sunan da Cherry bloom, shi dai yasan da boy ya yi saving number Leo, kuma Leo ne kawai zai kirasa video call sai kuma Vir or Aryan, guru ma yana gida.
Ɗan jujjuya wayar ya yi yana son tabbatarwa da wayansa ne kuwa? Daidai lokacin kiran ta katse, yana ƙoƙarin kunne wutar ya duba wayar waye sai ga wani kiran ya shigo, wayoyinsu fa idan basu da numberka kiranka ba zata shigo ba, sanin haka ne yasa ya ce dole na gida ne yake kira, dan haka bari ya ɗaga ya ga wanene dik da bai san wayan waye bane a tsakanin su ukun, nasa ne ko na Aryan or guru?.
Picking ya yi a daidai lokacin da ta ɗaga kai tana kallon Madam tana cewa. "Mom daddy baya ɗaukan kiran, kila ya bar wayan a wani waje ne"........ Ta kai karshen maganar tare da dawo da kallonta a kan screen ɗin. Ai wani irin razana ta yi ganin jade sexy eyes na Lion yana kallonta.
Ihu ta kurma tana miƙewa zaune, ta saki wayar a ƙasa tana faɗin. "He's the one! He's the one who killed my mom! Haka idanunsa yake, with this nose mask ya zo gidanmu, this is his eyes, mom he's the one!". Muryarta na rawa kirjinta na bugawa da karfi take maganar, lokaci guda kuma ta ɗauke wuta ɗiff, ta sulale ƙasa zata faɗi Madam ta rikota da sauri.
Kit Lion ya katse kiran yana jan siririn tsaki, ya janye nose mask na fuskansa ƙasa yana mamakin yarinyar yadda aka yi ta rike kamanninsa, wai da wannan nose mask ɗin ya je gidansu, da yake su IRON FIST nose mask ɗinsu kala ɗaya ne, dik duniya kuma su kaɗai ke da irinsa, su suka zaɓi design da suke so Company ta buga masu, shiyasa Seraphina ta ce da wannan nose mask ya je gidansu, hakika da irinsa ne sak ba banbanci.
Lallai yau akwai rikici tsakanin Aryan da Seraphina idan ta farfaɗo, sai ya faɗa mata dama yasan wanda ya kashe mammynta kenan, a gefe guda kuma akwai rikici tsakanin Aryan da Lion, sai ya faɗa mashi dama yana tare da Seraphina, sai ya faɗa mashi ma'anar Cherry Bloom, e kam akwai case!! Yau dai na ce bari in barku ku ɗan shana ba sai mun leƙa WS-HOSPITAL ba, ku huta da tashin hankalin na yau kam.
Likes comments and share fisabilillah.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️
QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
For more information 08161390581 Whatsapp me only.
STEP 1🔥
2025-12-19.🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️
E_____________ 57 & 58
CRYSTAL PALACE.
Gyara kwanciyarsa Lion ya yi yana tinanin meyasa Aryan yake zuwa wajen yarinyar nan har haka? Shi fa ya ce su bata rayuwa mai kyau ne, amma a nesantata da su, baya son ya buɗe idanu ya ganta a kusa da su ko kaɗan.
Kun fahimci wani abu jama'a? Lion ya tsani mata, amma har yanzu zuciyansa da sauranta a kan Seraphina, a yanzu ba wai ya tsaneta kai tsaye bane, ya tsani ta zo kusa da shi ne, dan yasan sai ta zame mashi rauni, Seraphina amana ce a wajensa, domin ya cika wannan amanar yasa bai barta ta ƙare a cikin gidan Dr sun mutu tare ba, bai ceci Dr ba, saboda suna da muguwar gaba a tsakaninsu, but ya ceci Seraphina, ya fita da ita ta window, bayan an kunnawa gidan wuta ya zo ya ɓoyeta cikin jaccuzi.
