Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jama'a jinin IRON FIST yana magana, kaifin kwakwalwarsu gado ce, kun ji yana hasashen ba mugaye bane. Noor ya ce. "Ai manyan duniya zasu aikata fin haka ma, da zarar ra'ayinka ya sha banban da nasu to fa kai ne ɗan ta'adda kuma mugu, su kuma asalin ƴan ta'adda mugayen basa kiransu da hakan saboda ra'ayinsu iri ɗaya"...... Kai kawai Zaynish ya girgiza, daga nan bai sake yin magana ba, ya yi shiru, suka cigaba da hira suna tafiya, sai da suka kusa isa wajen tantunansu ne Noor ya ce. "Zaynish lafiya ka yi shiru?". Nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Babu komai bro". Noor bai yarda ba, ya matsa ya rike Zaynish tare da tsayar da shi suna fuskantar juna, suka dakata da tafiya, cike da kulawa ya ce. "Bro, now we're one family, bamu da iyaye da ƴan uwa a nan, bamu da kowa, why not ba zamu haɗa kanmu, mu rungumi juna ba?". Matsawa Vash ya yi, ya dafa kafaɗar Zaynish yana faɗin. "Ka faɗa mana damuwarka mu yi maganinta a tare"...... Baya Leo ya koma ya jingina da jikin wata bishiya yana kallonsu bai yi magana ba. Nisawa Zaynish ya yi kafin ya fara basu labarin yadda ƴan ta'adda suka kashe mashi dangi, iya shi da sister ɗinsa kawai suka rage, ya basu labarin komai bai rage ba. Sun yi matuƙar tausaya mashi, Noor ya rungumesa game da cewa. "As from today we're your family also, ba kai da Aunty Ummie bane kawai, akwai mu, we are brothers now! Zamu tsaya da kai dik wuya dik daɗi, promise that kaima kana tare damu"........ Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume Noor. "We're brothers now!". Matsawa Vash ma ya yi, suka rungumi juna. Shi dai Leo yana gefe yana kallonsu bai tanka ba....... Wani irin haushi karnukan hannunsu suka fara yi, hakan yasa Noor janye jikinsa a miliyan ya ja da baya, ya tsorata da kukan karen. Ɗago kai Leo ya yi yana faɗin. "Me yake damun karnikan?". Ya faɗa tare da kuna light ɗin hannunsa a kansu. Shiru Leo ya ɗan yi game da cewa su Noor su yi shiru, dan karnuka basa haushi banza, bare ma karnukan da aka baiwa horo irin wannan....... Tsit suka tsaya karnukan na cigaba da daka haushi. Lokacin guda cikin zafa Zaynish ya ture Leo tare da damke wukar da wani mutun ya zo ta baya zai daɓawa Leo ɗin. Take wuƙar ta fasa mashi tafin hannu dan bai sanya hand gloves ɗinsu na aiki ba, janye wuƙar baya mutumin ya yi, hakan yasa ta kara pasa tafin Zaynish. Kafin DOL su motsa sai ganin wasu jiga-jigan mutane huɗu suka yi sun bayyana kewaye da su, suna sanye da bakaken kaya na manyan ɓarayi, suna wani irin haki, da alama gudu sosai suka yi kafin su cim masu. Siririn tsaki Noor ya ja tare da cewa. "Ku zo da wuri mu baku a jikinku muna son komawa kafin gari ya waye"....... Zazzare wuƙaƙen hannunsu mutanen suka yi, miƙawa Vash igiyar karen hannunsa Zaynish ya yi, ya sanya hannu ya tsaga rigar jikinsa gida biyu, ya ɗaure hannunsa dake zubar da jini, har lokacin haske wata tamkar kamar rana yana haskasu. Komawa baya Vash ya yi ya jingina da jikin wani ƙaton dutse dake wajen, ya barwa mazajen AZURE filin su fafata shi kuma ya rike karnuka. Haɗe bayansu Zaynish, Noor and Leo suka