindfolded navigation horon laluɓe ne a cikin duhu, saɓanin jiya na sallaƙa tsaunika ƙanana.
Bayan an ɗaure masu idanu babu damar kallo ko kaɗan, sai aka kwashesu a motar sojoji zuwa cikin daji mai ɗan duhu saboda cikar dogayen bishiyoyi da manyan itatuwa masu ganye, dik a cikin Barrack ɗin wajen yake, dama waje ne na musamman domin horar da matasan sojoji.
A nan Captain ya umarcesu da kowa ya tsallaka duwatsun dake gabansa, ya yi dik mai yiwuwa domin fitar da kansa daga cikin wannan waje. Ya kara da cewa, akwai duwatsu, sannan akwai itatuwa, akwai ramuka, wasu ramukan da ruwa, wasu kuma babu, dan haka su fitar da kansu daga wannan daji.
Bayin ALLAH, ba gani da ido, ga shi kwata-kwata bama su san filin ba, bare ace sun san ya yake zasu iya kwatar kansu, yanzu fa sai dai su dogara ga jin sautin umarni Captain, da kuma jin sautin nunfashi ƴan uwansu da laluɓe cikin duhu. Kuma idan suka tafka kuskure, za a mayar da su su sake farawa ne.
Sun tsorata sosai, dayawa daga cikinsu sun karaya. Da Captain ya ga haka sai ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa. "Wannan horo yana koyar da ku amincewa da kai, zaku iya yakin sunkuru ta hanyar shaƙar numfashin mutum, zaku iya yaki a daji ba tare da tsoro ko fargaba ba, koya maku yadda ake yakin sunkuru ne wannan, zai zamana da numfashin abokin gaba zaku iya farmakarsa, zaku koyi yaki da ji da motsi ne kawai, dan haka get ready!!".
Jin kalamansa yasa sun karfafa zuƙatansu, sun jajirce sosai, sun kuwa kara ɗaura ɗamara, take suka sauke ajiyar zuciya. Nan Captain ya umarcesu da su fara. Laluɓe suka fara yi, wasu na capko wasu, wasu kuwa tin ba'a je ko'ina ba sun fara faɗuwa ƙasa, wasu sun fara buguwa da jikin itace.
30 mins kawai garesu su fita daga cikin wannan daji, hakan yasa suka kara mai da hankali sosai, amma sun jijji ciwo ta hanyar faɗuwa, buguwa da dutse, buguwa da itace, dik sun fita hayyacinsu kafin su fito daga wannan waje.
Suna fita aka kwance masu idanu, kowannensu da sauri ya fara bin in da yake da kallo, suna nishi sama-sama. Ruwa aka basu kowa ya sha, sannan aka ce 5 mins garesu. Izuwa yanzu sun fara sabawa, dan haka basu ji wani tsoro ba da aka ce 5 mins garesu.
Wasu ma irinsu Leo, Zaynash, da Unays sun yi gaggawar riga kowa miƙewa domin cigaba da karɓar horon. Matasan sojoji da dama sun ji ciwo a hannun da gaban goshi, amma Captain bai nuna kamar ya gani ba dik da ya ganin, ya umarcesu kawai da su tashi su koma cikin motocin da aka kawosu bari su koma.
Da kyar wasu suka iya tashi, amma ko kaɗan babu alamar tausayinsu a idanun manyansu, kamar ma basu san suna yi ba! Kuma da dik wani motsinsu a idanun Generals na sojojin ne.
Sun yi matuƙar mamakin ganin yadda aka ɗaukesu zuwa wajen wani bene mai bala'in tsawon da ya fi na jiya, ya fi dik benayen dake GIDAN SOJA tsawo sosai. Kallon-kallo suka fara yi a tsakaninsu kafin su mai da kallonsu a kan Captain dake tsaye ya rungume hannaye a kirji. Ganin suna kallonsa yasa ya yi masu nuni da benen a kan su haura. Dole suka fara haurawa da gudun gaske, dan ba wasa ake yi a nan ba, dik jigatar da suka yi ɗazun basu bi ta kansa ba.
A nan ana koya musu yadda za su shawo kan tsoro ne. Dole su hau kan bene mai tsayi su tsaya ba tare da motsi ba, sannan su tsallaka wani igiya daga gefe zuwa gefe, ma'ana daga wannan bene zuwa wani bene.