Idan bai yi niyyar cikawa mahaifinta amanar ba zai kyaleta ne a gidan cikin jacuzzin ta mutu, amma saboda ya cika alƙawarin da yayansa ya bar mashi, yana kwance gadon asibiti ya turo jami'an SSO suka zo gidan da daddare a washegarin ranar da abin yafaru, suka shiga suka ɗauketa, baya ga haka in ya so zai iya watsar da amanar da yayansa ya basa a lokacin, amma sai bai yi hakan ba, dan dik duniya bashi da biyun mutane biyun nan, daga Hussainin daddynsa sai Yayan nasa, ko zai yi fushi a kan komai ba zai yi fushi a kan mutane biyun nan ba, dan ya cika amanar gabaɗaya ya ce a bata rayuwa mai daɗi, kada ta nemi komai a rayuwarta ta rasa, ta rayu tamkar ƴar sarki a cikin kingdom, amma kada a bari ta sake ganinsa, kada a bari ta sake zuwa in da yake, ya tsani ganinta
Kun san meyasa baya son haɗa inuwa da ita kuma baya son su haɗa inuwa da mata? Domin confirm sai mata sun zame rauninsu, kuma haka ne, in dan ya ɗauki Seraphina suna gida ɗaya, ko baya sonta ya tsaneta a hankali yau da gobe suna haɗuwa sai ya zama cikakken uba a gareta, idan haka ta faru kuma zata zame rauninsa na farko, idan wani abu ya tashi ko shi ba'a iya farmakansa ba ita za'a farmaketa wanda hakan zai raunata shi sosai, tana zuwa school ai, za'a iya cutar da ita ko ta nan, amma kunga yanzu tana rayuwa a gefe, bai saba da ita ba, hasalima bata san shi ba, ko kasheta aka yi ba zai ji zafin komai ba.
Tabbas mata raunin maza ne, komai jarumtar namiji idan kunga an kaisa ƙasa to ku duba a tafiyar da aka kaisa ƙasan an haɗa da mace, idan ana son galaba a kan namiji sai da sa hannun mace, haka ALLAH ya yi zuciyar namiji, macece rauninsa. Kuma hakazalika mace tana zama karfin namiji! Dik in kaga namiji ya yi nasara a rayuwa ku duba gefensa akwai mace, shiyasa MANZON ALLAH (SAW) ya umarci maza da su nemi mace ta gari, dan yasan mace itake juya kaso 65 zuwa 70 cikin ɗari na rayuwar namiji, idan ya samu mace ta banza babin wahalar rayuwansa ya buɗe kenan, idan kuma ya samu ta kirki, babin jin daɗinsa ya buɗe kenan, Manzon ALLAH (SAW) baya kuskure, da ya ce ku nemi ta garin kawai ku nema ne, dan mata sai shirin ALLAH!.
Da kun san tarihin daddyn Lion hakika da zaku ƙara gasgata me nike faɗe, daddyn Lion yarinman da ya taso cikin gata da tsantsar kulawa, ya bar gida kan ya cewa mahaifinsa sorry, daddyn Lion mutum mai zafin zuciya da taurin rai tamkar zaki, mutumin da ya taso cikin addinin bautar rana, an gwabza yaki da kakasa dan neman ƴanci daga turawan mulkin mallaka, jarumta gadon masarautansu ne, saboda zafin zuciyansa ya gwammaci ya bar gida, ya bar gata da iyayensa kan ya bada hakuri.
Ya komo US, ya rayu kaman sarki saboda dukiyan da mahaifiyasa ta basa a lokacin da yake barin gida, daga bisani ya gane yana da baiwa, zai iya abubuwa dayawa, ya tsaya ya jajirce sosai, a tafiyarsa ya haɗu da macen da take iya canza akalan rayuwansa, dik duniya a lokacin idan ya yi fushi ita kaɗai take ce mashi calm down, ta taushesa ya haƙura.
