mutane da ƴan uwansu, a lokacin da Lion bashi da lafiya hauka ne kawai guru da Champion basu yi ba, basa iya juran ko ciwo ɗayansu ya ji, kuma abokai ne fa kawai, sai dai abotarsu ta zarce kawai! Sun zama tamkar jinin jikin juna.
(Su waye suka ga trailer ɗin labarin nan da na saki kafin fara posting ɗinsa? Kun tuna na ce maku abokai da ba'a taɓa ganin irin abotarsu ba?)
Champion bai lura da Lion na kallonsa ba, ya wuce ya shirya cikin irin kayan jikinsu, sannan ya dawo in da suke. Yana isowa wajen ya ɗauki remote ya kashe Tv dake magana. A tare guru da Lion suka miƙe. Ƙasa suka sauƙo, jerawa suka yi izuwa parlo dan yin dinner. Tamkar ba kisa suka yi ba fa, suka ci abincinsu a natse, babu mai magana a cikinsu kamar kurame. Bayan sun kammala suka miƙe sai ɗakin da zakinsu yake a kwance.
Sai da suka duba lafiyansa sannan suka wuce zuwa room nasu, suka yi amfani da light control suka kashe wutar gidan, sannan suka kwanta. Asuba ta gari.
------------------------🔥
STAR LADY
Kwance take a saman bed a room ɗinsu, yanzu ba jimawa suka dawo daga class, da yake suna exams ne sai suke tashi da wuri. Ta afka duniyar tinani da damuwar sun kusa yin hutu, shikenan zata rabu da Rimsha, za kuma ta koma wannan kuntataccen gida da Champion yake kaita ita kaɗai tana rayuwa kamar mayya, ta tsani a yi hutu wlh.
Shafa fuskanta Rimsha da ta shigo yanzu ta yi, a ɗan firgice ta miƙe zaune, ganin Rimsha yasa ta saki ƙayataccen murmushin da ya kara fito da tsantsar kyanta, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Sis ina kika je?"........ Rimsha dake zama a gefenta ne ta amsa da. "Tinanin me kike yi ke kuma?"....... "Tinanin ankusa hutu zamu rabu".
Ajiyar zuciya Rimsha ta sauƙe, idan akwai wacce bata so a yi hutu to tana ganin a biyo bayanta, ta tsani komawa gidansu wajen waɗan nan mugayen Uncles ɗin nata. Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Rimsha ta katse masu shirun da cewa. "Ina zanenki yake?".
Take murmushi ya ƙara bayyana a kan fuskan Seraph, har ƴan kyawawan hakwaranta suka bayyana a waje, farare kal dasu, tamkar bata taɓa cin wani abin ba, kamar audiga. Jawo school back ɗinta dake wajen drawer ta yi, nan ta fito da cardboard paper and pencil ɗinta. Ware shi ta yi, take wani kyakkyawan zane ya bayyana, zazzaro idanu a kan zanen Rimsha ta yi, cikin zolaya ta ce. "Da ace dik abin da muka zana shi zamu rayu da shi mana, da kin more over sis".
Ɗan dariya mara sauti Seraph ta yi kafin ta ce. "Da kuwa ni kam na more ba, ke me kika zana ne ma?"......... Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "Ni waye na sani idan ba uncles ɗina ba, Uncle Faryan na zana"....... "Ban ga amfani sakamu zane ba". Star lady ta faɗa tare da fara nannaɗe nata zanen.
"Sister lady faɗa mun gaskiyar yadda aka yi kika yi wannan zane? Ban yarda dake ba, kina ga matashin da kika zana tamkar ba mutum ba!". A cewar Rimsha da ta dakatar da ita daga ƙoƙarin naɗe paper ɗin..... Ɗago ido ta yi suka kalli juna, sai ta kuma ta sauke da cewa. "Kawai zanen ne ya zo mun kaina na zana".
