Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zazzaɓi sai ya dakatar da ita, ya wuce ya fita ba tare da ya ji me take son ce mashi ba. Su Angelina suna tare da Arya a cikin ɗaki suna hira, shiryawa Arya ta yi cikin normal kayan gida kamar yadda Leo yai mata message, wandon jeans baki da top ash, ta ɗauki karamin pistol da ake basu dan kare kai, sannan ta ɗauki laptop ɗinta cikin rucksack ɗinta, bata yi wa su Angelina magana ba ta wuce ta fita. Da sauri Jehan ta taso tana nuna mata alamar zata bita. Riko hannunta ta yi, ta miƙawa Angelina ita tare da cewa. "Zan je wajen sir Nirash ne, akwai aikin da zamu yi, ki kula da ita". Ta kai karshe game da rage tsawonta ta sumbaci goshin Jehan, sannan ta saketa ta juya. Da sauri ta nufi tantin Leo, tsaye ta iskosa ya kammala shirinsa cikin combat trouser ɗinsa da normal tshirt, yana kokarin sanya wuƙaƙensu na sojoji a mazaunansu a jiƙinsa. Kamewa ta yi game da sara mashi kafin ta ce gata nan. Bai yi magana ba ya wuce gaba, bayansa ta bi, suka fita ta baya babu wanda ya sani, ko su Noor basu sani ba. Tafiya mai mugun nisa suka yi har zuwa in da gwamnati ta gina ginin office ɗin sojojin ruwa dake ɗan nesa da bakin ruwan. Dik juriya irin ta Arya sai da ta gaji a wannan tafiya, shi dai ya wuce gaba, ko sau ɗaya bai waigota ba, ga rucksack na laptop ɗinta da ta goyo a baya ko shi bai karɓa mata ba. Haka ta jure wahalar har suka isa, dik jikinta ya yi tsami. Tsarin ginin offine ɗin nan ya tsaru kam, ga tsawo sosai. A jikin katangar ta baya suka tsaya, Leo ya juyo da kallonsa a kanta, tana tsaye tana ɗan haki. Can ƙasan maƙoshi ya ce. "Zaki iya haurawa?". Kallon tsawon katangar ta yi, ya yi tsayi sosai, amma da yake basu san kalmar no ba sai ta ce. "Yes sir". Hannu ya miƙa kan ta bashi rucksack ɗinta. Ba musu ta cire ta miƙa mashi, karɓa ya yi ya goya a bayansa game da tura wayansa cikin anjihunsa, ya haɗe hannayensa dikka biyu ya ware mata tafukansa. Baya-baya ta koma, sai ta zo da gudun gaske ta taka kan hannun nasa da ya haɗa mata, ta daka tsalle shi kuma ya ƙara ɗagata da hannun nasa, ta kama saman katangar ta haura, a hankali ta fara nishin gajiya. Sauke rucksack ɗinta dake bayansa ya yi, ya jefa mata sama ta capke. Gefe ya ɗan koma, ya yi baya da gudu ya zo ya taka jikin katangar ya yi tsalle ya capki saman. Ya haura ya sameta. A tare suka dira cikin wajen. Tamkar ɓarayi haka suka fara lallaɓawa a wajen har suka samu wani ɗan lungun da kafa basa iya bi saboda ciyayi. A nan suka tsaya, ya juyo da kallonsa a kanta, a dake ya ce. "Kunna laptop ɗinki, dik wani na'urar dake amfani da network a nan nike son ki datsan mun, da son samu ne ki datsan mun babban na'urar da suke amfani da ita dan aiki, dik wani bayanansu ki sauke shi a laptop ɗinki". Kai ta jinjina mashi game da tsugunnawa a wajen, ta fito da laptop ɗinta ta ɗaura a saman laps ɗinta. A gaggauce ta kunna, kai tsaye ta nemi yin connecting na network ɗinta da nasu. Ta kuwa yi sa'a da yake tana kusa da su sosai, a take ta haɗe nata da nasun. A gaggauce ta fara ƙoƙarin yi masu kutse, a yadda take pressing laptop ɗin sai kun sara mata, cikin kwarewa da zafin nama. Kewaye Leo ya ɗan fara yi a wajen, ya je ya dawo, ya je ya dawo, yana duba masu babu mai zuwa ne. Tin around 12 suka isa wajen tana wannan aiki har 2:30, ta yi mugun gajiya, bayanansu na da mugun yawa, da kyar ta iya haɗosu ta fara ƙoƙarin saukewa a kan nata na'urar, kafafunta da take tsugunne sun gaji sosai, hannayenta dik sun gaji, yadda ta sunkuyar da wuya yasa wuyanta ya rike kam yana mata zafi. Dawowa kusa da ita Leo ya yi, can ƙasa ya ce. "Mintuna nawa ya rage komai ya sauƙa?"