Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
drone ɗinsu, su yi control ɗinsa ya je har in da miyagun suke, suna zaune a cikin tantin da suka kafa a sansani suna kallon dik wani motsin ƴan ta'adda a laptop ɗinsu suna kwasan bayanansu suna sanarwa sojojinsu. Kai an fa shirya masu kaya dayawa, sannan aka shirya masu ɗanyen abinci, su zasu girka kayansu da kansu, su Arya aka shirya masu laptops ɗinsu a cikin rucksack, sannan aka basu bututun iska saboda faɗawa kogi ko wani rami na ruwa. Tambayana a nan shi ne, shin masu karatu sojijin ƙasarku haka ake basu kwararrun kayan aiki a lokacin da za'a turasu faɗa da wasu ƴan ta'adda? Ko iya bindiga kawai ake basu?. Dikkansu suna sanye da uniform a jikinsu, har da su Arya yau an basu uniform, sun kuwa yi balain kyau, tamkar dan su aka yi kayan, sun kara kwarjini da firgita makiya. Dikka sojojin ƴan uwansu suna wajen dan yin bankwana dasu, ta yiwu su dawo a raye ko kuma akasin haka, kowa zai ga ɗan uwansa na karshe ne a yanzu. Ummie bata zo ba, dan Zaysh ya ɓoye mata, ya ce mata dai zasu shiga wani aiki, zata iya kiran wayansa ta ji a kashe idan babu rana basu yi caji ba, amma dik in ya kunna waya zai kirata. A haka ya kyaleta, dan baya son ɗaga mata hankali. Babban soldiers eagle aka kawo dan ɗaukarsu ya yi dropping ɗinsu a bakin dajin da zasu shiga mission na farko, idan ya saukesu a wajen sai su kutsa cikin daji da ƙafarsu. Suna ta ɗagawa ƴan uwansu hannu suka fara shiga jirgin a jere cikin tsari haɗe da ɗan pareti, da haka suka shige cikin jirgin suna kallon ƴan uwansu, Leo yana ta kallon Champion and Lion da guru dake tsaye a babban filin tashin jirgin AZURE, dikkansu suna sanye da nose mask, ga katuwar jacket da suka sanya, p-cap a ciki kafin su sanya hukar jacket ɗin, sun yi kyau kam matuƙa. Sai da jirgin su Leo ya ɗaga sannan IRON FIST suka bar barrack ɗin, suka koma hotel da suka sauƙa, ba yau zasu koma ba, dan akwai binciken da suka zo yi dan tabbatar da wata gaskiya da basu faɗi ba, so zasu ɗan yi kwana biyu a nan. Daddy Noor ma sai da ya ga tashin jirginsu sannan ya koma gidan GAT ya hau shirin komawa US. Su V da suka zo tafiya sai da zuciyarsu ta ɗan kaɗa, dan basu taɓa tafiya aiki ba kun sani, dole su ɗan tsorata, amma Arya yarinyar nan tamkar babu zuciya a kirjinta sai dutse, ko kaɗan bata tsorata ba, sai ma cewa da ta yi su yi sauri su tafi, dan ita ma ta shiryawa mutuwa, bata da tsoro ko kaɗan yarinyar, ita dai V ta ji kwarin gwiwa ne kawai a waje ɗaya shi ne Noor yana tare da ita, tasan dik wuya zai tsaya mata. Manassa and Angelina kam ba'a magana, ita Manassa komai normal ne, baka gane tana farinciki ko bata yi, kamar Vash take, komai daidai ne, ko su mutu ko su rayu dik daidai ne, ita kuwa Angelina har da guntun hawayenta, wai na kewar daddynta ne hawayen, kuma karya ne, zuciyarta ne ya fara karaya, ta ji tsoron su mutu, dama a cikinsu dik ita ce mai tsoro gaskiya fiye da Manassa, tana da saurin karaya, karfin hali ai sai Arya, balai, yarinyar nan ko mutuwa ake yi ba zata fasa abin da ta sanya a gaba ba, ita ta gado daddynta sak, dan kafin ya taka matakin GAT ai sai da taurin zuciya da jajircewa, to ita dai da kwarin gwiwarta suka nufi can. Jama'a an iso in da nike son mu iso, sojojinmu sun tafi Mission, yanzu zamu shiga ainahin labarin ZAKUNA BIYAR, yanzu zamu isa ga ainahin jigon labarin, masu hawan jini, masu low bp ayi hakuri da abin da alkalamina zai rubuta a wannan karon, na