"Wlh ban yarda ba, ko dai saurayinki ne?"...... "Saurayi kuma?". Ta faɗa da alamar mamaki. "E mana, idan ba saurayinki ba kin manta ranar da uncle James ya ce mu yi zane a class wannan matashin kika zana, yanzu ma madam Rohisha ta sanyamu zane kin sake zana shi, dik yadda aka yi kuna da alaƙa".
Ɗan taɓe baki star lady ta yi kafin ta ce. "Ni ban san shi ba, kawai zanensa nike yi"........ Karɓar zanen Rimsha ta yi, ta zuba mashi ido na ƴan sakanni kafin ta ce. "Dik yadda aka yi yarinyar nan kin saba zana wannan zane sosai, ki duba wannan bashi da banbanci da na uncle James da ya bamu muka zana ranar"........ "Rimsha, ni fa ban iya wani zane bane sai wannan shiyasa kowani work na zane da za'a bamu shi zan zana in dai na mutane ne".
"Kenan yanzu tsakanina dake akwai ɓoye-ɓoye?". Rimsha ta tambaya cike da rashin jin daɗi abin da star lady take yi mata, tana da zurfin ciki da ɓoye abubuwa sosai, har yau taki ɗaukarta a matsayin ɗaya suke. Ganin ta ɓata rai yasa star lady ta ce. "Sorry sis, for give me, zan faɗa maki waye shi to".
Rimsha yarinya mai sanyin hali, take ta sauko ta ɗan yi murmushi game da cewa to ina jinki. Gyara zama lady ta yi tare da cewa. "Wannan shi ne kaɗai Uncle ɗin da nike da shi a duniya, brother ɗin mammyna ne, ban ma san in da yake ba, kawai na taso ne da kaunarsa a zuciyata, tin ban iya magana ba nike kallon hotunansa a ɗakin mammyna, da na fara wayau ta ce mun shi ne kaɗai kanin da take da shi, kila watarana zan haɗu da shi, lallai in san cewa shi garkuwa ne a gareta da bi bakiɗaya, ya taimaka mata a lokacin da duniya dikka suka juya mata ba, shi ya zama silar zamanta komai da ta zama a yau, shiyasa kika ga na iya zanensa sosai, hotunansa a gidanmu sun 100, mammy tana son shi sosai, amma fa ba ainahin kaninta na uwa ɗaya uba ɗaya ba, kanin daddyna ne, zamansu ya yi kyau ne yasa ta ɗaukesa tamkar kani, ko an tambayeta kaninta take cewa ba kanin daddyna ba, shiyasa nike son shi matuƙa, ba zanensa ba kome zan iya yi a kansa". Da iya gaskiyarta ta yi maganar.
Siririn murmushi Rimsha ta saki tare da cewa. "Ko dai ko dai"...... "Ko dai me?". Ta faɗa tana harararta. "Ko dai son shi ya kamaki?". ........ "Brother ɗin daddyna ne fa, the same Father the same mother, aikin ga babu soyayya a tsakaninmu, da aka ce akwai damar yin soyayya to idan na girma zan yi aure shi kawai zan aura".
Yara da su sai manyance da iyayi ga shegen wayon tsiya.
Note sunan Seraph ni na yanke sunan, ainahin sunan Seraphina ne, saboda saukin kira yasa nike sauƙaƙa maku ta hanyar yanke sunan.
Murmushi Rimsha ta saki tare da kara ware zanen da kyau tana kallon kyakkyawan fuskansa, uhm batun haɗuwansa ba'a magana. Cikin zolaya Rimsha ta ce. "Har na ji zuciyata ta buga a kansa, ya haɗu sosai, shiyasa dik in kika yi zanensa sai kin cinye marking kin barmu a baya, dole in koyi zana shi ni ma ko dan samun marking, kuma ba karya ya haɗu, zan rinƙa zanensa in manna a bangon ɗakina a gida".