....... Tamkar zata yi kuka, da kyar ta ce. "A ƙallah 40 mins". Yadda ta yi magana da kyar yasa ya sauke kallonsa a kanta sosai, sai yaga tana ta ɗan jujjuya wuyanta alamar gajiya, wuyar ta rike mata sosai tana son ta ɗan sake, ga shi wajen da suke ɗin akwai ciyayi ne sosai ba halin zama, ta gaji matuƙa. Ganin hakan yasa ya dawo dab ita, durkutsawa ya yi ta bayanta, ya gyara hands glove ɗin hannunsa game da riko shoulder ɗinta dikka biyu. Take ta ji komai ya tsaya mata cak, slowly ta ɗan juyo ta kalli hannunsa dake kafaɗar tata. Nisawa ya yi tare da fara mammatsa mata wuyanta a hankali-hankali, daga kafaɗarta zuwa bayan wuya, ya sake komawa wajen damtsen hannunta, so yake yi ta yi sauri su bar wajen, dan sun shiga hurumin da na nasu ba, binciken bayan fage yake yi a sirrance, idan aka kama shi ya shiga wannan hurumi ba karamin balai zai shiga ba, dan ya keta in da ba nasa ba, shiyasa yake son ta yi sauri su bar wajen, ga shi ta gaji aikin ya daina gudu, bata iya pressing laptop ɗin sosai bare ta iya kwasan bayanai dayawa a lokacin guda, kaɗan kaɗan take copy ta yi paste, shiyasa ta fara mata tausa dan ta samu kwarin jikinta. Aikuwa tamkar ya sanya mata battery ne, yana fara yi mata tausan ta fara jin gaɓoɓin wajen wuyanta sun fara sake mata, take ta fara pressing laptop ɗin da sauri, ganin haka yasa shi ma ya kara yi mata tausan da kyau, musamman wajen bayan wuyanta, da ya zo wajen ya sanya hannayensa dikka biyu ya kama wajen, ya sanya ɗayan hannu ya riko wuyanta ta gaba, ɗayan kuma ya fara......... *Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.* Likes comments and share fisabilillah. QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A LADY TEEMA. STEP 1🔥 2026-01-01🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 75 & 76 *FOLLW MY TIKTOK ACCOUNT 👇* https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP *FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL ACCOUNT* 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S *It is about combining sperm and eggs to create children, and how the sperm of one man can be used to produce many children. The idea is presented in a different style. On the other side, there are soldiers fighting on the line between life and death, soldiers whose mission is to cleanse the world of corrupt and evil people. However, the path they have chosen to achieve this victory is filled with thorns: wicked people, traitors, oppressors, cruel individuals, and pure betrayal with no mixture of good at all.