Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta hanyar sms". Natsuwa Zaynish ya yi yana sauaronsa da kyau........ Cigaba ya yi da cewa. "Ya ce kada mu fitar da batun wa kowa, kuma ya ce dik babban sojan da ya kiramu kada mu kuskura mu bashi ainahin location ɗin da muke, koda kuwa BGA da muke ƙarƙashin umarninsa ne, in sun tambayemu in dai ba muna cikin haɗari muna neman taimako ba mu basu wrong information!". (Note, sojoji ko mutuwa suke yi basa bijirewa umarnin manyansu, idan manyansu suka kirasu suka tambayi a in da suke to dole su sanar dasu! Su Leo masu burin kawo gyara ne, shiyasa kuka ga suka birjire ta hanyar karɓar shawarar Captain, ina rubutu yadda sojojin gaske suke ne, in da nike fatan a gyara in na gyara a rubutuna zan faɗa maku ba haka sojoji suke ba ni na gyara dan ku sani kada ku ɗauka haka suke a gaske, dik abin da kuka ga ban yi baynin na kara wani abin ba to haka suke ko a zahiri ma, fatan kun gane?.) Kai Zaynish ya jinjina kafin ya ce. "Karfe nawa zamu tafi?"........ "5 na yamma ya yi, and ka sanar da su Noor, yawan haɗuwarmu mu huɗu a ɗaki zai iya haifar da zarginmu a zuƙatan sauran sojojinmu shiyasa ban kirasu ba, ka je kawai, idan ka je ka sanar da su Noor su shirya". Kai ya jinjina game da miƙewa, ya komo cikin sansaninsu, Leo kuma ya ɗauki wayansa ya kira Aryan. Cikin tantin Noor Zaynish ya nufa, a daidai lokacin Noor yana zaune kusa da V yana kokarin ɗagota ya rungume. Ya shigo ne ya ganta yadda ta kwanta daren jiya bata motsa ba, da sauri ya nufeta, yana yaye blanket ɗin ya taɓa jikinta wani irin zafin da ya ji ne yasa ya yi gaggawar zama a gefenta yana ambatar sunanta. Idanunta a datse gam, sai dai ha barci take yi ba, ga hawaye suna ta faman wanke mata gefe-gefen kunnenta. Saura one page Step 1 ya zo karshe. *Jama'ar kirki littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1 ya zo gangara, zamu shiga STEP 2 wanda shi ne ainahin labarin yake cikinsa, ZAKUNA BIYAR iya STEP 1 ne kawai free, daga STEP 2 zuwa karshe paid ne, 1k kacal yake, ki hanzarta making payment kada mu tafi mu barki, dan labarin bai ma fara ba, tarin ilmin, faɗakarwa, waazantarwa, wayar da kai, nishaɗantarwa dik yana cikin STEP 2, yanzu dik ba'ayi komai ba, STEP 1 dik sharar fagece, ainahin labarin yana gaba, in kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku Nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.* Likes comments and share fisabilillah. QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A LADY TEEMA. STEP 1🔥 2026-01-05🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ E_____________ 79 & 80 *FOLLW MY TIKTOK ACCOUNT 👇* https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP *FOLLOW MY WHATSAPP CHANNEL ACCOUNT* 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S Idanunta a datse gam, sai dai ba barci take yi ba, ga hawaye suna ta faman wanke mata gefe-gefen kunnenta. A rikice ya fara ambatar sunanta, ina bata amsa ba, karisa yaye blanket ɗin nata ya yi. Tana kudundune shiru bata iya motsawa ba. Shi ne ya kai hannu zai ɗagata Zaynish ya shigo. Kallo ɗaya Zaysh ya masu ya ɗauke kai, sai ya ce. "I want to talk to you, idan ka gama ina ɗaki". Bai jira amsar Noor ba juya ya fita, bai zaci V tana ciki bama da ba zai shigo ba. Ɗagota gabaɗaya ya yi tare da ɗaurata a saman kirjinsa, cikin kiɗima ya ce. "I know that you're hearing me, please talk to me my Juliet"....... Shiru bata motsa ba, tana dai cigaba da hawayeta. Hannayenta ya riko cikin nasa. "I'm so so sorry my Julie, I know I have wronged you greatly, I have punished you severely, but it is not my fault, it is your intense jealousy that makes me feel hurt when someone interferes in your business or speaks to you". Yana shafa kanta zuwa bayanta ya faɗa. Ya sake cewa. "You know that i really love you more, right?"