Harararta Seraph ta yi tare da kwace zanenta, a natse ta ce. "Uncle ɗina bai yi arha har haka ba, mutum ne mai tsada da darajar da ta fi lu'ulu'u, ba zan bari ki koyi zana mun shi ba, dan nasan har cikin toilet sai kin yi zanensa, yanzu fa shi ne uban da kawai nike da shi a duniya, ina fatan in haɗu da shi a nan kurkusa"...... Tana rufe baki sai ga Aana ta shigo room ɗin, gadonta ta nufa tana faɗin. "Seraphina daddy ɗinki ya zo, wai ki je".
Wani irin faɗuwar gaba ta ji, jikinta take ya yi sanyi saboda har yau tsoronsu take ji, dik da wancan zuwansa ya tausasa mata, ya kalleta da kulawa har da runguma, amma murɗaɗɗun mutane irin wannan ba'a gane in da suka dosa. Naɗe zanenta ta yi tare da maida shi cikin jaka, tana hararar Rimsha ta ce. "Mu je ki rakani".
Zazzaro ido Rimsha ta yi kafin ta ce. "Uncle ɗinki na jikin hoton nan ne?"... Kai ta girgiza alamar a'a tare da cewa. "Wannan wani ne, zan baki labari, mu je"......... Sauƙowa ƙasan bed ɗin ta yi, ta wuce gaba Rimsha ta rufa mata baya, kai tsaye suka nufi parking lot, dan yau ko office na director bai je ba, yana cikin mota a zaune.
Excuse ta yi mashi tare da buɗe front side, ta shiga tana ƙoƙarin matsawa Rimsha ta shiga ya rufe kofar da kansa. Lokaci guda ta ji babu daɗi, dan ita tasa Rimsha ta rakota, wannan kamar cin fuska ne ai, sam bata ji daɗi ba. Baya Rimsha ta koma ita ma, cikin rashin jin daɗi ta juya ta koma hostel ɗinsu, da kallo Seraph ta bita har ta kurewa ganinta, da yake akwaita da saurin kuka sai idanunta suka cika tab da kwallah, take violet ɗin suka ciza sosai.
Ƙasa-ƙasa ta ce. "Good afternoon daddy". Ta faɗa a daidai lokacin da hawayen da ya cika mata ido ya hau zuba. Sai da ya ɗauki good 2 mins kafin ya amsa da. "How's your day?". Ya faɗa tare da juyo da kallonsa gabaɗaya a kanta. Shiru ta gagara amsawa.
Intently ya miƙa hannunsa ya ɗago haɓarta, ya yi mamakin ganin tana kuka, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya kasa, dan ba zai iya shareta ba a yanzu da ya gane wacece ita, sake haɓarta ya yi ya kama hannayenta dikka biyu da hannunsa ɗaya, jawota jikinsa gabaɗaya ya yi, ya ɗagata cak ya ɗaura a saman laps ɗinsa tare da ciro hankey daga aljihunsa. Hawayen ya fara goge mata a natse kafin ya ce.
"Why are you crying Seraphina?"...... Kai ta shiga girgiza mashi alamar babu wani dalili. Hannu yasa ya kwantar da kanta a saman faffaɗar kirjin nan nasa, ya ɗan yi shiru tamkar mai tinanin wani abu, ita ma shiru ta yi tana shaƙar daddaɗar kamshinsa. Almost 5 mins suna a haka kafin ya ce. "Ya school?"........ "Lafiya". Ta amsa.
"Akwai abin da kike so ne?". Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Please daddy idan an yi hutu kada ka kaini wancan gidan da kake kaini ni kaɗai ɗin, babu daɗin zama"........ "Nima yanzu bana son in kaiki in da zaki yi nisa dani, zaki zauna a gida tare dani"....... Dik da tana balain tsoron gidansu, amma sau dubu gara shi a kan gidan da yake kaita ta zauna ita kaɗai, ko ba komai a gidansu zata ji motsin mutane. Dan haka sosai ta ji daɗi tare da ɗan rungumesa kafin ta ce. "Thank you daddy". Yarinta fa kenan, har ta mance da ta taɓa jin tsanansa a ranta, kuma fa lokaci guda ita ma ta jisa a ranta, dik yadda aka yi suna da alaƙa ta jini mai karfi, irin wannan abu jini ne ke fusgarsu.