Macen da ya so fiye da kansa, macen da ya sanar sirrinsa fiye da ɗan uwansa Hoosain, macen da in ta ɓata rai sai US ta tsaya na ɗan lokaci saboda fushinsa, idan ka taɓata to jini ne zai zuba, da dik wanda ya taɓata baya yafe mashi koma wanene, harta mahaifinta ya taɓa marinta a gabansa kafin su yi aure, kafin mahaifinta ya sauke hannu ya rama mata ɗaya tamkar dubu, daga mari ɗaya sai suma, kai tarihin daddyn Lion abu ne mai tarin darasi, zaku ji complete tarihin ba zan rage komai ba a gaba, dan ni wlh tarihinsa ya fi mun na kowa daɗi da ma'ana a labarin nan, ga tarin ilmantarwa.
Mom Lion ta ja shi ya shiga musulunci saboda tana son shi, sun shirya aure, uhm Muhammad Haiza'an, mamallakin HAIZA'AN AIRLINE, mutumin da ya tara dukiyan da yake iya baiwa gwamnatin Amurka da sauran manyan ƙasashe bashi a wannan lokaci, mutumin da in yai magana ko shugaban ƙasa baya ja in ja da shi, mutumin da karfin dukansa ɗaya daidai take dana mutane 20, ya rayu tamkar sarki a fada, ya nunawa mom soyayya fiye da dik mace, ya gatanta rayuwarta da dikkan ahalinta.
Family ɗinta dik suna fantamawa da dukiyansa, su je ƙasashen da suke so, ƙaninta sai a ƙasar da yake so yake cin abincin dare, kannenta ba'a magana, sun more fiye da tinani, idan zasu yi birthday su ɗauki jirgin ruwa tampatsetse, a tsakiyar teku ake party ɗinsu, a kashe kuɗi a cashe, dik daddyn Lion bai damu ba, ya sake masu komai, kamfanin jiragen sama yake da shi, kai na ce maku ku jira cikakken tarihinsa, amma daddy ya gatanta mom da ƴan uwanta.
Amma me yafaru? Da aka shirya kaisa ƙasa, ba za'a iya tinkararsa ba saboda karfin ikonsa, ko gwamnati tsoronsa take ji, karfin ikonsa ya baiwa CRYSTAL PALACE karfin iko a yau, dalilinsa yasa babu wani jami'in gwamnati da ya isa keta cikin CRYSTAL PALACE bare ya kama wani daga ciki, kuma har yau har gobe gwamnati na shakka da tsoron shiga cikin gidansa, gidan yana nan a rufe sai tarin jami'an dake gadin gidan tamkar akwai ran shugaban ƙasa a ciki, daddy ya sanya tsoro a zuƙatan azzalumai da zaman lafiya ga bayin ALLAH, ba ta yadda za'ayi a same shi bare a kashe shi, dole sai ta hanyar mutum ɗaya!
Mom Lion, ita kaɗai take da kusanci da shi fiye da yadda kowa yake da, ya rabb, ta zaɓi matsayin da gwamnati ta kwaɗaita mata fiye da wanda mijinta ya bata, ta zaɓi ta samu karfin iko fiye da wanda ya bata, ta aminta ta sa hannu kan zata fito da shi wajen da babu kowa a kama shi, ya rabb, baya fita sosai, sai dai a zo gida a samesa, amma a wannan rana da tsautsayi ta hau kansa, ta ce sai dai su fita yawo, ya ce ina take son su je, ta kwanta a jikinsa tana kirga mashi in da take son su je.
A wannan rana Lion ya zo gidan ganin jaririn ƙaninsa watau Nirash Leo, in baku manta ba Lion yana hannun Hosainin daddy ne. A wannan rana da ya zo bai samu haɗuwa da mom ba, dan tana wanka, shi kuma daddy baya son Lion ya zauna a gidansa saboda wani ɓoyayyen dalili nasa. MENENE WANNAN?.