san fore sure zuƙata zasu kaɗa, hankula zasu tashi, amma amin afuwa, ilimi da farkar da al'umma nike burin yi! Sannan zan so wannan ɓangare dana kira da jigon labarin nan kada ku tsallake waje ko ɗaya, da daɗi da ba daɗi dik ku yi hakuri ku karanta, dan amfananku ne, ba karamin amfani zai yi maku ba!! Muje zuwa kan jigon labarinmu a yanzu!. -----------------W-S-Hospital🔥 Cikin wajen tamkar ba'a duniya take ba, ta ko'ina glasses ne da wutar lantarki, zaku rantse da ALLAH dik lantarki duniya a nan wajen ake karar da shi, ko da sunan wasa wuta bata motsawa a wannan waje bare a ɗauke, jikin bangon ainahin wajen kakkafar bango ce da zaku yi zaton samudawan da ne suka gina shi ba mutane ba, dan gini ne da aka yi su da duwatsu masu karfi sosai. Amma daga ciki ko'ina na glass ne, ga kayan zamani ta ko'ina. A dunkule kenan, mu kara kutsawa ciki dan ganin meke going. Ƙofofin wajen masu ƙarfi ne sosai haɗe da kimiyar tsaro na zamani mai ban mamaki, suna amfani da fasahar tsaro mai ƙarfi, tare da makullai na lantarki, akwai wani sashen ma da babu wanda yake iya shiga sai mutane uku, dan wajen door ɗin kuna taɓawa shocking ne a jikin, sai dai a ga mutum ya ƙandare in ya taɓa. A gefe guda ga wani side tamkar fagen kwaje-kwaje na hospital haka aka yisa, dan ga ɗakuna da beds dayawa a side ɗin, kowani ɗaki da dalilin hasasarsa a wajen. A wani side ɗin kuma ɗakuna ne masu kyau da gadaje masu rai da lafiya na majinyata, ta kowani kusurwa akwai CCTV, a saman bene kuma akwai wani ɗaki mai cike da computer dan kula da cameras dake ta ko'ina. Hospital ɗin yakasance da ɓangarori guda biyar, kai tsaye mu je ɗayan ɓangaren. Wajen cike yake da glass, dik ɗakunan wajen glass wall ne, filin cike yake da dabbobi kala-kala masu haɗarin gaske, dabobin da idanu bai taɓa ganin irinsu ba, kowacce dabba tana cikin glass tamkar a gidan zoo, ga manya-manyan macizai, kunama, kifaye, kai harta cinnaka akwai wajensu, suna cikin glass, side ɗinsu yana da mugun girma sosai, kuma dik cike yake da waɗan nan dabbobi. Ɓangarorin hospital ɗin nan kowanne da abin da ya kunsa, ba zan fayyace maku me a ciki gabaɗay ba, sai tafiya ta yi tafiya, dan haka mu je zuwa, kun dai ji ɓangare na farko na dabbobi ne kawai!. Akwai nurses dayawa a hospital ɗin, amma dikka mata ne babu namiji ko ɗaya, sai dai dik nurse da zaku gani a wajen sai kun kalleta kun sake kallo, babu munana a wannan waje, ga su da zubin ƴar tsana, sirara ga shape, farare tas-tas da su, rigarsu na aiki guntaye ne zuwa tsala-tsalan cinyoyinsu masu kama da madara saboda hasken jikinsu, suna da hakin gashin mai shegen kyau wanda suka ɗauresa a tsakiyar kai, kansu da hular aikinsu, ga su da tsabtar balai, komai nasu cikin tsantsar kula da natsuwa suke yi, one thing about them, dik wata malamar asibit dake wannan Hospital ɗin shekarunta ɗaya da sauran, dikkansu they're age mate, babu wacce ta girmi wata a cikinsu, kuma dikkansu yanzu 18 years suke da shi, sannan abin da zai baku mamaki dayawa daga cikinsu suna ɗan kamanceceniya da juna, wasu ma ida ka gansu zaka zaci twins ne, sannan sun kai su 40 a hospital ɗin. Abin da mamaki ko? Ace shekarunsu su 40 ko sama da haka dikka ɗaya, sannan dikkansu mata ne ba maza tamkar dama zaɓosu aka yi, kai ko zaɓosu aka yi sai haka!. To akwai dai manyan likitoci maza guda uku, sannan akwai masu gadi zaratan maza madaka karti dake sanye cikin uniform ɗinsu mai zubin overall, ga wasu dakakkun takalma