Sun jima suna tattaunawa, dik da bashi da yawan magana, amma ya daure ɗaya biyu suka ɗan yi hira, sannan ya ɗauko cartoon-cartoon na su chocolate, biscuits, har da su sweet sosai ya bata. A ɗan shagwaɓe ta ce. "Daddy Madam ta hana mu cin kayan zaƙi fa, wai cikinmu zai yi ciwo"........ Ɗan zuba mata ido ya yi, lokaci guda kwakwalwarsa ta fara tariyo mashi lokacin da take jaririya cikin towel a kwance, a ransa ya ce. "Ba zan taɓa manta lokacin da aka haifa mana ke ba, da hannunsa Lion ya ɗaukeki ya yi maki huɗuba da sunan da Seraphina ba, bayan tafiyansa Mammynki ta dage sai Seraphina take son a kiraki".
Katse mashi tinanin ta yi da cewa. "Daddy zaka koma da su sweet ɗin ko?"........ Kai ya ɗan girgiza tare da cewa. "Ki je da su, babu wani ciwon da cikinki zai yi, ai baki girma ba"...... Shiru ta yi, a ranta ta ce to zancen waye zata ɗauka? Na Madam ko na daddyn nata?
Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce. "Ki ce wa Madam daddynki ne ya ce ki zo da sweets ɗin"........ Da okey ta amsa tare da kwasan kayan ta fito. Bayanta ya bi da kallo har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya tada mota ya wuce, ita kuma tana shiga room ɗinsu kai tsaye wajen Rimsha ta nufa. A gefen bed ɗinta ta zauna tare da cewa. "Sorry sis".
Miƙewa zaune Rimsha ta yi tana faɗin. "Nevermind my lovely star lady, daddyn nan naki akwai zafin rai da faɗa, amma ba komai"....... One side smiling ta ɗan saki kafin ta ce. "Wannen kikeso a cikinsu, zaɓa zan baiwa su Aana saura".
"Ke fa to?". Rimsha ta tambaya. "Waɗan da ya kawo mun last two weeks ma kinga basu kare ba, kawai wannan zan baku ne"........ Hannu Rimsha ta sanya ta ɗauki guda biyu ta bar saura kwali huɗu, dama shidda ne..... "Daddyn nan naki yana sonki sosai". Cewar Rimsha. Uhm kawai ta ce tare da kwasan saura ta baiwa su Aana, daga nan ta koma gefen bed ɗinta ta zauna tare da fito da littafanta zata fara karatu.
----------------------------🔥
To ku zo mu bi kowani jami'i daga cikin matasan jami'an mu zuwa gidansu mu ga ya suka isa ne? Ya rayuwarsu a gida bayan horo kafin su koma barrack. Daɗin abin ma dai dukkansu a Crystal Palace suke except Zaynish, dan haka haɗa kayanmu zamu yi, zaman Crystal Palace yakamamu, dole in kama mana gida ɗaya haya dani daku masu karatu, kumu je mu bararraje a can, hawa gomar dik zan kama mana, kowacce ta zo mu haɗu ai an zama dangi, to na yi gaba sai kun zo.
CRYSTAL PALACE.
MUHAMMAD KHAIZA'AN'S HOUSE. Idan baku fahimta ba gidansu Vash kenan. Gida ne mai ɗauke da family guda bakwai, Muhammad Khaiza'an da matarsa, ƴaƴansa maza guda uku, Faryan, Dr Aryan da ya je ɗaukar Vash a barrack, sai Harleen, sai Vash da Rimsha. Vash mahaifinsa shi ne babban yayansu Dr Aryan, ya rasu ne, mai bi mashi shi ne mahaifin Rimsha wanda momyn Rimsha ta yi breaking heart ɗinsa ya rasu.