Lion yana son Nirash sosai, ya ɗauki yaron, yai mashi wasa sosai, kafin mom ta fito ya kwantar da shi ya koma. Mom ta yi kwalliyar da tin da take bata taɓa yin isrinsa ba, sai tsokanarta daddy yake yi wai yau ta zama under 13, ta ƙara kyau, har ya ce gaskiya ba zai yarda ba, kafin su fita sai sun ɗan yi chaskale, dan ta yi kyau sosai, da yake ta san me ta shirya, ta yarda, a wannan rana ta bashi kanta na karshe, tin da yake da ita bata taɓa sake mashi jikinta irin wannan rana ba, har yake tambayarta meyasa yau bata mashi kukan yana wahalar da ita ta kame jikinta ba?.
Tana munafukin murmushi ta amsa da ai yanzu ta daina bashi wahala wajen saduwa, ta yi alkawarin yi mashi yadda yake so, ya ji matuƙar daɗi, a wajen ya ce ta faɗi me take so ya bata! Buɗar bakinta ta ce kyautar jirgin sama guda ɗaya, a wajen ya ɗauko ɗaya daga cikin takardun jiragen samansa, ya sanya hannu a kan wanda ta zaɓa, ya bata yana ƙara jawota jikinsa, dik bai san me ta shirya mashi ba..
Ta karɓa har da godiya, suka sake yin wanka, ta shirya Leo cikin haɗaɗɗun kaya, daddy ya ɗauki Leo a hannunsa yana sumbatar kumatunsa suka fito. Guards zasu rakasu ta ce yau fitar masoya ne, kada wanda ya damesu, hakan yasa daddy ya ce mutum biyu su rakasu, ta yi typing message ta sanar da mutanen can guards biyu ne kawai sukai masu rakiya, sun yi farinciki da jin hakan sosai.
Daddy da kansa ya tuƙa mota a wannan rana, motar da bai sake tuƙawa ba kenan a rayuwansa. Mom ta ce daji zasu je, dan yau soyayyarta ce sabo ta motsa, da yake ya yarda da ita fiye da kansa, bai kawo komai a ransa ba, ya ɗauketa suka shiga dajin, bakin teku dan hutawa, yana rike da Leo yana zura mashi harshe a bakin yana tsotsa, suka tsaya a bakin ruwa suna hirar soyayya, ya jawota jikinsa.
Unexpected suka ji harbi, an harbi guards ɗinsa guda biyu, da yake a lokacin akwai sa bakin gwamnatin wannan lokaci, sai abin ya tafi cikin tsari, yana bin gwamnatin bashin kuɗi billions of dollars, shi ne kan su biya gara su haɗa baki a kashesa, dalilin kenan da yasa suka yaudari mom da ta haɗa harda yaranta ta kashe dan a rasa magada kuɗin Haiza'an gwamnati ta ci bulus, ita kuma mom da yake kanta dusa ce a ciki, sai ta aminta da su, ta shayar da jaririnta guba, Lion ya gudu, saboda a lokacin da suka kusa kama daddyn Lion ɗin ya yi wa Hoosaininsa message kan ya ɓoye mashi Lion!.
A wannan lokaci sun gagara kama daddyn Lion, ya rike mom sun gudu cikin daji, abu ɗaya yasa ya tsaya aka kama shi, watau da ya ga mom ta sanya mashi bindiga a kansa ta ce ya miƙa wuya, ya rabb, gigitar wannan al'amari yasa ya tsaya ya gagara motsawa, macen da yake ƙoƙarin bada ransa ya ceceta ita da ɗansa, amma ita ce ta sanya mashi bindiga a kai take cewa ya miƙa wuya ga miyagu?!
Sumar tsaye ya yi, ya dinga kallonta babu kyaftawa, a wannan lokaci WS-HOSPITAL guards suka kewayesa, WS-HOSPITAL su brain ɗinsa suke so, while gwamnati kuma suna son a kashesa dan kada su biya kuɗinsa da suka ci.