Wanda ya nuna tsoro, sai a barshi a can sama har sai ya cire tsoron gabaɗaya. Dayawa daga cikinsu jikinsu ya yi kermar tsoro, amma dole suka jajirce, dayawa daga cikinsu daga kan wannan horo zuƙatansu ta fara bushewa, take suka daina jin tsoron mutuwa, ace ka hau bene can sama, sannan ka bi ta kan igiya ka tsallaka daga wannan bene zuwa wani? Ai dole zuƙata su fara bushewa daga tausayi da tsoro!.
-------------------------🔥
Bayan dik wahalar da suka sha, sai aka koya musu rikon ƙananan bindigogi wanda aka karantar da su jiya, su za'a sanyasu rikewa da yadda ake sauya harsasai cikin minti biyu kacal. Idan mutum ya kasa cika wannan lokaci, sai a hukunta shi da ƙarin horo hawa bene ko rarrafawa cikin ƙasa or taɓo. Wanda ya fi kwarewa, shi ake ba damar jagorantar abokan horonsa, hakan yasa suka zage dantse.
Captain ya kura masu ido sosai yana kallon motsin kowa, tin daga kan yadda ya ga Leo yake canza bullet na bindigarsa ya gane ba yau guy ɗin nan ya fara rike bindiga ba, lallai dole yasanta sosai, saboda a ƙasa da minti ɗaya ya canza bullet ɗinsa, ba Captain kawai ba, harta manyan jami'an dake kula da dik motsin matasan sojojin sun razana da ganin abin da Leo ya yi, har ya sanya masu shakku a kansa, suka fara jin anya kuwa ba wata a ƙasa kuwa? Dan shi ba ɗan kasansu bane, saboda GIDAN SOJAN AVARIS da ya fita daban a duniya ne yasa ya ce zai yi appley a nan, zai zo ya karɓi horonsu da kyau, a gida ma sun ki, amma ya kafe shi fa lallai sai ya zo, da suka ga ya kafe kawai suka sake mashi.
In takaice maku labari haka ranansu ta biyu ma ta kasance a GIDAN SOJ, suka karɓi horo kamar jiya. Bayan horo, kamar jiya sai karfe 8:30 bayan sallar isha'i suka koma ɗakunansu. Suna shiga suka yi wanka suka hau shirin kwanciya.
Sai dai da suka shigo basu ga Noor ba, kuma basu tambayi ina yake ba. Suka hau shirin kwanciyarsu, suna cikin shiri ne ya shigo ɗakin tare da rakiyar wasu sojoji guda biyu, ya ji ciwo ne a kafa sosai a dajin da aka kaisu aka ɗaure masu ido, ya taka wani karfe ta fasa mashi kafa, ciwo ne da ba za'a iya kyalesa ba, dole suka ɗaukesa zuwa military hospital ɗinsu aka wanke kafar aka gyara mashi kada wata cuta ta shiga.
Sojojin suna rakosa suka juya suka fita, shi kuma ya kariso ciki, da sauri Vash and Zaysh suka yi kansa, rirrikesa suka yi suna tambayansa me yake faruwa. Idanunsa a kumbure saboda uban kukan da ya ci, kyawawan pink lips ɗinsa irin na mata sun ciza sosai, saboda ya yi ta ciccizasu a lokacin da yake jin azaba, har gefen lips ɗin nasa ta fashe saboda damketa da hakori da yake yi.
Kama shi suka yi zuwa saman bed, suka kwantar da shi tare da cigaba da tambayansa me yake faruwa. Idanunsa ya rufe kafin ya kwashi dik irin azaban da ya sha ya faɗa masu. Gudun farko kawai ya maimaita sau biyar, rarrafawa cikin kasar laka ya yi sau uku, a wannan daji sai da ya ya dinga sakewa har sai shidda, a nan ne ya taka wani karfe mai kaifin gaske ta fasa mashi kafa ta jefe wajen idon sahu ba ta wajen takalma ba.