Nasan yanzu kun gane karatun, da Vash da Rimsha ƴaƴan wa da ƙani ne, mugun Uncle ɗinta da kuke ji tana ambatar nan ba kowa bane face Aryan, ya tsaneta saboda ya fi kowa shaƙuwa da daddynta kafin mom ɗinta ta shiga rayuwansu ta rabasu da shi na har abada. A dalilin rasa mahaifin Rimsha yasa Muhammad Khaiza'an ya karfafa dokar haramta soyayya a zuri'arsa, dama can ya haramta auren soyayya, a dokarsa sai dai shi ya zaɓa maka mata, a cewarsa auren soyayya dik yaudara ce, dik yadda aka yi a lokacin samartakansa an taɓa yaudaransa.
Haka yaransa suka tashi basama soyayya, mahaifin Vash da Mahaifiyarsa ba auren soyayya suka yi ba, Abba Muhammad Khaiza'an ne ya haɗa auren, kuma suka zauna lafiya har ALLAH ya basu Vash, sun koma ga ALLAH sanadin haɗarin jirgin sama da ya yi sanadin rayuka da dama. Shi mahaifin Rimsha bijirewa mahaifinsa ya yi, suka kullah soyayya da mahaifiyarta tin a school, ya kafe lallai shi ita zai aura, ba yadda Abbansa bai yi ba, ya ce wlh idan ba ita ba kashe kansa zai yi, cikin fushi Abba ya amsa da ya je ya aureta amma shi babu ruwansa, kuma ba shi zai nema mashi aure ba.
Sai da su Arya suka dinga rokansa, sannan ya hakura ya nema mashi aurenta, daga karshe dai ta ci amanarsa, ta haifi Rimsha tana jaririya ta ajiye mashi ita ta tafi bayan ta kwashe mashi makudan kuɗaɗe, ko shayar da yarinyar bata yi ba, Abba ya yi takaicin hakan, ya dinga faɗa, a lokacin kuma daddyn Rimsha ya yake jiki ya faɗi yana faɗin shi a kira mashi matarsa, har lokacin bai daina kukan sonta ba, daga nan Abba ya ce ko bayan ransa bai yafe ƴaƴansa su yi auren soyayya ba, wai sai auren haɗi, ya zaɓa maka da kansa, ya aura maka a kawo maka ita ɗaki kawai!
A taƙaice dai soyayya haramunce ga ahalin Muhammad Khaiza'an...... Kun san me mutane na? Wani diraman da za'a buga a cikin wannan ahali ba? Uhm sai shiru kawai, ku dai mu je ciki, ahalin haramta soyayya kenan, ko ya za'a kaya? Ga su dai da zaratan maza, su Vash da auren haɗi, jama'a you will love this part and laugh over.
Zaune Faryan and Harleen suke a parlo, kowannensu danna wayansa yake yi, matasa ne da basu rufe 30 years ba, yayansu Aryan shi ne mai 32 years. Sun yi nisa cikin abin da suke yi sai ga Rimsha ta sauƙo daga upstair, sanye take da silky pj's a jikinta, a lokacin da su Vash suka dawo daga horo Rimsha tana gida kenan, sun dawo hutu suma, kada ku manta a ɓangaren rayuwarsu a makaranta da rayuwarsu Lion na koma baya ne dan in faɗa maku yadda suka rayu, dan haka iya rayuwarsu ta makaranta ce muke baya, bana son ku rikice shiyasa na sake yi maku bayani!.
Ganin su Harleen a parlo yasa ta sha jinin jikinta, ta fasa zama tare da juyawa zata koma sama. A natse Faryan ya ce. "Rimsha lafiya zaki koma?"...... Idanunta a kan Harleen, muryanta na rawa ta ce. "Babu komai uncle"........ "Zo nan". Ya faɗa yana mata alama da hannu. In baku manta ba dama na faɗa maku uncle ɗinta Faryan ne kawai yake sonta.
