hukuma, dan haka sai ya ce. "Ku ɗaukesu zuwa tsakiyar teku, dik ku harbesu su faɗa cikin ruwa, kada ku barsu da rai, dan cigaba da ɓarna zasu yi, kuma kun kyauta da baku taɓa kayan ko kuce zaku ƙonasu ba, da duk abin da kuka yi wa kayan a kan ƴan ƙasan za'a fanshe".
Cike da rashin fahimta ya ce. "Brother a kan ƴan ƙasan za'a fanshe shi kuma?".
Miƙewa zaune Aryan ya yi. "Yeah, a kansu za'a fanshe, ai dik wani asarar da ka yi wa gwamnati ko ka yi wa manyan sanannu a duniya fa to a kan al'umma zasu fanshe, su basu san asara ba, dan zasu ninka cutar da suke yi wa ƴan ƙasa ne, su tsananta kidnapping, su ninka farashin kaya, su kwashi mutane fiye da kima a makarantu su ce sai an biya miliyoyi, dole al'umma su fitar da kuɗi su biya, idan suka biya kunga ai sun fanshe a kansu, ka lura dik lokacin da gwamnati ta yi wani asara to a cikin wannan ɗan tsakanin zaka ga an ninka satar mutane, an ninka fashi da makami, an ɗaga farashi abubuwa".
Ya ɗan nisa game da cigaba da cewa. "Gara da baku taɓa kayan ba, dan bashi da wani amfani ma ku kona, dakatar da mai laifi ya fi dakatar da kayan laifi! Lallai ka zaƙulo dik masu hannu a cikin lalacewar kasar, ka fiddosu ka hukuntasu, ka gwada masu jininmu ne kai, ka jagoranci tawagar da zasu tsabtace garin tas daga ɗauɗar miyagu".
Ya ALLAH muma ka turo mana waɗan da zasu jagoranci tawagar kawo mana gyara da canji yanayi, ko a cikin sojojinmu, ka a cikin ƴan siyasarmu, ko a cikin malamai, ko a cikin matasa, koma a ina ne ALLAH ka turo mana su!.
Sosai Leo ya ji kwarin gwiwa da kalaman Aryan, ya yi mashi godiya, Aryan yai mashi fatan alkhairi kafin su yi sallama da juna. Dik zancen da suke yi Noor yana jinsu, dan a h-free Leo ya sanya wayar. Ɗago ido ya yi ya kalli Noor, sai ya ce. "Mu ajiye batun aiki a jefe, less talk about Islam, yakamata ka fara koyan wasu abubuwa".
Kai ya jinjina game da cewa. "Ina son hakan, kuma ina son my Juliet ta musulunta ita ma"........ Lion ya ce. "Yakamata ku yi aure yadda addinin musulunci ya tanada"........ Ɗan zarowa Leo idanunsa ya yi, sai kuma ya ce. "Kamar ya kenan?".
Bayani Leo ya hau yi mashi dallah-dallah. Ya gamsu matuƙa, sai ya ce to zai bata sadaki a nan, Leo yai mashi alƙawarin zama waliyinta idan ta amince, shi kuma zai kira daddynsa a waya ya shaida, ga shedu Vash da Zaynish, dama shedu biyu ma a musulunci sun wadatar, dan haka a daren yau za'a ɗaura masu ainahin aure.
Sosai Leo ya ji daɗin amincewa da Noor ya yi, ALLAH sarki, kome aka faɗa mashi kan addini hannu bibbiyu yake runguma. Dan haka Leo ya zage wajen koya mashi addini, basu bar wannan waje ba sai lokacin sallar azahar, nan ne suka koma sansaninsu. Bayan sun yi sallah Leo ya shiga ya duba wannan aiki na Arya.
Hayakin dai yana nan yana fita yadda yake, babu wani abin da ya canza a wannan waje, ita kuma Arya a lokacin tana ƙoƙarin samo mashi bayanai kan wajen da aka harbe drone na V, bata faɗa mashi an harbe ba, dan ita bata dogon bayani sai dai ta bada result a aikace, tana son in ta gama bincike ta tattara komai, sai ta bashi good result da ba sai ya sha wahalar tambaye-tambaye ba.