yi suna kallon mutanen. Kansu mutane suka yi da wuƙaƙen, hakan yasa suka dare suka rabu. Wani irin faɗa suka fara gwabzawa na nuna banbanci kwarewa, sai dai sun yi mamaki ganin mutanen sun iya faɗa irin wanda ake koyawa sojoji. Mutane su huɗu, su kuma su uku haka suka fara gwabzawa. A tare mutane biyu suka yi kan Noor shi kaɗai, kaucewa wuƙar da suke ƙoƙarin caka mashi ya fara yi, while shi kuma Leo ya kwace wuƙar nasa mutumin ya jefar, sun fara faɗar hannu, wani punch Leo ya kai mashi a bayan kunne wanda yasa ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa. Ganin ya faɗi ne yasa ya daka tsalle, ya taka wani dutse dake kusa da Vash, ya ƙara tsalle game da juyawa ya daki ɗaya daga cikin masu kawowa Noor hari da wuƙa, a wuya ya dakesa da ƙafansa, sai ga mutumin ya faɗi ƙasa. Dafa shoulder ɗin Leo Noor ya yi, ya daka tsalle ya taƙa ɗayan mutumin a fuska da waɗan nan shaggun tauraran takalman nasu, baya-baya ya yi ya faɗi ƙasa. Dafe shoulder ɗin Noor Leo ma ya yi, ya daka tsalle tare da juyawa ya taka mutuminsa da ya taso yanzu yake ƙoƙarin nufosu, watau ya farfaɗo daga punch da ya sha...... Da karfi Leo ya riko waish ɗin Noor tare da ɗaga shi sama, Noor ɗin ya ware kafarsa ɗaya ya kaiwa mutumin da suke faɗa da Zaynish duka a gefen wuya, wannan duka ɗaya ba tashi Noor yai mashi, dan wannan shegen takalman nasu ya daki maƙogwaron mutumin wanda yasa ƙashin wajen ta ɓalle, kun san takalmansun nan ba karamar taurice da ita ba. Zaynish bai iya faɗa da mutumin sosai bane saboda yankar da suka mashi a hannu, so da hannu ɗaya yake faɗa shiyasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar ɗaga Noor ya daki mutumin. Yana sauke Noor ɗin ya yi tsale ya yi backtorn ya taka ɗayan mutumin da ya taso yanzu a kai sai da ya koma ya zube a ƙasa. Tsalle Noor ya yi ya taka tsakiyar bayan Leo dake duƙe, ya ware kafafunsa ya daki guy da ya sake miƙewa a ciki, hakan yasa guy ɗin ya sake komawa ƙasa, ya durƙusa kan gwiwinsa yana nishi sama-sama tamkar yana son sumewa ne. Dirowa ƙasa Noor ya yi, yana dirowa Leo ya miƙe tare da dafa shoulder ɗin Noor ɗin, ya daka tsalle tare da ware kafafunsa ya sake kaiwa guy ɗin dake durkushen wani mugun duka a gefen wuya da kafarsa, hakan yasa guy ɗin yanke jiki ya faɗi baya numfashi. Dirowa ƙasa Leo ya yi tare da fara karkaɗe hannunsa alamar sun gama da su dikka........ Vash ne ya cire bindigar dake wajensa yana faɗin. "Dik ku kashesu, ba za'a rasa mai sauran numfashi a cikinsu ba"........ Hannu Leo ya ɗaga masu game da cewa. "Ku kamasu mu koma da su sansani, ina zargin ta yadda aka yi suka iy faɗar sojoji, lallai ba ƴan ta'adda bane kawai!". Noor dake haki kaɗan-kaɗan ne ya ce. "Ina zargin navy ne!"...... A natse Zaynish ya amsa da. "Tabbas na zargi hakan nima"....... Vash ya ce. "Okey kenan Navy sun san da zaman filin da muka je yau kenan?". Leo dake ƙoƙarin zare belt na wandonsa ne ya amsa da. "Suna da sani mana, sun san komai, kawai sun mayar da kansu karnukan farautar manyan Avaris ne shiyasa basa ɗaukar mataki"..... Zaynish ya ce. "Okey, watau sun ga shigarmu wajen?"