* Ya fara daddanna mata tsakiyar bayan wuyan nata. Sosai ta fara aiki da sauri. Aikin da ta ce zata yi in less than 40 mins sai ga shi ta yi sa in less than that 20 mins ta kammala. A gurguje ta rufe laptop ɗin, Leo ya miƙe game da bata hannunsa kan ta kama, da kyar ta iya kamawa ta miƙewa saboda gajiyar tsugunno, ganin haka sai ya karɓi rucksack ɗin nata, ya goya a bayansa sai ya ce ta yi tsalle kamar ɗazun ya ce ta kama katanga. Ai ina, ba zata iya ba, kafafunta basu miƙe sosai ba, dole suka ɗan tsaya a wajen na ɗan lokaci kafin ta samu kwarin iya tsalle ta haura katangar, barci ya cika idanunta, jikinta dik ya yi sanyi, haka ta dira ta baya ta tsuggunna har ya diro. Gaba ya wuce ta miƙe ta rufa mashi baya, haka suka miƙi wannan doguwar hanya dan komawa. A can cikin sansani kuwa. Zazzaɓi yana neman hallaka V babu wanda zata faɗawa, dan Noor yana bakin wuta, while ya fasa mata waya ba halin ta kirasa, ba zata iya taka kafafunta ta je ta same shi ba, sai ta kudundune cikin blanket ɗinsa tana kuka, ko abincin da ya kawo mata bata iya saukowa ta ci ba. Around 11 na dare Zaynish yasa aka kira mashi Angelina cikin tantinsa, ta je da laptop da sauran kayan aikinta. Yana zaune a saman mattress ɗinsa ta shigo, ba tare da ya kalli in da take ba ya nuna mata wajen zama, tana sanye da sleeping silky pjs a jikinta, a gefensa ta zauna tana ɗan satar kallonsa, musamman ligh brown African hair ɗinsa dake kara ɗaukar hankalinta. Ajiye wayar dake hannunsa ya yi game da mayar da hankalinsa a kan laptop ɗinta, a tare suka yi iya kokarinsu wajen ganin sun shigar da karamun drone na surrinsu mai kama da fly wajen hayakin nan amma abin ya faskara, dole ya juya akalar drone ɗin, ya duba cajin jiki, yana da cajin da zai iya kwana ɗaya a sama, hakan yasa ya ratsa da shi ta gefe-gefen wajen. Daga gefe ta gaba wannan tangamemen tekun ne, shiru Zaynish ya yi, a cikin ransa ya ce idan kuwa haka ne wannan in da hayakin yake fitowa a saman ruwa ne, gini aka yi a saman ruwa ta baki-bakin, ruwan na ratsawa ta ƙasan ginin yana wucewa. Na'am ya yi da hakan, sai ya cigaba da bin bakin ruwan dan ya ga me zai iya giftawa dik da ba wani haske sosai sai hasken farin wata dake tankar kamar rana. Angelina ta zauna shiru sai kallonsa take yi, ko ɗazun ta yi waya da Aunty Ummie again, dik shi bai sani ba. Ya jima a wajen tsaye bai ga motsin komai ba face jiragen ruwa manya-manyan dake can tsakiyar tekun. A cikin ransa ya ce dik yadda aka yi akwai jiragen ruwa dake ratsa wannan waje, to me suke kawowa ko me suke zuwa ɗauka a wajen? Gaskiya suna son sani, suna jiran umarnin gaggawa daga sama. A can kuma sauran sojojin suna shan ɗumi, Manassa da Vash suna hira a wajen, dan su basu fara aikinsu bama tukun nan. Ya ce sai gobe. A daidai wannan lokaci karfe 12 na dare AZURE ta yi kiran meeting na gaggawa kan lamarin MISSION NA DOL. BGA ya tura takarda office na GAT, ai GAT yana ganin takardan ya yi kiran meeting na gaggawa, a lokacin har ya tashi a aiki da yamma, amma da yaga BGA ya turo takarda kan DOL sai ya fasa tashi, ya bada lokacin around 12 na dare zasu yi zaman, ya gagara hakura sai gobe, dama tin tini yake jiran wani motsi daga wajensu. (Ni kam na ce ai ko dan su Angelina team DOL zaku rinƙa samu umarni da wuri daga GAT!) A wannan meeting room da suke zama dik end of the week su yi meeting kan tsaro aka shirya zaman. An tsara komai, kafin 12 ta cika dik wasu jiga-jigan generals sojoji sun hallara a wajen. Kamar kullum, GAT ne ya fara miƙewa, ya kunna mic na gabansa, a dake ya yi wa kowa barka da zuwa, kafin ya baiwa BGA damar gabatar da abin da ya tarasu. Dik kowa ya natsu tsit, BGA ya miƙe cikin mutunta kai, ya zaro farar takarda daga file na gabansa kan table, sai da ya fara yi wa kowa barka da zuwa kafin ya sanar dasu abin da Leo ya sanar