Bayan ya duba ya fito ne suka haɗu da Zaynish, nan suka wuce bakin ruwa a tare da Noor and V. Da suka zauna saman duwatsun bakin ruwa ne Zaynish ya sanar da Leo batu kan yarinyar can, jinjina mashi Leo ya yi kafin ya ce. "Ku ajiyeta, idan muka gama mission muka koma sai a miƙata wa gwamnati ita a nemo iyayenta a hukumance"...... Na'am suka yi da wannan batu.
Daga nan suka cigaba da tattaunawa kan aikinsu, kowannensu yana kawo hasashensa da zurfin tinaninsa kan menene a wajen wannan hayaki. Suna tsaka da hirar ne sai ga team 2 sun zo wajen, su Unays kenan. Da ido Leo ya cewa ƴan room ɗinsu su yi shiru kan wannan case ɗin, yanzu Leo ya ƙara hankalta da mutane tin da suka kama sojojin ruwan nan, da Captain ya daka mashi warning kan aminta da mutane ma sai ya kara kame kansa, dama can su basa yarda da mutane ai kun sai.
Da su Unays suka zauna sai Noor ya ɗauko masu wani hira daban kan aiki, ya fara neman jin hasashensu kan wannan mission ɗin....... A haka suka cigaba da hira har dare, lokacin sallah ne kawai yake tada su.
After some hours.
Gari ya yi sanyi, sojojin dake sansanin gabaɗaya suna wajen wuta suna shan ɗimi, matan ma suna tare da su except Arya dake cikin ɗaki tare da wannan yarinyar nan, ta baiwa yarinyar abincin darenta sun ci tare, ta ƙara yi mata wanka, yanzu haka tana zaune a tsakiyar tantinsu rike da laptop tana ta ƙoƙarin tabbatar da abin da take zargi a kan wannan waje da aka harbe drone na V.
Yarinyar kuma ta kwanta a ƙasa kusa da ita, sai Arya ta ɗago kanta ta ɗaura a kan cinyarta, ta rasa meyasa take son yarinyar sosai take kuma tausayinta. Yarinya har ta fara murmurewa kyanta na kara bayyana.
A wannan lokacin ne sojojin team 1 suka fita da waɗan nan Navy ɗin ta bayan tantunansu ba tare da kowa ya sani ba, dikkansu suka ɗauki mutum ɗaiɗai suka wuce. Kai tsaye bakin ruwa suka nufa. Suna tafiya cike da jarumta, dik sauran sojojin ba wanda yasan meke wakana, suka isa cikin ruwa ta baki kaɗan. Leo yasa pistol ɗinsa ya harbesu ba tare da sun farfaɗo daga alluran barcin da aka yi masu ba, suka jefa gawarwakinsu a cikin ruwa, suka tsaya sai da suka tabbatar gawarwakin sun bi ruwa, sannan suka juya suka koma sansani.
Cikin tantunansu suka shiga, suka canza kaya zuwa marasa nauyi na barci, sannan Vash, Zaynish and Noor suka fito zuwa wajen wutar nan. Leo kuma sai can ya fito game da zuwa bakin wutar.
Dik suka mimmiƙe suka sara mashi, bai yi magana ba ya kira V ta hanyar yi mata alama da hannu, da sauri ta nufesa. A gefe ya tsaya ta bisa, cikin wannan natsuwa tasu ya faɗa mata abin da suka shirya da Noor. A daidai lokacin Noor ya iso wajen. Leo baya son Noor ya fara aikata ba daidai ba daga shigansa musulunci shiyasa yake son ɗaura wannan aure, dan yasan Noor ba zai hakura da daina taɓa V ba tin da sun saba.