a kafafunsu mai balain karfi Kai in takaice maku tsaron wajen nan wane mutum ya iya giftawa, ko tsuntsaye basa iya zuwa wannan waje, dan lantarkin dake wajen ba zai bari dik wata halitta mai rai ta gifta ta sama ko ta ƙasa ba. Akwai benaye guda biyar daga gefe masu hawa ɗai-ɗai, sannan akwai ƙananan gidaje wa ƙannanan ma'aikatan lafiya da guards masu tsaron wajen, kamar general government hospital ne fa, kun san shi ne ake yi wa ma'aikata gidan zamansu a cikin hospital ɗin. Mu ƙara kutsawa ciki. ---------------------------🔥 Wasu matasan likitoci dake sanya cikin kayan aikinsu ne suka fito daga cikin elvator da ta tsaya a sama a yanzu, maza ne su uku da a kallan shekarunsu zai iya zuwa ɗaya kamar yadda kansu watau tsawonsu yake ɗaya, komai na jikinsu iri ɗaya ne, harta hands gloves na hannayensu da nose masks na fuskokinsu iri ɗaya ne, ankel boot dake kafafunsu ɗaya, kansu na sanye da huluna masu zubin na sanyi, suna sanye da doctors nose mask ne, wanda ya hana ganin fuskokinsu sai idanu kawai. Komai na jikinsu farare ne tas, sun fito a cikakkun kwararrun likitocin nasu A TAƘAICE SU WAYE SU?!. DR JAMES. surgeon dr, suna yi mashi laƙabi da likita mai gani har hanji, saboda kwarewarsa a aiki, ga iya tiyata bisa tsari, sannan akwai tsantsar natsuwa da zallar rashin yin magana, dan ko kusa ko alama baya ɗaga ido ya kalli mutane bare magana, baya dariya, kai ko fuskansa ba'a samun gani bare dariyarsa, likita ne da ya shahara a kan aikinsa over, Sai DR KAMAL, bokan turai, assistant surgeon mai gani har hanji ne, kuma halinsu ma iri ɗaya. Sai kuma DR MARK, waɗan nan uku shaƙiƙan aminai ne na gaske, suna kuma kaunar junansu sosai. Kai tsaye a bakin wani kofa da aka rubuta P-P a jikin door ɗin suka tsaya. Na tsakiyansu watau mai DR JAMES ne ya ɗan gyara hand gloves na hannunsa kafin ya zareta, sannan ya ware yatsunsa ya sanya a jikin fingerprint dake jikin kofar. Take door ɗin ta yi scanning kafin ta buɗe kanta. Turawa ya yi, kusan a tare suka shige ciki. Ɗaki ne tamkar ɗakin tiyata, an shirya komai da ya danganci tiyata, ko'ina tsab a cikin ɗakin, ga wani sanyin Ac dake tashi, akwai doguwar sofa mai zaman mutum uku a cikin ɗakin, sannan akwai wasu manyan kwalabe da freezers bayan gadon tiyata, gefe guda akwai drawers. Kusan a tare suka zauna a saman wannan sofa ɗin tare da ɗaura kafafunsu ɗaya bisa ɗaya, dik cikinsu babu wanda ya yi magana da ɗan uwansa, sai DR JAMES ne ya mai da hand gloves ɗinsa tare da duba time a agogon dake manne a hannunsa. A daidai wannan lokacin wasu nurses mata guda biyu kyawawan gaske suka shigo cikin ɗaki, suna turo wani bed. Wata macece kwance a saman bed ɗin, tana sanye ciki kayan tiyata, an shiryata tsab, da alama an yi mata komai da ake buƙata, dan ga shi tana barci alamar anyi mata alluran barci. A daidai bed dake cikin ɗakin suka gungura gadon su tsaya, sannan suka kama matar suka mayar da ita saman gadan cikin ɗakin, a natse suka tura gadon da suka zo da shi suka fita waje. Kada ku manta dik nurse's dake cikin wannan hospital ɗin shekarunsu ɗaya watau 18 years, na kara tina maku ne dan yana da muhimmanci ku rike hakan kada ku manta. A tare waɗan nan likitocin suka miƙe tsaye, wajen drawers ɗin nan suka nufa. Kowa ya sanya kayan tiyata, gloves, mask, gown, suka cire wanda suka zo da shi kenan. DR JAMES ne ya umarci DR JAMES da ya je ya duba kayan aikin da nurses ɗin nan suka shirya komai yana na intact ko?. Karisawa gaban