Tin da ya fara basu labari suka yi mugun tausaya mashi, sai sorry suke ce mashi. A tare suka haɗa kai, suka shirya mashi ruwan wanka, sannan suka tallafa mashi ya shiga toilet dan yin wanka. Dik abin da suke yi Leo yana zaune yana nazarin makaman da aka kara koya masu yau, na jiya ne aka sake maimaita masu da kyau dan ya shiga kansu yadda yakamata. Bai ko ɗago ido ya kallesu ba, dan shi ba abota ya zo yi GIDAN SOJA ba! Horo ya zo karɓa.
Bayan Noor ya kammala wanka da shirinsa tsab, kowannensu ya haye saman bed ɗinsa, sannan suka fito da wayoyinsu kamar jita. Noor ne ya fara kunna wayansa, dan kafin a basu wayoyin sai da aka shar'anta masu cewa da daddare ne kawai aka lamunce masu su kunna waya, dan haka in zasu kwanta suka kashe wayar basa sake kunnanta sai sun dawo ɗakin bayan horo.
Shi dai Zaynash yaki fito da wayansa, dan yana jin kunyarsu, dikkansu wayoyinsu manya-manya na ƴaƴan manya, nasa ce kawai matacciya, sai yake jin kunyar fitarwa.
Noor yana kunna wayar ya kunna data, nan sakonni suka hau shigowa kamar ruwa, dik kuma na ƴan uwansa mata ne dake ta turo mashi saƙon kukan sun yi kewansa.
Bai bi ta kan kowannen saƙo ba, kai tsaye ya shiga kan number da aka sanya my dad. Video call ya dannawa wannan number yana ɗan gyara kwanciyarsa da kyau, sai ciza laɓɓa yake saboda zafin da jikinsa take yi mashi.
Bugu ɗaya aka ɗauka, dik da ɗakinsu da haske amma fuskan Noor bata fita sosai a call ɗin ba, hakan yasa ya kunna hasken wayar ta gaba. Yana sauke idanunsa a kan wani kyakkyawan mutum mai ɗan matsakaicin jiki, suna kama sosai, fari tas da shi, ga idanu dara-dara farare tas, da alama mutumin ma a kwance yake, kyakkyawan gaske sosai.
Harara ya dallawa mutumin kafin ya ce. "My dad baka yi barci ba?"....... Wani irin cool smiling ya saki kafin ya amsa da. "I'm waiting for your call, how can I sleep?".......... Sake hararansa Noor ya yi. "Daddy gidan Soja akwai wahala, ba zan iya jura ba, ka zo ka ɗaukeni". Ya kai karshen maganar cikin raunin murya. "Pleasure very soon zaka saba".... Zai yi magana daddy yai sauri sake cewa. "No, kawai ka faɗa mun success da ka samu a yau?".
Yana turo baki ya amsa da. "Alot my hero". Wani irin ƙayataccen murmushi dad ya saki kafin ya ce..... "Thats is my son, I know you will succeed, try to bring us a good result"..... "I will try my best dad, where's my Auntys?"....... "They're not here, they're in their room, but Lisa bata nan"....... Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Dad here is my friends da na haɗu da su a nan, they help me and they're so king and perfect". Ya faɗa tare da juyar da wayansa ya nunawa daddy bed ɗin su Zaynash dake kwance shiru.
"Zaynash this is my dad, ku gaisa". Ya faɗa yana sauƙiwa kasan bed ɗin intently, ya zo ya miƙawa Zaysh wayar. Karɓa ya yi, a mutunce suka gaisa, daga nan ya karɓa ya miƙawa Vash ma suka gaisa. Dik da basu magana da Nirash sai ya ji yana son kai mashi wayar su gaisa da daddynsa, wata zuciya ta ce a'a kada ya je, wani kuma ya ce ya je Nirash zai amsa. Daurewa yai tare da nufar bed ɗin Leo.
Sallama ya yi mashi tamkar wanda zai shiga wani ɗakin saɓanin yadda ya je wajensu Vash ba sallama. Ai cikin zafa su Vash suka ɗago kai suna kallonsa, suna jiran su ga Leo zai karɓi wayar ne ko kuwa.
A gaban bed ɗin ya tsaya tare da cewa. "Here is my dad, ku gaisa"...... Leo yana kwance shiru, ya kifa littafin tasa a fuska kamar yana barci, kuma idanunsa biyu,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 95