Noor na zuwa wajen ta rungumo shi game da faɗa mashi ita dik hukuncin da ya yanke ta yarda da shi. Ya ji daɗin hakan, ya ɗauko sadakin diamond chain ɗinsa ya bata, ya kira daddynsa a waya ya haɗa shi da Leo. Kun san daddy farincikin yaransa kawai yake so, dan haka ya aminta da wannan haɗi, sai dai fa ya ɗan tirge da farko, ya ce meyasa Noor zai shiga wata addinin ba tare da ya nemi shawarinsa ba?.
Hakuri Noor ya dinga bashi, daga nan komai ya wuce. In taƙaice maku a wannan dare aka ɗaura masu aure irin na addinin musulunci ba tare da sanin GAT ba, sai dai sanin Aunty Lisa da ita dama kun san ai tana bayan Noor koma me zai je ya zo, tana nan dai tana cin amarcinta abinta, ta ƙara kyau, yanzu da GAT yaga su Arya sun yi dogon zango ya fito da batun auren nasa, yanzu haka ana ta shirye-shiryen dinner partyn da za'ayi a cikin barikin.
V bata musulunta ba, Noor bai ce ta musulunta ba, Leo ya ce ya kyaleta da kanta zata ce zata musulunta, kuma wannan musulunci shi ne daidai, ba wanda za'a cewa mutum ya yi ba, a cewar Leo in dai tana zaune da musulmai tana ganin kyawawan halayensu tsab zata musulunta.
Bayan sun ɗaura auren ne, Noor da V suka koma wajen wutar, Vash and Zaynish suka rufa masu baya, shi kuma Leo ya koma cikin tantinsa dan aikin dake gabansa, bashi da lokacin zama a bakin wuta dan jin ɗimi shi, yasan me yake gabansu. Arya ma dai irinsa ce, bata da wannan lokacin, aiki ya fi mata komai muhimmanci.
A wannan lokaci Manassa ta ɗauko rucksack ɗinta, ta zo ta da nufin ta gyarawa Zaynish hannunsa ta sake wanke mashi. Da sauri Angelina ta bita, a kusa da shi suka zauna, ya ware masu tafin hannun nasa, ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon farin yashin dake wajen.
Kwance bandejin dake hannunsa Manassa ta yi, ta wanke mashi hannun game da zuba mashi magani, ta sanya sabon cotton kafin ta mayar da bandeji ta rufe mashi. Sai sorry Angelina take ce mashi, shi kuma ko kaɗan bai ɗago ya kalleta ba.
Bayan sun kammala Manassa ta miƙe ta nufi tantinsu ta mayar da rucksack ɗinta, sannan ta dawo ya zauna a kusa da Vash tana satar kallonsa ta ƙasan ido, while tana chatting da shi matsayin aljana, ya ce mashi taga ya kula mace yau, kuma sai ta hukunta yarinyar.
Shi kuwa ya ce mata. "Wannan yarinyar rayuwata ce, in kika kasheta ni kika kashe, dan haka kin rasani kema". Wani irin musulmin daɗi ta ji, yadda ya ce wannan yarinyar rayuwansa ne, ya rabb, sai ta ji tamkar ta miƙe ta je ta rungumesa, sai murmushi take yi, tama gagara amsar da zata bashi.
Ita kuwa Angelina tana zaune kusa da Zaynish tana aikin satar kallonsa, Unays kuma yana satar kallonta, yana ta ALLAH ALLAH Zaynish ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna.
----------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.
Ko da aka fita breakfast Seraphina ta yi rarrashin duniyar nan Rimsha taki kulata, daga karshe ma miƙewa Rimsha ta yi ya fice waje, zuciyanta baya jin rarrashi ko kaɗan, ita kaɗai tasan waye Aryan.
Tana fita Uncle ya dawo kusa da Seraphina ya zauna, yana kallon kyakkyawan face ɗinta ya ce. "Baki yi kewata bane?". Ɗan turo baki ta yi. "Na yi amma kaɗan".
Haɗaɗɗen murmushi ya sakar mata kafin ya ajiye mata chocolate ɗin hannunsa a saman table ɗinta, chocolate mai heart design, ya yi mugun burgeta chocolate ɗin, ta ɗan zaro idanu a kan face ɗinsa kafin ta ce. "Is so nice, thank you". Ta faɗa game da miƙa hannu ta ɗauki chocolate ɗin.