da shi a waya. Bayan ya kammala bayani ne ya koma ya zauna sai MGR ya miƙe tsaye, cike da girmamawa ya ce. "A ina wannan waje yake? A ina su Nirash suke dama?". Cike da ɗan mamaki Captain ya kalli MGR, cikin ransa ya ce. "Ko ina ruwansa da in da suke tin da ba a karkashin office ɗinsa suka tafi Mission ba?". A fili kuma binsu da ido kawai ya yi yana mamakin halin wasu jami'an ba tare da ya yi magana ba. BGA ya rike mic ɗinsa game da cewa. "Bani da sanin takamamman in da suke, saboda bai faɗa mun ba, amma dai koma ina ne ina jin babban waje ne, kuma sun zaɓi waje mai kyau suka kafa sansaninsu". MGR ya ce. "Wai dama su nawa ne a sansanin nasu? Da wasu sojoji suka tafi?"........ General Ibrahim IB ne ya ce. "Ina ganin dik wannan ba shi ne ya tara mu a nan ba, umarni suke nema dan zuwa duba menene a wajen, so yakamata ne mu duba mu ga idan ya dace a basu izini sai a basu, a basu izinin su je su duba a sirrance, in sun ga me a wajen sai ayi zama kan abin da ya dace, either a basu umarni kan su tashi wajen in abin da bai dace ba ake yi a wajen, ko kuma a basu umarnin kama masu aiki a wajen, in kuma abin da ya dace ake yi a wajen ba shikenan ba". Ya yi maganar yana kallon MGR. Tin da ya fara magana manyan generals suke jinjina kai alamar tabbas zancen General Ibrahim haka ne. Bayan ya kai karshen maganar ya juyo da kallonsa a kan GAT da ya yi shiru yana sauraren shawarinsu. General Ibrahim IB a dake ya ce. "Sir, ni a tinanina yakamata a basu izinin zuwa su duba menene a wannan waje, saboda mu san matakin da yakamata mu ɗauka". MGR ne ya ce. "Amma kafin a basu izini yana da kyau mu fara sanin in da suke, saboda ko mun ji shiru a kai masu ɗauki"....... Uhm kai Captain ya jinjina, a cikin ransa ya ce. "Ko kuma a faɗa maka in da suke dan ka ji ko kana da alaƙa da wajen hayaƙin ba"........ Shi dai GAT bai ce komai ba, shiru yana cigaba da saurarensu dan ya ji shawaran kowa. General Ibrahim IB ya ce. "No need MGR, ba sai mun san takamaiman daidai in da suke ba, umarni kawai za'a basu su kaddamar da aiki, mun basu makamai wadatattu masu lafiya, mun basu dik abin da zasu buƙata! To me na neman sanin ina suka kafa sansani? Dan kai masu agaji? Agajin me bayan wanda suke tattare da shi?"........ MGR ya ce. "Kar ka manta rayuka ne suma, and bamu san wani irin hayaki ne a wajen ba, kada yazamana abin ya fi karfinsu yafi karfin makaman da suka tafi da shi azo a far masu, gara mu san in da suke ta yadda ko an fi karfinsu zamu tura masu wani agaji na gaggawa". Kai General IB ya girgiza. "MGR wai me naka na son sanin in da suke? A ƙarƙashin office ɗinka suka tafi Mission ne? Ko dai kana da wani plan a ƙasa ne?". Ib ya faɗa yana tsare MGR da ido.... Take MGR ya haɗa malaman jikinsa, ya ɗan yi shiru kafin ya ce. "No sir, ba wani plan, kawai na damu da rayukansu ne duba da yadda muke rasa sojojinmu a arewacin kasar nan, so ina tsoron rasasu ne". "Dik sojan da ya fito daga nan AZURE na sani kun sani ba dai wani ɗan ta'adda ya fi karfinsa ba, kun san irin horon da muke basu, manyan ƙasashen duniya nan suke kawo sojojinsu dan mu horasu saboda ingancin horarwarmu, to me naka na jin tsoron rasasu? Baka yarda da kanka bane?". General IB ya faɗa, babu wasa a tattare da shi. BGA ya ce. "Shi nima na gani, no need mu damu da abin da muka san mun fi karfinsa, koma