...... Kai Leo ya jinjina alamar yeah sun gani. Cike da takaici Zaysh ya ce. "Okey, Navy na gadin ɓarnar manya ƙasa ba wai su dakatar da ɓarnar ba, watau masu gadinsu suka mayar da jami'an?". Jinjina kai Leo ya yi alamar kwarai kuwa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina ake son ƴan Avaris su sanya ransu? A hukuma azzalumai, a shuwagabannin azzalumai, a makaranta azzalumai, a kasuwa azzalumai, a asibiti azzalumai, a koina azzalumai, ina suke son jama'a su sanya ransu? Wa suke son su kaiwa kukansu ya tsaya masu?".. A taƙaice Leo ya ce. "ALLAH, shi kaɗai zasu kaiwa kukansu kawai, amma basu da wata mafita, a ko'ina akwai gurɓatattu"....... Vash ya ce. "Basa tsoron mutuwa"........ Zaynish ya ja dogon tsaki game da cewa. "Sun manta akwai mutuwar ne ai, sun manta akwai ranar da zasu tsaya gaban ALLAH su zayyana dik abin da suka aikata". Noor dake ƙoƙarin haɗe guys ɗin can ya ɗauresu da belt ɗinsa da ya kwance ne ya ce. "Ni fa ina son addinin nan naku, saboda naga akwai adalci sosai a cikinsa, kome zaku faɗa bisa adalci kuke faɗa". Ai da sauri Leo ya ce. "Are you sure kana son shiga?"....... Kai ya gyaɗa a lokacin da yake ɗago guys ɗin ya saɓa a saman shoulder ɗinsa. "Ina son shiga, bro kyawawan halayenku sun ratsa zuciyata, ibadarku, komai naku akwai kyau, ina son shiga"........ Da sauri Zaynish ya ce. "A'a to sauƙe waɗan nan mutane ka karɓi shahada yanzu". Jinjina kai Leo ya yi tare da sauƙe mutumin da ya ɗauka a ƙasa, ya zo ya rungumi Noor yana faɗin. "Ba zamu iya jiran sai mun isa sansani ba, yanzu kawai ka furta shahada".. Ba karamin daɗi Noor ya ji ba ganin suna ta murna dan zai shiga addininsu, aikuwa hakan ya ƙara mashi kwarin gwiwa, sai ya sauƙe mutanen, Leo da Zaynish har suna haɗa baki wajen karanto mashi shahada, ya maimaita, ya ALLAH, su kaɗai suka san irin daɗin dake ransu, rurrungumesa suka yi, Vash mai karnuka ma zuwa ya yi zai rungumesa Noor ya ja da baya yana faɗin. "Bro, ba da dogs ɗin nan ba, ka bari sai mun koma sansani ka". Murmushi Vash ya saki yana ja da baya. ALLAHU AKBAR, yau Noor ɗinmu ya zama musulmi, ya rabb, yau ranar murnace a garemu mu team NOOR. Haka suka kwashi mutanen, a lokacin 5 na asuba ta yi, gari ya fara haske, kai tsaye suka ƙarisa wajen sansaninsu, cikin dabara suka shiga sansanin, in baku manta ba ai fitar sirri suka yi, kai tsaye tantinsa Leo ya ce su kai mutanen, already biyu daga cikinsu sun mutu, ɗaurin goro yai masu ya barsu a ciki. Ya fito da sauri ya nufi wajen tekun nan dan ya yi wanka su yi shirin sallar asuba, lokaci ya yi, while a daidai lokacin ita ma Arya ta fito dan ta je ta yi wanka, ita tana son yin wanka a lokacin da jama'a suke barci, dan yana son shiga gefen tekun nan wajen ƙorama ta yi wankarta, bata son shiga toilet ɗinsu na nan sansani. Zuciyarta cike da tinanin su Leo basu dawo ba, dan ita tasan basa nan, ta damu sosai, kai tsaye cikin tabkin wajen ƙoramar ta nufa, hannunta rike da soap ɗinta and gel, ta ratayo towel ɗinta a wuya, while tana sanye da pjs a jikinsa, su V dik suna barci, saura sojojin wasu suna wajen wutar da suka hura, wasu kuma suna cikin tantunansu. Da yake wajen akwai duhu saboda duwatsun ƙoramun, sannan