Zuba mata idanu ya yi, yana binta da wani irin kallon ƙauna mai narka zuciya, yana jinsa a wani irin duniya na musamman. Ita kuwa ɓare chocolate ɗin ta yi, sai taga mai zalar madara ce a tsakiya, ɗan turo baki ta yi. "Daddy ya hanani sha milk". A dame ta ya maganar tamkar zata yi kuka.
Kai wannan shagwaɓar tata yana mugun tafiya da imaninsa fa, ɗan nisawa ya yi game da cewa. "Meyasa ya hanaki shan milk?"......... Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "There was a time da na yi ciwon ciki a school, sai muka je hospital, a nan ne aka ce in daina shan milk".
Hannu ya kai kan eyes ɗinta, ya ɗan janye fatar ƙasa na idanun kafin ya ce. "E kam dole daddy ya hanaki shan milk, anyway ki sha wannan ba dayawa bane ai, ba zai maki wani illah ba". Ya faɗa game da cire hannun nasa daga kan fuskarta.
Ai tana jin hakan ta ɗauki chocolate ɗin ta fara ci, sanyawa a bakinta ta yi zata gutsira ta cire saura kenan uncle ya yi saurin ɗago haɓarta, sai yasa bakinsa ya ɗan gutsira yana kallon cikin kwayar idanunta. Ai bata san lokacin da ta saki chocolate ɗin ya faɗi ƙasa ba, ta fasa sha, ta kuma zazzare violet eyes ɗinta a kansa sosai.
Ganin ta jefar da chocolate ɗin ne yasa uncle ya ɗan miƙe yana ƙoƙarin haɗe bakinsu ya tura mata na bakinsa da ya gutsira. A zabure ta miƙe tana ja da baya. Cike da mamaki ya fara binta da kallo, dan su wannan ai ba wani abin bane a wajensu, meyasa take gudu to?.
"Beb, are you okey?". Ya faɗa yana miƙewa tsaye da kyau. Tana ƙara zazzare mashi idanu ta ce. "Dad ya hana in bar wani namiji ya taɓani, and i promised him that ba zan yi hakan ba, then mom also, ta mun warning a kan irin haka, please sir kada ka sake gigi yi mun irin wannan abin, kada ka sake gigin haɗa bakinmu, i can't tolerate this". Da iya gaskiyarta take magana, babu wasa a kan fuskanta.
Ganin hakan ne yasa ya ja da baya yana ce mata sorry, ya ce ba zai kara ba ta yi hakuri........ "Just go kawai!". Ta faɗa cikin tsiwa tana nuna mashi hanyar wajen chair ɗinsa, bata son dik wani abun da zai ɓatawa daddy Champion namu rai.
Uncle na juyawa zai koma wajensa ta yi gaggawar wucewa ta fito, ta nufi wajen Rimsha, ta yi ta ƙoƙarin dannarta har aka dawo class, yau ko abinci basu ci ba. Haka suka wuni a school babu daɗi, Rimsha taki sakewa su yi hira, har aka tashi school.
Farya ya riga Aryan zuwa, sai ya ce da Seraphina ta zo su mai da ita gida. Tana ɗan murmushi ta ce. "No uncle, ka bari daddy zai zo, ya hanani hawa motar kowa"........... Faryan bai matsa mata ba, ya ɗauki Rimsha kawai, da yake Rimsha jikin babu daɗi ba wani sallamar kirki suka yi da Seraphina ba, baiwar ALLAH jikinta ya yi mugun zafin zazzaɓi sosai, wani irin azababben ciwo kanta ke yi mata, duk ta fita hayyacinta, ta shiga fron seat kawai ta zauna shiru, ƙara bata hakuri Seraphina ta yi game da yi masu bye-bye.