menene sojojin AZURE suna iya tinkararsa ba tare da tsoro ko shakka ba, ko kai da kanka baka yarda da horon barrack ɗin namu bane?". MGR ya girgiza kai game da cewa. "Sorry sir, ni dama saboda damuwar rasasu ne, amma ba komai, nima ina bada goyon bayan a basu izini su je zubasu"..... Shiru ne ya ɗan biyo baya a room ɗin, kafin General IB babban General na AZURE, sojan da baya ɗaukar wasa kuma baya wasa, jami'in da gaskiya da aikinsa suka kawo shi kujeran da yake kamar dai Captain Onbish, jami'in da baya karɓar cin hanci, baya bin bayan rashin gaskiya, ko ɗan uwansa na jin yakama da laifi sai ya hukuntasa daidai da hukuncin da ake yi wa kowa!. A dake ya ce. "Sir ni a nawa shawarar a basu izinin a sirrance su je su gano menene a wajen, in suka bamu information na abin dake wajen sai mu san matakin dayakamata mu ɗauka". Ya faɗa yana kallon GAT dake ta binsu da ido. Jawo paper neman umarnin GAT ya yi. Ya buɗe ya ɗan duba rahoton da BGA ya rubuta kan DOL ɗin. Pen ya ɗauko, cike da kwarewa ya rattaɓa hannu kan ya bada izinin su je su duba. Daga nan ya miƙawa General IB paper. Karɓa IB ya yi, ya ɗauki pen ɗinsa shi ma ya rattaɓa sign ɗinsa. Daga nan ya miƙawa Lieutenant General shi ma ya sanya hannu, sai aka miƙawa Major General shi ma ya sanya hannu, sai Brigadier General watau BGA shi ma ya sanya hannu, sannan aka baiwa Colonel ya rattaɓa nasa hannun, sai Lieutenant Colonel, sai Major, daga nan aka baiwa Captain, yana sanya hannu aka baiwa First Lieutenant, bayan ya sanya hannu sai Second Lieutenant, yana sanya hannu suka maidawa BGA takardan. Karɓa ya yi, dikkansu suka haɗa maki wajen yi wa team DOL fatan alkhairi da fatan nasara, daga nan GAT ya ce a rufe masu taro da addu'a, kasancewar General IB musulmi ne sai ya riga kowa miƙewa ya fara kwararo masu addu'a har da na fatan ALLAH yasa GAT ya musulunta, dan mutumin kirki ne sosai, ga kaunar kasa da ƴan kasa, yasan aikinsa matuƙa. Daga nan aka tashi wannan zama around 1:30 na dare, GAT ne ya fara fita kafin su General suka rufa mashi baya. Yana komawa gida ya isko Aunty Lisa tsaye a parlo sanye da sleeping dress tana ta faman jiransa, ta ɗan kiba sosai, da alamar tana da ciki. Yana shigowa ta tafi ta rungumesa tana mashi welcome, shafa kanta ya yi game da cewa. "Ya shirye-shirye?"...... "Welcome my oga sir". Ta faɗa kafin ta bashi amsar tambayarsa na ya shirye-shirye da cewa. "Komai yana tafiya daidai a nawa ɓangaren kai fa?". Rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa cak yana amsa mata da. "Komai daidai, amma party biyu kawai za'ayi sai soldiers day shi ma ɗaya". Ya faɗa a lokacin da suke shigewa room ɗinsu. Watau jama'a shirye-shirye bikin GAT da Aunty Lisa ake yi, ana shirin party, yanzu ya fitarwa da duniya cewa zai yi aure, shi ne ake shirye-shirye, ga alamar kuma Aunty Lisa na da ciki, har ma ya ɗan fara girma. Akwai shagali, su Arya sai dai su dawo su samu Aunty ɗinsu da baby, dan cikin Aunty Lisa zai iya kai 3 month ma. Gaskiya daddy GAT yana sha'aninsa, ya tura yara mission shi kuma yana buga nasa mission ɗin a gida, bari dai in yi shiru kada ace na ce, to ban ce ba!. D------O-----L. Tin Arya tana iya jurewa ta taka da kafafunta har ta gagara, abin yai mata yawa, ga barci ga gajiya. Wani irin jirin gajiya da ya ɗebeta bata san lokacin da ta tafi gabaɗaya ta