Jikinta na ɗan kerma ta karisa sauƙowa ta nufosu...... "Don't come here!". Muryan Harleen a kaifafe ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta kalli Faryan da ya kirata, narai-narai da ido ta yi tamkar zata yi kuka. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Zo abinki, rabu da uncle Harleen ɗin nan da mugun halinsa".
Gagara motsawa ta yi, dan tana tsoronsa sosai, a gidan daga Aryan a waɗan da take tsananin tsoro sai Harleen. A daidai lokacin wani dattijo ya sauƙo ƙasan, irin dattawa masu kwarin nan ne, da karfinsa, yana rike da wata sanda mai kama dana mulki yana ɗan dogarawa, kafarsa ɗaya a ɗan karkace ne, karaya har biyu ya taɓa samu a ƙafa shiyasa yake ɗan ɗingisa kafar yake kuma yawo da sanda.
Hannunsa rike da wani littafi mai suna The Franklin scandal yana karantawa. Hannun Rimsha ya kama tare da nufar su Harleen, kun san da cewa shi ma a farko ya ki Rimsha? Ya ce sai dai a kaita gidan marayu, dan wlh Abba yana da mugun zafin zuciya, sai da Ammie ta dinga lallaɓasa, kun san uwa, ba zata so jinin ɗanta ya walaƙanta ba, ta dinga bashi hakuri tana tuna mashi faɗar ALLAH da yake cewa laifin wani baya shafar wani, sannan ne ya aminta ya yafe ya kuma rike Rimsha, da gidan marayu zai kaita.
A saman sofa kusa da Harleen ya zauna yana faɗin. "Harleen wai ba zaka daina takurawa jikata a gidan nan ba ko?"......... Shiru Harleen bai yi magana ba, sai ma yunkurawa da ya yi zai miƙe ya bar wajen kenan suka ji alamar motsin buɗe kofa. Dikkansu kai kallonsu wajen suka yi.
A natse Aryan ya shigo cikin parlon bakinsa a ɗauke da sallama, daga ɓangarensa ya fito, fuskan nan tasa tamkar hadari, a ɗaure tamau. Ai Rimsha na ganinsa ta watsa da gudu ta yi sama, dan ta san shi ko Abba baya iya dakatar da shi a kan tsanar ganinta da ya yi, a kan ya ja mata bala'i ya karyata gara mata ta gudu ai. Tana haurawa sama suka ci karo da Vash da ya tashi barci a yanzu, jiya basu taso da wuri ba sai mangrib suka baro AZURE, cikin dare suka iso, shi ne yake ta barcin gajiya, tin da ya yi sallar asuba ya mai da barci sai yanzu ya farka.
Tsawa ya daka mata game da cewa. "Baki da hankali ne kike yi wa mutane gudu a cikin gida haka?". Kara shiga tashin hankali ta yi, sai kawai ta fashe da kuma mai tsuma zuciya. Abinku da soja, to shi da zuciyarsa kamar dutse ina zata tsumu? Wani tsawan ya sake daka mata kan ta wuce ta bashi waje ko ya yi ball da ita. Ai tin bai gama rufe baki ba ta wuce da gudun gaske ta nufi room ɗinta.
Siririn tsaki ya ja tare da wucewa ya sauƙo ƙasa cikin zafin nama....... Jama'a a irin wannan gida ta ya za'ayi Rimsha ba zata fi son zaman school ba?.
Saman gadonta ta faɗa tare da fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya, tana jin tsanar kanta na ratsata, sai ta ji yau dai ta tsani mom ɗinta da ta ja mata wannan tsana, ita me laifinta. Cikin kuka ta ce. "Ni me laifina? Me na yi maku? Ni ɗaya nike da mom ne?".