Daga nan Faryan ya tada mota suka wuce suka barta tsaye. After 10 mins da tafiyarsu sai ga daddy ya faka a gabanta, a daidai lokacin kuma Aisha ta ƙariso wajen....... Gidan baya ta buɗe ta shiga tana ɗagawa Aryan gaisuwa. Bai amsa mata ba, hankalinsa gabaɗaya yana a kan Seraphina da taki shigowa, ta yi folding hands ɗinta a kirji tana kallonsa cike da tsantsar so.
Sauke glass na motar ya yi game da cewa. "Kema yau sarautar ce ta motsa irin uncle............". Sai kuma ya yi shiru tunawa da ya yi yanzu kowani magana ya yi rikewa take bata mantawa, dama zai ce irin Uncle ɗinta Zayra'an dake can gida yana zuba masu sarauta ne, sai kuma ya tina tsab zata ce sai ya nuna mata shi, ko ma ta tuhumesa da wani abin.
Dik da bai ƙarisa maganar ba sai da ta titseye shi da cewa. "Daddy wani uncle kuma?"...... Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Wanda na haɗaki da shi a waya ranar"....... "Daddy yaushe zaka zo da shi?". Shiru ya ɗan sake yi, sai kuma ya ce. "Ranar aurenmu zai zo, yanzu dai shigo mu je".
Tana ɗan tura baki ta buɗe ta shigo, ta ɗaura rucksack ɗinta a kan laps ɗinta tana kallonsa. Tada motar ya yi suka nufi gida. Yana parking ta fito tana turo baki, fitowa ya yi shi ma game da karɓar rucksack ɗinta, Aisha ma ta fito suka nufi cikin elevator.
A parlo suka isko Madam da su Aunty Safiyya suna hira, suna ganinsu suka hau yi masu welcome, kai tsaye ɗakin Seraphina ya nufa ba tare da ya yi masu magana ba, ko kallon in da suke ma bai yi ba. Yana shiga ya ɗaura rucksack ɗinta a saman table, ya wuce ya hau saman bed. "Zan yi barci kada ki tasheni".
Tana turo baki, ta kai hannu ta rike waist ɗinta, tana kallon kyakkyawan face ɗinsa kafin ta ce. "My gentle chaos, waye zai yi feeding ɗina lunch?"...... Wani irin kallo ya bita da shi da idanunsa dake rikiɗewa zuwa na mai jin barci sosai, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Aikinki nike yi ne? Maza je ki yi wanka ki je ki yi feeding kanki da kanki, dan kin samu da safe na baki ko?".
Turo baki ta ƙara yi, take ta hau hura numfashi sama-sama tamkar zata fashe da kuka. Zazzaro idanunsa ya yi. "Awwa my cherry, jeki yi wanka sai ki dawo in yi feeding ɗinki, barcin banza, ni ai naki ne, komai nike saboda ke ce"..... Wani irin murmushi ta saki wanda ya sanya shi lumshe idanu saboda kyan da ta ƙara, da sauri ta nufi closet ɗinta.
Nisawa ya yi, a cikin zuciyansa ya ce. "My first love Seraphina, my rigima, my shagwaɓa, my drama, my everything, ALLAH ka mallaka mun ita, kasa tawace". Ya faɗa tare da waro idanunsa kai tsaye sai cikin violet eyes ɗinta a dab da shi.
Wlh ta yi mugun bashi tsoro, unexpected haka, dole ya razana, ga violet ɗin ya ciza sosai, ta zazzaro mashi a dab face ɗinsa, ya lumshe idanu yana tinani bai san lokacin da ta fito har ta iso in da yake ba. Ɗan ja da baya ya yi yana kallonta, a zahiri ko kaɗan ba zaka zaci ya tsorata ba, dan bai nuna alama ba.
Murmushi ta ɗan sakar mashi kafin ta ce. "Daddy ina dubawa ne in ga kayi barci ne ko baka yi ba"...... Harara ya dallah mata kafin ya ce. "To ban yi ba, jeki yi wanka ki zo"....... Dama ta rankwafo kansa ne, sai ta ɗan miƙe tana murmushi.