gari bai waye sosai ba, dan 5:20 ne a yanzu, so hakan yasa bata ga Leo ya cikin ruwan ba. A saman wata karamar dutse ta tsaya, ya cire pjs ɗin jikinta kaf, ta ware dogon silky ash hair ɗinta da ya kai mata har ƙugu, ya rage daga ita sai wani ƙaramin vest zuwa cibiya wanda bashi da hannu, daga ƙasa pant fari tas mai kyau. Zama ta ya bakin dutsen tare da sanya dogon kafarta dake ɗaure da diamond chain mai kyau a cikin ruwan, ita tana saka chain da waist beat dan kwalliya, amma su V basa sakawa. Ajiye kayanta da towel ɗin a saman dutsen ta yi, ta ajiye su gel ɗinta ma. Ɗan rintse idanu ta yi tana faɗin shiiii alamar ruwan da sanyi, sai kuma ta ɗan ja tsaki game da cewa. "Ko ina su sir Nirash suke? Sun samu nasarar abin da suka je nema? Ina masu fatan cin nasara". Ta sake jan tsaki tare da datse idanunta, da sauri ta faɗa cikin ruwa tana faɗin shiii sanyi. Dik abin da take yi a kan idanun Leo, amma ita bata farga yana cikin ruwan ba, da yake yana can tsakiya. Linƙaya ta fara yi yana juyi a ciki tana jin daɗin ruwan............ Nima na juya alƙalamina dan ba'a kansu kawai zan ƙare page ɗin ba, zamu dawo anjuma mu ga ya zasu kaya a cikin ruwan nan, ga Noor ya musulunta, Zaynish da yankar wuƙa a hannu, ga haɗaɗɗun karnuka guda biyu da muka samu, ga waɗan nan miyagun da muka kama, kai ga-ga ɗin ma yawa me da shi fa. Bari dai mu je mu dawo. --------------------------🔥 CRYSTAL PALACE. "Daddy please talk to me, baka da lafiya ne?". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Hannunsa yasa ya laluɓo nata hannun, ya ƙanƙame cikin nasa, can ƙasan maƙoshi ya ce. "Stop crying kada abin ya mun yawa kin ji my Cherry?". Ajiyar zuciya ta sauƙe, da kyar ta iya cewa. "Daddy na bari, amma ka faɗa mun me yake damunka ne, baka da lafiya ne?"....... Ɗan matse hannunta a cikin nasa ya yi, yana ɗan lumshe idanu ya ce. "Ban taɓa maraicin uwa ba sai yau, ban taɓa jin zafin rasa Ummiena ba sai yau, my Cherry please ina son farinciki na musamman ta ɓangarenki kin ji?". Ya faɗa tare da juyo da jikinsa ya kwanta a miƙe. Hannunta ɗaya ta ɗaura a kan lion chest ɗinsa. "My gentle chaos, zan yi dik iyawata wajen ganin na wanzar da farinciki a tattare da kai, yanzu dai faɗa mun baka da lafiya ne?". Ta kai karahe tana ɗan sunkuyo da kanta a kansa kaɗan, ta ɗan ɗaura goshinta a kan nasa......... Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Lafiyata lou, kawai ina cikin damuwa ne, na tina Ummieta". "Daddy na yi alƙawarin sanyaka farinciki tamkar yadda Ummie take sanyaka"......... Ɗan miƙewa ya yi, ya koma yai kwamciyar ruf da ciki, ya ɗago kansa suna kallon juna, zallar madarar kaunarta ne kwance a cikin kwayar idanunsa, in a low way sosai ya ce. "Are you sure?". Ya faɗa yana ɗage mata gera guda. ALLAH sarki har ya mance me Abba yai mashi, masoyiya ta kwantar mashi da hankali. Tafukanta ta ware, kumatunsa dikka biyu ta tallabo, tana murmushi ta ce. "I'm very sure my gentle chaos". Ta faɗa tana ɗan matse kumatun nasa....... Zuba mata idanu ya yi yana jin wani irin tsantsar kaunarta na ratsa mashi zuciya, haɗe fuskokinsu ta yi, ko kunyar kallon cikin kwayar idanunsa bata yi, a