Daga bakin kofa Faryan ya amsa da. "Baki da laifin komai Rimsha, kuma ba ɗaya kuke da ita ba, kawai zafin zuciya ce da riko irin nasu Yah Aryan, amma ki kara hakuri everything is nearing its end". Ya faɗa tare da shigowa ciki. A gefen bed ɗin ya zauna, da sauri ta tashi ta faɗo jikinsa tana rirriƙesa tare da fashewa da sabon kuka, cikin kuka take faɗin. "Uncle kai da Abba and Ammie ne kawai masu tausayi a gidan nan, su uncle Aryan har Yah Vash basu da tausayi, kowa baya sona, shi ma Yah Vash ba kamar da ba, a baya idan ina kuka yana rarrashina, amma yanzu sai faɗa da tsawa, haka da asuba da na bugesa ban sani ba kamar zai dokeni.......". Kukan da ya ci karfinta ne yasa ta dakata da yin maganar.
Cikin tausasawa ya ce. "Vash yanzu ya zama soja, dik wani sanyin halinsa ya tafi, sai kin yi hakuri da shi kin ji? Su Yah Aryan kuma watarana zasu gane baki da laifi su daina kyararki".
Cigaba da kukanta ta yi bata sake yin magana ba, dan jin zuciyarta take yi tamkar zai fashe ne.
A can parlo kuwa, Abba ne ya ce. "Aryan zo nan". Ba musu ya je ya zauna kusa da Abba, shi kansa Abban shakkar yi mashi magana a kan Rimsha yake yi, saboda ya san zuciyar Aryan shi ya gado, ga balain kafiya kamar kafurin farko, tin da ya furta ya tsani Rimsha fa dole su yi hakuri kawai su kyalesa, in ya juya baya juyuwa ne.
"Ina son ka kaini asibiti anjuma a duba mun karafunan dake kafata ɗin nan, dan na fara jin canji". Abba ya faɗa ba wai dan hakan ya so faɗa ba, so yake yi ya taushesa ya ce ya rage tsanar Rimsha, amma kwarjinin ɗan nasa yasa ya canza maganar.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
https://www.facebook.com/share/g/1EUXbqsDjP
STEP 1________🔥
2025-11-17.🔥
FIVE LIONS, FIVE MISSIONS, ACTION, DEATH OR LIFE, ADVENTURE, BRAIN GAMES, REDRESS, A BREATHTAKING LOVE THAT STEALS THE HEART AWAY.♥️🔥
NOTE. FIVE LIONS babu complete ɗinsa, yanzu nike posting ɗinsa, yanzu aka fara!
E_____________14
"Ina son ka kaini asibiti anjuma a duba mun karafunan dake kafata ɗin nan, dan na fara jin canji". Abba ya faɗa ba wai dan hakan ya so faɗa ba, so yake yi ya taushesa ya ce ya rage tsanar Rimsha, amma kwarjinin ɗan nasa yasa ya canza maganar.......... "Okey Abba".... A gaggauce cikin girmamawa su Harleen suka ɗaga mashi gaisuwa, mugun tsoronsa kowa yake ji, basa wasa da abin da ya shafesa, dan yana nan kullum fuska a haɗe kamar hadari, ɗan banzan kuma ga shegen kyau mai tsananin shiga rai, in ka gansa sai ka sake kallo, musamman idan ya motsa ɗan bakin nan zai yi magana wasu dimple a both sides na soft kumatunsa suka lotsa, sai ka kallesu ka sake kallo, ka ji tamkar kada ya daina magana, ga bala'in daɗin murya sai rashin mutunci cike da cikinsa, maganar ma sai ya yi ra'ayi yake yi ƙasa-ƙasa dan bala'i, idan ka ji ruwanka, in ma baka ji ba kai ka sani, shi dai baya maimaita magana, kuma dole ayi abin da ya umarta ko an ji ko ba aji ba.
Da fine ya amsawa su Harleen ciki-ciki. Ya faɗa tare da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 95