Unexpected idanunsa suka sauƙa a kan tudun kirjinta da suka bayyana ta wuyan bathrobe ɗin jikinta. Ai ji ya yi barcin nasa ma ya watse, ɗan lumshe idanu ya yi ya sake warowa a kansu, sai kuma slowly ya ɗago da kallonsa a kan face ɗinta dan yaga shi take kallo ne ko yaya. Da sauri ta ɗauke idanunta daga kansa, sarai ta ga in da yake kallo, amma ta yi kamar bata gani ba.
A bayyane ya sauke ajiyar zuciya ganin cewa bata kallonsa, slowly ya dawo da kallon nasa a kan kirjin nata, ya rabb, watau matasan tula-tulan nan nata sun yi matuƙar tafiya da dik wani tinaninsa na yau. Wani irin nyawu ya haɗiya har sai da ƙashin maƙogwaronsa ta harba sama ta sake yin ƙasa. Ita kuma ja da baya-baya ta fara yi tana faɗin. "Daddy ko zaka zo ka mun wankan ne?". Da sauri ya lumshe idanu game da warowa a kan face ɗinta, ta ɗan tsaya a tsakiyar ɗakin tana kallonsa.
"Jeki yi wankanki, akwai lokacin da zan dinga yi maki ɗin yana zuwa". Da kyar ya faɗa saboda nauyi da tongue ɗinsa ya yi mashi. Slowly ya ɗan yi ƙasa da eyes ɗinsa izuwa kan tsala-tsalan cinyoyinta da suke jajir tamkar ka taɓa jini ya fita, suna wani sheƙi, ga shi kunsan gaban bathrobe ɗin a buɗe yake, sai wannan igiya tasa da ta ɗaure tsakiya, so sama wajen wuyan a buɗe, haka ƙasa daga wajen igiyar cikinta a buɗe yake.
A iya tsakiyan cinyoyinta rigar ya tsaya mata, ga shi a buɗe, har farin pant ɗinta na ciki yana iya hangowa. Da kyar ya danni zuciyansa ya ɗauke kallonsa daga kanta, muryansa tamkar wanda yake a cikin maye ya ce. "Cheery kina buƙatar shopping, waɗan nan riguna din sun maki gajarta, kin cika tsawo dayawa, kina saurin girma sosai".
Tana ɗan murmushi na ganin ta rikita shi ta amsa da. "Daddy ni su nike so, sun fi daɗin sakawa, so ba sai an mun shopping ba". A shagwaɓe sosai ta faɗa, in baku manta ba ai ta cewa Rimsha zata yi maganin daddy very soon, shi ne ta fara tin yanzu, tana goge mashi hadda.
Baya son sake juyowa ya kalleta, sai ya ɗaga mata hannu kawai yai mata alamar taje. Tsabar rashin ji irin na yarinyar nan a maimakon ta je ɗin, sai ta nufosa, tana turo baki game da shagwaɓa ta ce. "Daddy nice baka son gani?".
Yana ƙoƙarin ce mata a'a sai ji ya yi ta haye gadon, ta dawo ta in da face ɗinsa yake facing tana saka mashi kukan shagwaɓa. Ai kawai zuba mata idanu ya yi, ya gagara motsa ko da ɗan yatsansa ne. Ita kuwa kuka take sosai na shagwaɓa game da rike hannunsa da yatsunsa suke ɗan rawa saboda yanayin da jikinsa yake.
Ai bai san time ɗin da cikin zafa ya fisgota ta faɗo jikinsa gabaɗaya ba, da yake bai saba ba, bai taɓa jin irin wannan yanayi ba, sai gabaɗaya jikinsa ya hau kerma, musamman yatsun kafafunsa dana hannayensa. Juyawa da ita ya yi, ya mata runfa da lion chest ɗinsa, hannunsa na rawa ya kai saman wuyar rigar jikinta, ya yi ƙasa da wuyar yana ƙoƙarin taɓa mata tula-tulanta.