........ Sai a lokacin ta ja doguwar numfashi game da saukewa a hankali, slowly ta ɗan motsa idanunta kafin ta buɗesu. Da sauri ya ɗan datse nasa idanunsa saboda ganin yadda idanunta suka yi jajir kamar wuta. Intently ya waro idanun nasa a kanta. "Sorry my Juliet". Ya faɗa in a low way. Kallonsa kawai take yi bata yi magana ba. Wayansa ya ɗauko, number Manassa ya kira, bugu ɗaya ta ɗauka, a takaice ya ce. "Comes to my room with your rucksack now". Daga haka ya katse kiran. Ajiye wayar a gefe ya yi, ya dinga lallaɓata tamkar kwai a saman plate, ya yi nadamar abin da ya yi mata, bai kamata ace ya yi fushi har su kwana waje daban-daban ba, ya zafafa dayawa sosai. Manne da juna Manassa ta shigo ta samesu, sai da ta kame ta sara mashi sannan ta yi dropping rucksack ɗin nata a ƙasa. Kwantar da V a jikinsa da kyau ya yi. "Zo ki duba mun lafiyarta". Ya faɗa ba tare da ya kalli Manassa ba. Da sauri ta jawo rucksack ɗin ta nufosa tana faɗin. "What's wrong with her sir?". ..... Bai iya bata amsa ba sai ido da yake bin V da shi, dik hankalinsa ya gama tashi bawan ALLAH. A kusa dasu Manassa ta ajiye rucksack ɗin nata, ta fito da wata ƴar na'urar gwajin cuta, cike da kwarewa ta fara duba V. Shiru ya yi yana kallon matar tasa, yana jin kamar a dawo mashi da ciwon jikinsa a barta ta huta. After like 10 mins Manassa ta ɗago ta kallesa, a natse ta ce. "Sir wannan ba zazzaɓin kwayar cuta bane, damuwa ce da yawan kukan da ta sha, tana ɗan samun farinciki ya musanya damuwar zata warware"........ Kai ya jinjina alamar to kafin ya ce. "Thank you sister". Manassa da rashin ji, tasan V bata son allura, sai ta ce. "But sir, akwai wani injection ɗaya da zan bata yanzu dan ya saukaka zafin jikinta"........ Ai V bata san time ɗin da ta waro idanunta waje ba, ta sa hannu ta ƙanƙame Noor sosai, da kyar muryarta na rawa ta ce. "My Romeo, don't let her inject me". Idanunta na ciccikowa da sabon kwallah ta faɗa. "I can't". Ya faɗa yana ɗago da kallonsa a kan Manassa. "Is it really necessary that she must be given injections?". Manassa looked at him and said. "Yes sir, the injections are very important, they must be given". She said, trying to suppress the laughter that was about to escape so she wouldn't ruin her plan, tsabar yarinyar nan bata son zaman lafiya, tana son rikita mana V. Noor turned his gaze back to V and said gently. "Let her give you the injections, okay? It won't hurt you, I'm here with you, alright, my Juliet?". He said as he stroked her hair. Immediately she panicked and tightly held onto his hand that was clasped with hers, her eyes trembling as they moved from his face to Manassa's face. With great difficulty she managed ta ce. "My Romeo, I don't want those injections, please, I will die if she gives it to me, they are painful, tell her to go so I can feel better". She ended up almost bursting into tears, crying pitifully as she released a warm, feverish breath. Ganin ta fashe da kukan yasa Manassa yin gaggawar cewa. "Sorry my love, ba da gaske nike yi ba, naga kin ki yi wa sir ɗinmu magana ne yasa na ce let me help him to do something that will make your mouth open and talk". Ta kai karshe tare da ɗaukar rucksack ɗinta, da gudu ta nufi waje dan kada Noor ya kamata ta saka ƴar gold kuka. Aikuwa ya yi yunkurin kamata ɗin ALLAH yasa ta tsere, kuma dama ya so ajiye mata ko rankwashi ɗaya a kai in da ya kamata, dan ta saka mashi Julie kuka, bata kyauta ba. Ganin ta gudu yasa ya kwantar da V, ya miƙe ya fito. Jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da ruwa a ƙaramin bowl. A kusa da ita ya