shagwaɓe ta ce. "My gentle chaos ina sonka sosai". Wani irin kallon kauna ya ɗan bita da shi kafin in a low way sosai ya ce. "Love you more, from the button of my heart, love everything about, coz you're special". Ɗan ɗagowa ta yi, ta sumbaci gefen lallausan kumatunsa, tana murmushi. Hannu yasa ya shafi soft cheek ɗinta game da lumshe idanu, a cikin ransa yana jin zai samu hanyar rabuwa da Rimsha, shi bama wai rabuwa da ita ba, bai damu ba dan bai ɗauketa mace ba, bai yarda matarsa bace dama, amma dai koma me yana tsoron ɓacin ran Seraphina sosai, shiru ya yi yana tinani, can ya tina why not ya haɗa guru da Rimsha? Saboda Abba yana da abu guda ɗaya, idan Rimsha da kanta ta same shi ta ce bata son Aryan lallai zai yarda ya raba wannan aure, hakan kuma ba zata faru ba har sai Rimsha ta faɗa son wani. Da alama hanya ce ta haɗuwarta da guru wannan aure nasu, tabbas zai ɗauketa ya kaita gidansu, ta rayu a cikinsu matsayin sister ɗinsa, daga nan guru zai fara sonta, idan soyayyarsu tai zurfi Rimsha ba zata iya rabuwa da shi ba, tabbas zata faɗawa Abba bata son shi, shi kuma zai raba wannan aure nasu, daga nan shi kuma Aryan ɗin bayan ya saketa ya aura mata scorpion ɗin, tabbas zai wahalar da ita ta yadda ba zata taɓa jin son shi a ranta ba, hakan zai sa ta fara son guru da wuri ayi komai a gama. Lallai wannan shawara ta yi, tina haka yasa ya sauƙe dogon numfashi....... Lallai nima na shaida, wannan wata hanyace ta haɗuwar Rimsha da guru, ko kuma Lion da Rimsha ba........... 👀 Cikin zolaya ya ce. "My Cherry yanzu idan na ce mata biyu zan aura zaki yarda?"........ Zazzaro idanunta a kansa ta yi, sai kuma ta tamke fuska tamau. "No daddy, ni kaɗai zaka aura, babu wani mata biyu!". Tana hura dogon hancinta ta faɗa, zallar kishinsa ya gani kwance a cikin kwayar idanunta tin ma bata san menene auren ba. Kai ya jinjina tare da cewa. "Yadda kike son kawarki Rimsha ɗin nan ba zaki yarda ku auri miji ɗaya ba?"........ Siririn dariya ta ɗan yi kafin ta ce. "Mijina ni kaɗai ne, ita ma mijinta ita kaɗai zata aura!". ....... "But why?". Ya tambaya cike da mamaki, dan ya zaci sai wacce tasan aure take kishin mijinta ai. Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi game da cewa. "Daddy ba kace in daina maganar da bata dacen can ba?". Kai ya jinjina alamar haka ne ya hanata, ohk sai yanzu ya gane nufinta, watau ba zata yarda wata mace ta raɓesa har ya haɗa jiki da ita ba, lallai Seraphina ta wuci tinaninsa, miƙewa zaune ya yi, sai ya canza topic na hirar kafin ta jefa mashi wata maganar ta juya mashi ƙwaƙwalwa. Ƙarisa hayewa saman gadon ya yi tare da kwanciya da kyau, ya jawo pillow ya ɗaura a kan kirjinsa, yana binta da wani irin narkakken kallo mai narka zuciya ya ce. "Ina jin kamar ke na rumgume ba pillow ba, zan yi barci kada ki tasheni". Wani haɗaɗɗen murmushi ta saki wanda ya fito da dimple ɗinta sosai, har wushiryar dake tsakanin fararen hakwaranta tas ya bayyana. "Daddy kana feeling love a kaina kamar yadda nike ji a kanka dama?"....... Kai ya jinjina mata alamar. Da sauri ta dawo kusa da shi, ta haɗe hannayenta ta kama kumatunta, cikin shagwaɓa ta ce. "Daddy, let feel our love". "Sure?"