Ƴar ƙaniya gabaɗaya ta rikice, wani irin tsoro ne ya dira mata a rai, take jikinta ya fara kerma, turesa ta fara ƙoƙarin yi tana ambatar sunansa game da bashi hakuri, hakan ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa. A zabure ya dakatar da kai hannunsa kirjinta, a zabure ya miƙe daga kanta, ya saketa da sauri. Cikin zafa ya diro kasan bed ɗin.
Door ya nufa, ko sau ɗaya bai waiwayota ba har ya fice cikin zafin jini. Yana fita ya nufi benensu yana furta auzubillahi minasshaiɗanin rajin, yana koran shaiɗanin da ya kusa galaba a kansa, ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi da hannu ɗaya, har wani irin jiri yake gani.
Ita kuwa yana fita ta diro ƙasa, jikinta na kerma ta afka toilet da gudu, ƴar ƙaniya ta tsorata.
Zaune ya isko Vir and guru a saman sofas dake balcony suna hira, Lion yana wanka. Jikinsa sam babu kwari ya wuce ya kwanta saman sofa, ya tada kai da cinyar guru yana mayar da numfashi a hankali-hankali.
Duka Vir ya kai mashi a damtsen hannunsa yana faɗin. "Yana ganka a wannan yanayi?"........ Shiru bai amsa masu ba, ya lumshe idanu kawai. Gashin kansa guru ya fara shafawa yana faɗin. "Kai Vir ka kyale champion, yanzu ya wuci yadda kake tinani".
Vir zai yi magana Lion da ya fito wajen yanzu ne ya ce. "Aryan come". Ya faɗa tare da juyawa yana hararar Vir ya koma ciki. Da kyar Aryan ya iya miƙewa ya rufa mashi baya, Vir ya dawo da kallonsa a kan guru kafin ya ce. "Kamar wani abin na damun ɗan uwanmu"......... "Ba komai". Guru ya bashi amsa, watau idan kuna neman mutum mai mugun zurfin ciki na wuce misali to ku samu guru, kunga dai ba laifi bane ya nunawa Vir cewa Aryan ya faɗa soyayya ne tin da basa ɓoyewa juna komai, amma ba zai iya faɗa ba tin da Aryan ɗin bai faɗa masu ba.
Shi in kun fahimcesa ko a tsakaninsu ne ba zaku taɓa jin maganar waninsu yana faɗawa wani ba, zai nuna kamar bai san komai ba, idan Aryan ya faɗa masu to fine, in bai faɗa masu ba shi dai ba za'a ji daga bakinsa ba.
Sosai Vir ya damu yana ganin kamar Arya bashi da lafiya ne. Amma guru ya hakikance lafiyansa lou. Dole Vir ya rufe zancen suka ɗauko wani chapter.
A can kuwa Lion ne zaune a gefen bed suna fuskantar juna da Aryan, cikin tsantsar natsuwa Lion ya ce. "Na nemi zaɓin ALLAH kan komawa gidan daddy da bayyana manufarmu ga duniya, na samu natsuwa a kan hakan, sai dai ina jin zuciyata babu daɗi sosai". Ya yi shiru yana yin ƙasa da idanunsa.
Babu mai fahimtar Lion biyun yadda Aryan yake fahimtarsa a duniya. Shiyasa magana irin wannan yake fara yi da Aryan ɗin kafin su Vir, kuma a irin wannan gaɓa ya fi son jin ra'ayinsu one by one ba tare da sun ji ra'ayin da ɗan uwansu yake badawa ba, shiyasa sai ya yi zama da su one by one.
Nisawa Aryan ya ɗan yi, tuni ya wastsake daga komar da ya shiga na love, ya dawo daidai ɗan duniya, ai Lion ba'a kawo mashi wargi da shirme............... "Tin da har kayi addu'a, kuma ka samu natsuwar zuciya kan can ɗin, to ina ga is better ne can ɗin shiyasa".
Kai ya ɗan jinjina alamar haka ne, shiru ya biyo baya for like 2 mins, Aryan ne ya katse masu shirun da cewa. "Our Lion ina neman wata alfamar"....... Zazzaro jade eyes ɗinsa Lion ya yi,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 82 Chapter of 95