zauna, ya ɗauko hanky ɗinsu na sojoji, a cikin ruwan ya tsoma, sannan ya rabata da kayan jikinta dikka. Dik rashin kunya na yaran GAT sai da ta ji kunyar yadda ya tuɓeta tsirara da ranar ALLAH, da sauri ta takure jikinta waje guda. Ganin haka yasa ya ɗan sunkuyo kanta, suna kallo juna cikin ido ya ce. "What again? Meyasa kike ɓoye jikinki? Is it not my property?". Tana kallonsa bata iya amsa mashi ba, ya ɗan ɗaga jikinsa daga sunkuyon, ya jawo blacket ya ɗan rufeta zuwa ciki ganin ta takure kanta sosai. Sai ya ɗauko hanky ɗin, ya matse ruwan kafin ya fara mammanna mata a fuska zuwa sauran jikinta. Tin tana ɗan noƙewa har ta sakar mashi kayansa, dama jikinsa ne, ya bi ko'ina ya dinga sanya mata ruwan hanky ɗin har sai da jikinta ya yi sanyi, sannan ya rabu da ita tare da ɗaukar ruwan ya fitar waje. Ya dawo ya ɗauki abinci, ya ɗauketa cak ya ɗaura a saman laps ɗinsa bayan ya mayar mata da kayanta, sai ya fara bata abincin a baki. Shagwaɓa ta hau zuba mashi kan ita ba zata ci ba, ita dai ya kyaleta, shi kuwa ya ce ɗure zai yi mata, ganin da gaske ne yasa ta hakura ta fara karɓar kaɗan kaɗan, yana bata yana lallaɓata kamar wata ƴar baby, bata san time ɗin da ta ci dayawa ba, bayan ya tabbatar ta ƙoshi sai ya kwantar da ita ya miƙe da plate ɗin ya fito. After like 5mins ya shigo hannunsa rike da robar, a gefe ya ajiye game da komawa kusa da ita, ya zauna yana kallonta. Lumshe idanu ta ɗan yi, can ƙasan maƙoshi ta ce. "Forgive me my Romeo, it won't happen again". Hannayenta ya riko cikin nasa. "Forgive me too my wife, nima na yi laifi kin ji?".......... Buɗe mashi hannayenta ta yi alamar ya zo, da sauri ya kwanto kanta yana kallon fuskanta. Ɗan ɗago kai ta yi, ta sumbaci lallausan cheek ɗinsa. A tare suka sauke cool ajiyar zuciya, ya ɗan saki one side smile kafin ya sumbaci cheek ɗinta shi ma...... "I love you more my Julie". Ya faɗa yana kai hannunsa saman gashin kanta, ya fara shafawa a hankali. Samun damar sauke double ajiyar zuciya ta yi, take ta nemi zazzaɓin ta rasa, ya gudu, dama na kewan masoyi ne, to daga dawowansa ya gudu, ta ji wani karfi ya zo mata, da sauri ta miƙe zaune, ya ɗan ɗagata ya zauna shima, faɗowa jikinsa ta yi tana murmushi, one side smiling ya saki tare da rungumeta sosai, yana jin tamkar ya tsaga kirjinsa kawai ya sanyata ciki ko zai huta, musamman yadda ta bashi abu mai darajarta watau budurcinta, ba zai taɓa manta wannan rana ba, shi kaɗai yasan irin musulmin daɗin da ya ji, sonta ya ninku a zuciyansa sosai da sosai kuwa. Haka suka wuni cikin farinciki da farantawa juna rai, ya kara mannewa da ita, yau tin safe bai fita koda bakin ruwa bane, yana kwance cikin tantinsa tana kwance a kirjinsa, ko yaya ta motsa sai ya ce me take so, a nan aka kawo masu abincin rana, suka ciyar da juna cike da so, yana jin kaman kada ya motsa ko nan da can. Sai around 4:30, sun yi sallar la'sar, ya dawo cikin tantinsa, nan ya iskota tsaye tana ƙoƙarin sanya botir na wandon jeans ɗin jikinta, ta yi wanka dan ta samu lafiya sosai, fitansa ya je wajen sallah ne ta samu damar yin wanka. Tana ƙoƙarin jan zip ɗin sama sai ganin hannunsa a kan zip ɗin ta yi. Ya kama zai zuge mata sai taga ya zuge ƙasa. Ɗago kai ta yi zata yi magana ya yi gaggawar haɗe bakinsu, daga nan ya ɗauketa sai saman mattress, gabaɗaya ya manta bata da lafita, ya aikata abin da bai yi ba jiya, ya yi mai gabaɗaya, yana mata kuka tana mashi kuka ita ma, yana sambatun daɗi ita kuma tana na azaba. Dik ya wanke mata gefen wuya da hawayensa na kukan daɗi. Sai da ya samu gamsuwa mai kyau sannan ya kyaleta, ya ɗan rungumota ya hau rarrashi bayan ya goge nasa hawayen kenan. A lokacin saura 20 mins su tafi wannan aiki. Bai sanar da ita