faɗi ƙasa ba. Intently Leo dake gabanta ya juyo, ganin ta faɗi ƙasa yasa ya juya ya kalli hanya, sun kusa isa sansaninsu, duba time ya yi a wayansa 3:30 ya yi....... Matsawa dab ita ya yi, a cikin ransa yana faɗin dole ya bata ainahin horo ba horon kare kai ba, in dai zai yi aiki da ita dole ta iya jurar dik wani wahala, dole ta zama kaman shi, dan haka daga gobe dole ya fara horar da ita. Cike da wannan tinani a ransa ya rage tsawonsa, ya gyara hannun rigansa kafin ya ɗauketa cak sai saman shoulder ɗinsa, ya juya suka cigaba da tafiya. Hannayenta tasa ta saƙalo wuyansa, bata san time da ta kwanta shiru a jikinsa ba, har barci ya fara ɗaukarta, bama ta san lokacin da suka isa sansani ba, sai ji ta yi ya kwantar da ita saman mattress ɗinsa kasancewat ta baya ya shigo dan kada kowa ya gansu, and ya yi tinanin ta yi barci shiyasa ya kwantar da ita wajen, bai tasheta bane kuma dan kada ya yi magana a waje sojojinsu su fahimci baya nan ya fita, dan wannan aiki na bincikar hukumar navy aikinsa ne shi kaɗai da yake yi wanda baya son kowa ya sani, shiyasa ya wuce cikin tantinsa da ita. Da ya kwantar da ita sai ya suke rucksack ɗinta dake bayansa, ya tsaya kusa da mattress ɗin, murya can ƙasa ya fara kiranta da ke ta tashi ta tafi cikin tantinsu........ Da kyar ta yunkura ta miƙe zaune, ganin ta farka yasa ya koma gefe ya zauna a ƙasa game da fito da laptop ɗin nata, aiki zai dasa yi, babu alamar barci a tattare da shi. Miƙewa ta yi, jikinta dik a mace ta nufi hanyar fita, har ta kai kofa muryansa ya katseta da cewa. "Zoki cire password na laptop ɗin"....... Nan fa ta ji kirjinta ya buga, dan kuwa ɗazun ta canza password na laptop ɗin daga sunanta ta mayar sunansa, tana zaune kawai bata san ya aka yi a lokacin ta tsinci kanta da sanya sunansa a password ɗinta ba. Ƴan kame-kame ta fara yi, ta ɗan sosa kanta kafin ta juyo ta dawo, wannan shi ake cewa ɓoyyar soyayya, ɓoyayyar zuciya, hidden love ba. A gefensa ta tsugunna, zuciyarta cike da tinanin yadda zata sanya wannan password ɗin a gabansa. Cikin ikon ALLAH sai ya juyo mata da laptop ɗin saitinta yadda ba zai ga me take yi ba, ai a bayyane ta sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya har tasa ya ɗan ɗago yai mata kallon second ɗaya ya ɗauke idanunsa. Cikin girmamawa a hanzarce ta shigar da password ɗin game da juyo mashi da laptop ɗin. Bai ko ɗago ya kalli in da take ba ya fara ƙoƙarin buɗe bayanan da suka sanƙamo. Cike da shakkarsa game da tsoro da girmamawa ta ce. "Sir, zan iya taimaka maka?". Barci take ji kamar zata mutu, amma kunji wai zata tayasa aiki, kai soyayya wahala ce wani lokaci. Shi kuma da ba'a mashi abin arziki da wani kansa tin na haihuwa irin na Lion ya ɗaga mata hannu, ko kallon in da take bai yi ba mata alama da hannu a kan ta fice mashi daga ɗaki...... Jikinta ya yi mugun sanyi na abin da ya yi mata, ta yi tinanin yanzu tin da suna aiki tare zai ɗan rage share mutane da jiji da kai, Arya bata san cewa shi ɗin jinin sarauta bane, a jininsa jiji da kai da izza take. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi waje, tana fitowa suka ci karo da Zaynish dake ƙoƙarin shigowa. Baya ta ja game da kamewa ta sara mashi. Ko kallon in da take bai yi ba ya wuce ciki. A cikin ranta ta ce ita tsakanin Zaynish da Leo ɗin ma bata san wanene

Chapter 90 of 95