Haka suka kama shi mom na tsaye, suka ɗaɗɗauresa da igiya, wlh daddy yana tsaye yana kallon cikin idon mom bai motsa ba, ta rigada ta kashesa da ransa, wannan wani irin cin amana ne mai tsananin zafi?. Taya kuke tinanin Lion zai yafe mata? Ko shaiɗan bashi da kalaman da zai sanya zuciyar Lion ya yarda da mace, wlh babu mahaluƙin da ya isa ya sanya shi ya yarda mace tana da kirki, ya taso yana ganin yadda mom da dad ɗinsa suke soyayya sosai tamkar zasu haɗiye juna, amma daga karshe ku duba fa?.
Da yake mom tasan daddy na mutuwar son yaransa, sai ta ce a tsayar da shi, kafin a wuce da shi bari ta baiwa Nirash guba a gabansa, so take ta kashesa da heart attack ne kawai....... Azzaluman suka tsaya, ta karɓi guba a hannun ɗaya daga cikin guards na WS-H, ta buɗe kwalbar, tin da uwar daddy sarauniyar Ring Of Power ta haifesa bai taɓa zubar da kwallah ba sai a wannan rana, yana gani ta tsiyaya gubar a marfin kwalbar, ta ɗigawa Nirash dake ta faman wasa a baki, take ya fara lashe baki abinsa.
Ya rabb, sai ga hawaye masu tsananin zafi sun fara zuba daga idanun daddy da suka rikiɗe suka yi jajir tamkar wuta, ya ALLAH, ko motsi ya gagara yi, waɗan nan hawaye da suna magana, da sun faɗawa duniya kalamai daga zuciyar daddy wanda zasu firgita duniya! Haka guards na WS-H suka wuce da shi, mom kuma aka dawo da ita gida da nufin gwamnati zata bata muƙami na musamman a gwamnatance.
Tana dawowa gida ta kwantar da Nirash a kan gado, ta shirya kayanta, ta ɗauki takardan jirgin da ya mallaka mata, ta fita da gudu ta bar Leo a kan gado, daga nan ta nufi gidan gwamnati, dan tasan Hoosainin daddy ba zai kyaleta ba, in duniya dik gatanta ne sai ya ga karshenta a irin wanan bakar zuciyar tasu.
Tana barin gidan sai ga Lion ya shigo, dan a lokacin ya samu labarin dik abin dake faruwa daga bakin Hoosainin daddynsa. Cikin zafa ya hau benensu, yana neman mom ɗinsa, a lokacin bai san da sa hannunta ba, dan lokaci daddy bai faɗa masu ba, sai daga baya ne ya kirasu a waya yake sanar da su har Aryan ya ɗauki kiran.
Yana shiga ɗaki ya isko Leo kwance kumfa na fita daga bakinsa, yaron yana fafutukan rai ko mutuwa, ai tuni Lion ya mance da abin da ya kawosa, ya rungumi ƙaninsa da gudu ya fita. Jama'a tarihin daddy akwai taɓa zuciya sosai, ya sha gwagwarmayar rayuwa bawan ALLAHN nan, amma zaku ji komai dallah-dallah a gaba, yanzu tsakure ne, tarihinsa shi ne the most best part a littafin nan!.
Kunga a yanzu ko shaiɗan bashi da kalaman da zai zuga Lion ya yarda da mace har ma ya sota, irin wannan zazzafar cin amana mai ƙona zuciya, hmmmm, dan haka kome Lion ya ce da mata ƴan mata ayi hakuri, ba laifinsa bane, muɗin ne muka dinga bashi darasin rayuwa mai tafarfasa bama mai zafi ba, ga Dr ma ta ƙara mashi nata ta hanyar kashe mashi yaya, ai shi Lion hmmmm na dai yi shiru, amma yaga rayuwa!.