...... Kai ta jinjina. "Let feel it daddy"....... Ɗan nisawa ya yi tare da ƙara ƙanƙame pillow ɗin a kirjinsa, kamar mai raɗa ya ce. "Give me some love words that will make my sleep more nice, idan na tashi zamu cigaba da hira, now I'm feeling sleeping, jiya ban yi barcin dare sosai ba". Kai ta jinjina tare da matsar da face ɗinta dab shi........ "Love you more my gentle chaos, a dik lokacin da ka ji kamar kana kaɗaici, remember that you have a beautiful wife, sister, baby, Cherry, beside you, ina tare da kai to make your smile more beauty, make your heart more peaceful, make your body more........". Fasa ƙarisawa ta yi, saboda tai mashi alƙawarin ba zata sake yin maganar da bata dace ba. To Tin da ta fara magana ya tsare ɗan bakinta da kallo, zuciyansa na ingiza shi da ya yi kissing ɗinta kawai, ya rabb, shi kaɗai yasan me yake ji a kanta, kome take yi ƙara kyau take yi, kome ta yi burge zuciyansa take yi, shirmenta abin so ne a garesa, kalamanta abin so ne a garesa, soyayyarta ya zame mashi jinin jiki. Matsawa ta yi ta ɗan sumbaci cheek ɗinsa tana faɗin. "Sleep well, make sure that i come into your dreams as your wife, ina kwance a saman kirjinka ina......". Still kame bakinta ta yi, ta fasa ƙarisa maganar. Slowly ya lumshe idanunsa yana jin wani irin daɗi a ransa, lallai Seraphina ta fara natsuwa, sau uku kenan yanzu tana kame bakinta taki ƙarisa magana saboda ya hanata, kai lallai ya ji daɗi sosai yau. Ganin ya lumshe idanu ne yasa ta tsaresa da kallo tana jin sabon sonsa yana shigarta. After like 5 mins slowly ya waro idanunsa kai tsaye a kan face ɗinta, in a sleeping voice ya ce. "Stop looking at me Cherry". One side smilling ta saki kafin ta ce. "Daddy ni da fuskan mijina zaka ce in daina kallonka?". Tana turo baki ta kai karshe. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a kan shafaffen cikinsa dake da guraye saboda gym da yake yi, in a sleeping voice ya sake cewa. "My cherry, I'm feeling hungry sosai, ban yi breakfast ba, dinner ɗin jiya ma ban ci ba". Yana magana yana lumshe idanunsa, watau sai da ya zo wajenta ya samu natsuwar iya gane ashe yana jin yunwa. Da sauri ta ɗaura hannunta a saman cikin nasa, daidai in da hannunsa yake, sai ta ce. "Daddy tashi in yi feeding ɗinka, bari in je in haɗa maka abinci a kitchen". Ta faɗa tare da yunkurawa zata miƙe, da alamar tausaya mashi sosai a kan fuskanta. Slowly ya riko hannunta cikin nasa, ɗan jawota ya yi, sai ta tafi gabaɗaya ta faɗo kansa, fuskokinsu yana saitin na juna, in a low way sosai ya ce. "Let me sleep first, idan na farka sai ki bani abincin a baki kin ji?". Kai ta jinjina alamar to ta gagara yin magana, saboda yadda ta kalli kwayar idanunsa dab ita ya rikita zuciyarta. Slowly ya saketa game da lumshe idanunsa, kafin wani ɗan lokaci ya yi barcin gaske mai daɗin da ya jima bai yi irinsa ba. Shiru ta zauna tana ta faman kallonsa, bata son matsawa daga kusa da shi ko kaɗan, tana ganin kamar rabasu za'ayi idan ta matsa, har da kwanciyar ruf da ciki, ta ɗaura kanta a saman kirjinsa, tana kallon face ɗinsa, a hankali barci ya ɗauketa ita