table dake kusa da gadon DR KAMAL ya yi, duba kayan ya hau yi, an shirya irinsu scalpel wukar tiyata, retractors na buɗe ciki, forceps & clamps, needle holder & surgical needle, electrocautery machine na goge jini, suction machine na fitar da jini ko ruwa, sutures zaren da ake ɗinki, sterile drapes na rufe jikin maras lafiya, catheter na fitar da fitsari. Hannu ya ɗaga tare da ɗaga yatsa ɗaya yana yi wa DR JAMES alamar da komai yana nan yadda yakamata. A tare suka kariso wajen domin fara aikinsu. DR JAMES ne ya fara checking na bp, pulse, oxygen, da heart rate na mara lafiyar, sai da ya tabbatar bata a cikin haɗari sannan ya sanya mata catheter dan fitar da fitsari. DR MARK ne ya matso ya fara tsabtace wajen ciki zuwa gwiwa da ƙafa na maras lafiyar, ya yi amfani da disinfectant watau chlorhexidine. DR JAMES ya rufe maras lafiya da sterile drapes, sannan ya duba lokaci a agogon hannunsa dan ya tantance matakin da Anesthesia da suka bata yake. A natse ya ɗago ya kalli DR MARK, da sauri ya ɗauki scapel ya miƙo mashi tare da ɗaukar cutton ya matsa kusa da shi. Ta sama suprapubic incision bikini cut ya fara yankawa a natse game da kula sosai. Ya buɗe tsoka da peritoneum har ya isa mahaifa. DR MARK ya ɗauko retractors ya miƙa mashi, da shi ya yi amfani wajen buɗe wajen sosai ta yadda zasu ga abin da suke yi da kyau. Da fallopian tubes suka yi amfani dan gani mahaifar, DR JAMES ne ya fara da yanke ligaments da jijiyoyin dake rike da mahaifar, cikin kula sosai suke yi ta yadda ba zasu samu matsala ko su rasa wata jijiya da zai yi sanadiyar kashe mahaifar ba. DR MARK ya gyara electrocautery dan hana zubar da jini sosai. Kun san me? Tin daga ovaries suka tsinke mahaifan nan, suka ciresa gabaɗaya, da alama wannan mata bata son ta sake haihuwa ne, domin kuwa idan ovaries suna nan za'a iya yi mata dashen wata mahaifa lokacin da ta buƙata, amma babu su yana da matuƙar wahala, a yanzu ma ba'a samu hanyar dashe ovarries ba. DR KAMAL ne ya ɗauko wani kwalba mai kama da cikin mace DR JAMES ya sanya wannan mahaifa a ciki, suka rufe kwalbar, DR KAMAL ya karɓi kwalbar ya fita da ita ta wata kofa dake cikin ɗakin wacce zata fidda shi ta part na kwajinsu. Kallon DR MARK DR JAMES ya yi. "Done my work!". Yana gama faɗar hakan ya bi bayan DR KAMAL ta kofar da ya fita. Binsu da kallo DR MARK ya yi, sai da suka fita sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da juyawa ya fara ƙoƙarin karisa nasa aiki. Rufe duct ɗin mahaifa and vaginal cuff ya fara yi da zaren ɗinki. Sai da ya ɗinke peritoneum, fascia, muscles, subcutaneous tissue, sannan fata a hankali cikin kula sosai, yana yi yana mai da idanunsa kan fuskar matar, ga idanun nasa dara-dara da su Masha ALLAH. Bayan ya kammala komai ya duba yanayin lafiyar maras lafiyar, ya duba yanayin jininta ko tana buƙatar ƙari ko kuwa aa, ya duba bp, hr, fitsari, da zafin jiki, ya duba komai a natse, ya yi sa'a komai lafiya, dama ya tsammaci hakan, saboda sun saba wannan aiki ba'a samun kuskure, so ba yau bane farau. Wata allura ya ɗauko, ya haɗa ya yi mata a damtsen hannu, sannan ya kira wasu nurses guda biyu suka shigo bayan ya tattara dik sauran kayan tiyatar ya mai da su muhallinsu, yazama tamkar ba'ayiwa matar komai ba. Umarni ya yi wa nurse's ɗin da su ɗauki matar izuwa recovery room na ɗan lokaci dan ta samu damar farfaɗowa daga anesthesia. Daga nan ya zaro wata farar takarda, rubutu ya fara yi cikin kwararre da