-------------------------🔥
Baki a ɗauke da sallama Aryan ya shigo ɗakin, tin daga kan yadda yaga Lion bai amsa mashi sallama ba yasan akwai matsala, ƙarisowa ciki ya yi, ya zauna a gafen bed yana faɗin. "Bro are you okey?". ..... Zuba mashi idanu kawai Lion ya yi, babu abin da kwakwalwansa yake tariyo mashi face yadda mom and Dr suka ci amanarsa, zuciyansa ta tsananta zafin da yana ji ba zai iya magana ba, in ya buɗe baki zai iya haɗiyar zuciya ne, sai kawai ya bi Aryan da ido, lokaci guda idanun nasa suka rikiɗe suka yi jajir tamkar wuta.
Ganin hakan ba karamir girgiza Aryan ya yi ba, matsawa ya yi ya rikosa yana ƙara tambayansa lafiya, shiru bai yi magana ba, sai datse idanun nasa ma da ya yi gabaɗaya kawai. Rungumesa a jikinsa Aryan ya yi, yana ɗan shafa bayansa, sai ya tina a lokacin da suke yara in sun je gidansu Lion, idan suka gwabza faɗa suna huci sai daddy ya ɗauko ruwa ya karanta masu ayatul kursiyu kafa bakwai-bakwai ya basu su sha, take zuciyar take sanyi.
Tina hakan yasa ya yunkura zai kwantar da Lion ya miƙe kenan sai gani ya yi an miƙo mashi ruwa, slowly ya ɗago kai, guru ne ya ɗauko ruwan ya tufa mashi ayatul kursiyun, dan in da sabo guru ya saba tofawa Lion da Aryan ayatul kurshiyu a ruwa, yo waɗan nan biyun idan suka fara faɗa tin suna yara ma ai sai da ayoyin ALLAH ake shawo kan zuƙatansu, kuma a da basa taɓa kwana biyu basu gwabza faɗa ba, yanzu da girma ya zo suka rage, amma basu daina ba, sai in ra'ayinsu bai banbanta ba.
Karɓar ruwan ya yi game da cewa thanks. Guru ya buɗe mashi marfin, ya saita a bakin Lion yana ɗan shafa wuyansa, da yake Lion ɗin zuciyansa ta ɗauki zafi tamkar an ɗaura dalma a wuta, sai ya ji yana buƙatar ruwa mai sanyi, dan haka ya buɗe baki ya fara karɓa. Tas ya shanye ruwan bai rage komai ba, ajiyar zuciya suka sauƙe.
Aryan ya kwantar da shi game da sanya mashi pillow, guru ya matsa ya taɓa gaban goshinsa, babu zafi, kawai zafin zuciya ce. Da haka suka samu barci ya ɗaukesa, sai suka koma parlo suka zauna.
Guru ya ce. "Kasan da cewa suna shirin rikita media ɗin Avaris yanzu?"...... Jinjina kai Aryan ya yi. "Yeah, suna shiri ɗaukewa mutane hankali saboda abubuwa biyu dake shirin faruwa, na farko asirinsu kan amfani da tankar mai suna kashe mutane yana gab da tonuwa, na biyu shigo da sabuwar plan na sabuwar dabarar kashe mutane da karɓe masu dukiya da zasu yi"..
Guru ya ce. "Suna tafiya da plan A and B ne ai, tin da asirinsu kan tankar mai zai tonu shi ne zasu shigo da plan B, ba zadai su kyale mutanen Avaris su zauna lafiya ba".......... "Ina zasu kyalesu su zauna lafiya tin da sun karɓo kwangila daga turawan yamma, ai sai sun idasa aikinsu, Avaris tana daga cikin ƙasa masu yawan population shiyasa suke son ragesu, sai abin kuma ya zo ya haɗe masu da karfin tattalin arziki da suke da, ai kaga dole su ji a jikinsu". .....