ma. CRYSTAL PALACE, idan na kira sunan CRYSTAL PALACE a yayin da muke cikin CRYSTAL PALACE ɗin muna labari to ina nufin zuciyar CRYSTAL PALACE gabaɗaya ne, watau gidan MUHAMMAD HAIZA'AN, gidansa ne zuciyar CRYSTAL PALACE, gidan da ya fita daban a tsarin ginin cikin CRYSTAL PALACE ɗin, gidan da aka ware a waje daban, yana gefe can, wani shinfiɗaɗɗen titi da aka shinfiɗa wanda ya miƙe har cikin gidan kawai abin kallo ne, kun san dukiya tai kuka ba kaɗan ba, ya rabb, tin daga farkon titin nan jiga-jigan jami'an SSO ne suke shawagi, ko tsuntsuwa basa bari ta gifta ta sararin samaniyar gidan Haiza'an, lallai na shaida dik wani karfin iko ya kare a wannan waje. Zaku rantse da ALLAH dik jami'an dake US aka zuba a wannan gidan, wasu irin guards waɗan da ko fuskansu baka iya gani face idanunsu dake rikitar da zuciyar bawa su ke gadin gidan, ya kuke tinanin san da yake raye kenan? Wai a haka ya rasu ne wannan karfin ikon! Ya ALLAH. To mu yi tattaki zuwa cikin gidan dan mu ga meke going a ciki, ya tsarin gidan yake tin da na ce ya fita daban da tsarin sauran gine-ginen dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Jama'a ban taɓa tinanin za'a samu gidan da zai fi Black Tiger empire haɗuwa ba, sai ga CRYSTAL PALACE da kanta, ga kuma uwa uba zuciyar CRYSTAL PALACE watau gidan Haiza'an, ya ALLAH kai mana arziki mai albarka kawai. Siffar ginin gidan ya kasance irin ginin mediterranean ɗin nan ne ta gefe-gefe, daga ta gaban gidan kuwa zallar glass ne, girman gidan ya fi fili flot 20, saɓanin benayen CRYSTAL PALACE shi wannan gida yana da gate, an kewayesa ne, sai kun wuci gate uku manya-manyan masu cike da tsaro na ban mamaki kafin ku ƙarisa cikin gidan, sannan shi wannan hawa uku ne kawai. A gefe guda harabar gidan ga tampatsetsen lambu mai ɗauke da ƙananan arche, ƙananan ƙoramu ne da aka yi su dan ƙawata lambun, ga wasu irin fitillu da aka ƙawata lambun wanda ko dare ne zaku zaci rana ne saboda haskensu da ƙawarsu, uwa uba lambun da glass wall aka kewayesa, daga waje kana iya hango haɗuwarsa ta ciki, ya ALLAH, ga wasu kifaye orange and red da aka zuba cikin tampatsetsen glass suna ta yawo cikin ruwa, shi ma ya ƙara ƙawata lambun matuƙa, ga wasu flowers masu mugun kyau da ɗaukar hankali, a bakin kofar lambun daga gefe an yi wasu flower da aka shukasu aka yi siffar sunan HAIZA'AN'S GARDEN da su, jama'a wlh lambun nan ya haɗu fiye da yadda kuke hasashensa a ranku, kuɗin da aka narƙa a wannan waje, kai kuɗin mahaikatan dake gyran lambum nan kawai jarin wani ɗan siyasa ne a Avaris!. A budget ake cire kuɗin masu aikin gyaran gidan Haiza'an, a shekara ake lissafi a cire kuɗin masu gyaran gidan, akwai mata akwai maza, kowa da aikinsa, kullum na ALLAH sai sun share ko'ina sun gyara tamkar yana raye............ Jama'a baku tunanin bayan mutuwar daddy Haiza'an akwai abin da ya faru kuwa?. A tsakiyar tampatsetsen harabar gidan akwai wani waterfall wall, architecture design of gunking zaki ne dake faman fesa ruwa daga bakinsa, ya wage baki sosai ruwa na zuba ta bakin nasa, a ƙasa an yi mashi round tamkar rijiya ruwan da yake zubarwa tana taruwa a wajen,

Chapter 74 of 95