kuma kyakkyawan handwritten ɗinsa mai bala'in kyau, abin da yake rubutawa a jikin takar shi ne, za'a bar mara lafiyar a asibiti ta yi kwana biyu zuwa biyar dan a kula da lafiyarta, sannan a bata nasogastric tube dan kada cire mahaifar ta hanata cin abinci, a kula da cimar da za'a rinƙa bata, a mayar da hankali a kan dik wani motsinta a cikin ƴan kwanakin nan dan tabbatarwa ta samu ingantaccen lafiya, kaɗa a barta ta yi aiki mai nauyi. Ya yi dogon note tare da naɗe takardan ya bi bayan nurses ɗin izuwa C-R ɗin. A jikin matar ya ajiye note ɗin tare da ɗauko wata takarda ya yi sign, sannan ya ɗauki wayansa ya matsa gefe kaɗan. Call ya yi kamar na minti ɗaya, ya katse kiran ya fita waje. Da fitarsa bai fi da mintuna 40 ba sai ga wasu nurses mata guda biyu sun shigo ɗakin, matar suka ɗauka suka fice, suna tura gadon nata har izuwa wajen wani daki da majinyata ke hutawa, suka sanyata a cikin, daga nan suka bar room ɗin, babu kowa a cikin ɗakin sai ita kaɗai, ko'ina tsab-tsab ga kamshi da sanyin AC dake tashi, . Shi kuma DR MARK bayansu DR JAMES ya bi. Cikin wani glass room ya shiga, komai na ɗakin glass ne except wall. Ɗakin gabaɗaya kewaye yake da kwalabe na glass masu kama da cikin mace, an shirya kwalaben a shirye datsan-datsan, kusan rabi da kwatan kwalaben ɗauke suke da mahaifar mace a ciki, tamkar yadda ake dashen mahaifa wa cikin mace haka aka yi dashen wa waɗan nan kwalabe dake ɗauke da ruwa tamkar yadda mahaifa yake a cikin mace, gabaɗaya kwalaben kuma suna haɗe ne da na'urar dake basu daidaiton yanayi ya hanyar amfani da wutar lantarki. TO FA, ABIN AL'AJABI! ME SUKE YI DA MAHAIFA KUMA?. Karisawa kusa da su DR MARK ya yi, a natse ya ce. "Done my work"....... Hannu DR JAMES ya jinjina mashi alamar ya yi kokari, sannan ya mai da hankali kan aikin da suke yi. Buɗe wata kwalba mai kama da cryo storage tubes ya yi tare da gyara hands gloves na hannunsa, ya ɗauki wannan mahaifa ta wannan mata, a natse cikin tsananin kula suke komai. Da kallo ɗaya zaka yi wa yadda suke aikin nan kasan cewa kwararrun likitoci ne na gasken-gaske, in short su likitoci ne da irinsu basu wuce a kirga ba ma a duniya, matakin kaifin ƙwaƙwalwa da bincikensu ya zarce yadda kuke tinani, they're gifted, amma dik da haka cikin taka tsantsan suke aiki yadda zaku san aikin mai haɗari da wahalar gaske ne suke yi, idan aka samu matsala kaɗan komai na iya lalacewa su tabka babban asarar da ba zasu taɓa son hakan ba!. A cikin wannan kwalba DR JAMES ya sanya wannan mahaifa, sai da ya tabbatar zamanta ta yi daidai sosai, sannan ya kunna wata naura dake jikin kwalbar dan canzawa mahaifar yanayi izuwa yanayin cikin mace, take cikin kwalbar ta kawo wuta sky blue mai ɗan haske, ta fara fitar da siririn sauti mai bada vuuuuu kamar vibrate na waya. Da sauri DR JAMES ya juya ya rungumi DR KAMAL alamar sun yi nasara, matsawa DR MARK ya yi shi ma suka rungumi juna sosai, sannan suka raba jikinsu. A natse suka fara takawa suna bin dik kwalaben dake cikin wajen suna dubasu, tamkar suna duba wani abin haka. Sai da suka tabbatar komai normal sannan suka nufi hanyar fita a tare. Kai tsaye side na dabbobin dake cikin wajen suka nufa, suna tafiya ne a kai ɗaya. Kewaye suka fara yi a wajen dabbobin, yana da girma sosai wajen, guards dake tsaron wajen kawai sun fi mutum 20, kun ga kuwa ai wajen da girma. Kowani dabba da irin abincin da yake ci, ga kwanon abincin kuma a gabansa an zuba mashi, waɗan nan guards ɗin suke baiwa dabbobin ruwa da abinci, har macizai dikka suke ciyar da su, shiyasa aka samu jiga-jigan guards madaka karti masu rai da lafiya dan kula da su. Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa suka gaida Dr's ɗin cikin girmamawa. Kai na gaji da rubutun, haba, ku ce Princess dakata ki bari haka, ya isa ki huta mana! Amma dik kun yi shiru sai typing nike yi kamar ba'a sona! To sai Monday idan mai dikka ya kaimu!. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥 ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. STEP 1🔥 2025-11-24.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________22 & 23 Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa game da sunkuyar da kai suka gaida Dr's ɗin cikin girmamawa. Hannu Dr Mark ya ɗaga masu alamar sun ji kafin su wuce ba tare da yi masu magana ba. Miƙewa nurses ɗin suka yi suna binsu da kallo har suka kurewa ganinsu, dawo da kallonsu a kan juna suka yi, ɗayar ta ce. "Sister Maya kin san wani abu ne?"........ Kai Maya ta girgiza alamar a'a bata sani ba. "Dr James ya haɗu over, kin san da cewa son gaske nike mashi?". Ta faɗa tana ɗan ciza laɓɓa......... "Sister Zinta i think ai kin same shi kin gama, ko bake kika ce mun ya yi inviting ɗinki zuwa waiting toom ɗinsa a yau da yamma ba?". "Haka ya ce in same shi a waiting room ɗinsa bayan tashi daga aiki, amma kuma ai ban san dalilinsa na kiran nawa ba! Maybe ma wani aikin zai sanyani, kin san shi baya rabuwa da sanya mutane aiki". Ta kai karshen maganar tana ɗan tura baki a cikin mask ɗin. "Amma ai idan aiki ne baya taɓa cewa a same shi a waiting room kai tsaye haka, sai dai office, ni a nawa ganin kamar ya kyasa dake ne, in kuwa haka ne ki shirya faɗa da sister Lazy, dan ba zata taɓa yarda wata ta raɓesa ba"........ Siririn tsaki sister Zinta ta ja tare da wucewa gaba tana faɗin. "Idan har na samu hankalinsa ya dawo kaina wacece kuma wata Lazy? Ba dik taƙamar da take mana da nuna ta fimu ɗin saboda shi yana kulata bane? Dame ta fimu? Kada ki manta ita ma fa ɗalibar lafiya ce kawai kamarnu". "Uhm ni dai ina ji maki tsoron balainta, dan mafaɗaciya ce"......... "Ita ɗin banza, dik taƙamarta dan tana aiki a karkashin office ɗinsa ne, shiyasa nima na zage ina son komawa karkashin office ɗin nasa". Maya zata yi magana daga bayansu suka ji an ce. "What are you doing here at this time da yakamata ace kuna bakin aiki?"........ Da sauri suka juya, wata malamar lafiya ce dai kamar su, tana sanye da kayan aikinta, kana ganinta kaga irin masifaffun nan masu zubin taliya ƴar murji, idanun nan a tsaitsaye, gashin idon kamar wacce aka shuka shinkafa a ƙasa, suna tsaye zara-zara ga tsawo. "Sorry sis Lazy". Suka faɗa a tare suna haɗa baki kafin su wuce su cigaba da tafiya zuwa in da zasu ce. Can ƙasa sister Maya ta ce. "Bana faɗa maki ki guji balain sister Lazy ba, kina ganinta tamkar wacce ake yi wa loading na masifa a kanta kowacce rana, kullum da sabon salon balain take zuwa". Cike da tsoro Maya ta karisa maganar. "Sai kuma ta yi, kawai yanzu inai mata biyayya ne saboda a karkashin office ɗin Dr James take aiki, amma ba wai dan ta fini da wani abu ba". Sister Zinta ta faɗa......... Suna tafiya suna hira har suka shiga wani sashe a cikin hospital ɗin. Wani glass room suka shiga mai ɗauke da tarin chemical dayawa, an shisshirya chemical ɗin a cikin transparent glass, kowani chemical da sunansa a manne a jikin kwalbansa.

Chapter 32 of 95