Guru zai yi magana kenan aka fara kiran wayar Lion dake hannun Aryan, fito dawayar ya yi, ta miƙe ya nufi cikin ɗaki, jim kaɗan ya fito hannunsa rike da wayarsa yana karawa a kunne, Abba ne yake kiransa, ya ce maza ya zo ya bashi kuɗi yanzu akwai sayayyar da za'ayi wa amarya Rimsha dan gyaran jiki, Ammie ce ta ce Abba ya kawo kuɗin, shi kuma ya ce Aryan ya kawo, Dr Aryan ne bank ɗinsa.
Waje ya nufa yana ce da guru yana zuwa, da safe journey guru ya amsa mashi. Tin da ya fita bai sake dawowa ba sai 12 na dare, ya sallami Abba a kan ya tafi gidansa, dama sun san yana da gida. Abba bai matsa mashi ba, dan shi yasan irin tarbiyar da ta basu, dan haka baya damuwa idan Aryan baya gida.
Yana fita ya koma wajen Lion bai je wajen Searaphina ba, dan Lion ne a ransa, ya tafi ya barsa cikin damuwa. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin Lion, zaune ya iskou a balcony suna aiki, Lion da laptop, guru da waya. Ɗan zuba mashi idanu Lion ya yi, yana son yi mashi magana amma har yanzu zuciyansa bata sauƙa ba, he's not in a good mood, baya jin ma zai iya motsa bakinsa ya yi magana, sai kawai ya bi Aryan da ido.
A kusa da shi Aryan ya zauna, cikin sanyin murya ya ce. "How are you feeling now?". Ya faɗa yana kai hannun jikin Lion ɗin, ya ɗan taɓa forehead ɗinsa, babu zafi, kitson kansa dake watse ya hau tattara mashi kafin ya sake tambayansa meyake damunsa?.
Shiru Lion bai tanka ba, a gabaɗaya wannan dare uppan bai furta ba, sun yi juyin duniyar nan yaki ya yi magana, daga karshe ya miƙe ya je ya kwanta, bayan ya kwanta suka bisa ɗaki, Aryan ya dinga lallaɓasa kan ya tashi ya ci abinci, amma ko motsawa bai yi ba, daga karshe ya ja bargo tare da lumshe idanunsa, dik yadda zasu yi sun yi, suka kira Vir suka haɗu, suka dinga mashi magiya, amma Lion yaki ya yi magana, yaƙi ya ci abinci, yaƙi ya kula kowa, tsabar zafin zuciya, a yadda ta kwantan nan haka har barci ya ɗaukesa, shi kaɗai yasan me yake ji, hmmmm ba zasu gane bane.
A wannan dare suma dakyar barci ya yi awon gaba da su, dik sun shiga damuwa, har shi Vir ɗin ma, da kyar ya rintsa, Aryan bai leƙa Seraph ba, saboda damuwar da ya shiga.
Washegari da asuba suka farka domin zuwa Masallaci, ga mamakinsu sai basu ga Lion a gidan ba, sun ji mamaki sosai, dan sun san baya fitar asuba haka, sai dai in wani meeting ya je kafin ya dawo asuba tai mashi a can, wani meeting ɗin nasu kuma da asuba ake farawa, amma haka kawai baya fitar asuba. TO INA YAJE?
Numbersa Aryan ya fara kira, sai dai a kashe take, Aryan ya shiga damuwa sosai, a daddafe suka yi wanka, suka shirya suka tafi masallaci. Bayan sallar asuba suka kira yaransu na SSO, sun tambayesu Lion suka ce bai zo ba, sun kira mr President suka tambayi ko Lion ya ce mashi yana zuwa, nan ma ya ce rabonsa da magana da Lion tin jiya da safe. Kiran masarautar Ring Of Power suka yi, suka kira number grandma, amintattun dake mata hidima ɗaya daga ciki ta ɗauka.
Aryan ya tambayi sun samu labarin zuwan Edward ne? Suka ce a'a bai ce zai zo ba.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 69 Chapter of 95