akwai in da zasu je ba, da ya kammala rarrashinta sai ya ce. "Kada ki je ko'ina, ki zauna a nan zamu je wani waje, and ki kunna laptop ɗinki, get ready and wait for my call". Tana turo baki ta amsa da. "To amma kada ka jima"...... Kai kawai ya jinjina mata, dan yasan jimawa kam dole ne, in sun yi sauri ne su dawo gobe cikin dare, wajen yana da nisa. Haka ya lallaɓata kafin a gurguje ya miƙe ya je ya yi wanka, ya fito ta taimaka mashi ya shirya cikin normal kayan ba uniform ba, sai yabon kyansa take yi, musamman European hair ɗinsa dake nannaɗe kamar indomie. Ya jawota jikinsa ya rungume, yana shafa bayanta, ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, a kunne yai mata raɗa kamar haka. "This thing is so sweet, over and over, zan tafi ina farinciki matuƙa, my God bless you my wife, i love you forever and ever"........ Ta rikosa ta bayansa kafin ta ce. "Take good care of yourself my Romeo, ka dawo da wuri, dan ka fara saba mun da kwanciya a jikinka, bana jin zan iya barci ba tare da kai ba". Ya ɗan sumbaci forehead ɗinta, yana kokarin saketa ta yi gaggawar ɗaga kafafuwanta ta haɗe bakinsu. Cikin zafa ya fara kissing ɗinta yana lumshe idanu, a can bayan wasu duwatsu dake nesa da tantinsu kuma su Zaysh suna tsaye suna jiransa, dik ya susuce a kanta, yana jin tamkar kada ya tafi, kaman dai ya zauna da ita, sai ma da ta kara zautar da shi, a cewarta wai dan kada ya daɗe, dan ta yi maganinsa yasa tana tsaka da kissing ɗin nasa ta ɗaura hannunta kan gaban wandonsa. Lamarin da ya kara gigitar da shi, yana jinsa da karfi da lafiya, yana jin kamar idan aka barsa daga nan har washegari da safe zai ta yi babu hutawa ne, gani ma yake yi ko mata irinta cikin trailer aka kawo mashi kafin wayewar gari zai gama da su, yana jin kamar ta mashi kaɗan ita kaɗai. Tana ɗaura hannu kan gaban wandonsa ya rikice mata, tuni ya tura hannunsa cikin rigarta ya fara wasa da kirjinta, dama ba dan ya ƙoshi ba ɗazun ya saketa, sai dan tausaya mata kawai. Cak ya ɗagata sai kan mattress, ya manta da cewa zai yi tafiya, ya hau ƙoƙarin rabata da kayanta sai ga kiran Leo ya shigo wayansa. Da kyar ya iya zaro wayan, bai lura da waye mai kiran ba, idanunsa sun rufe ya yi picking up, cikin romantic voice ya ce. "Hello"...…... Tin da Leo ya ji haka ya gane karatun, sai ya ce mashi. "One minute". Daga haka ya katse kiran. Zaynish da Vash suna zaune a kan duwatsu suna ɗan hira sama-sama. Ai Noor jifa yai da wayar dik da ance mashi one minute, bai saurara ba, ya rabata da kayanta ya sake gwangwajewansa, sai da ya samu natsuwa ne ya tina da abin dake faruwa. A gurguje ya diro kasa, in less than 5 mins ya watsa ruwa a jikinsa ya dawo, this time ƴar kaniya tana kwance ta gagara miƙewa, idanu sun raina fata, ta yi kuka har idanun suka kumbura bai sarara mata ba, da ta ce bata ji, jiki dik ya yi laushi. Ta gagara miƙewa tai wa masoyi rakiya. Sai shessheƙa take yi, a gabanta ya tsuggunna bayan ya kammala shiri, ya riko hannunta ɗaya, ɗayan hannunsa ya ɗan shafa kanta. "Ki shirya mun kanki, in na dawo sai mu yi round 3 ko my wife?". Ya faɗa cikin zolaya kuma cike da sabuwar kaunarta. Kallonsa kawai take yi ta gagara yin magana. Ya sumbaci cheek ɗinta kafin ya sama albarka, sannan ya miƙe, yana kallonta cike da so, tamkar kada ya tafi ya barta, haka ya jure ya fito, kai tsaye ya nufi in da suka yi zasu haɗu. Ita dai tana kallonsa har ya kurewa ganinta sannan ta lumshe idanu. Mu koma baya kaɗan. A tare Jehan da Arya suka wuni, sai dai wunin yau gabaɗaya ya karewa Arya ne da tinanin Leo da kuma tunanin tausar da yai mata a cikin ranta, ga shi bata samu damar ganinsa ba, dan bai fito waje ba, yana cikin tantinsa sai lokacin sallar azahar ya fito, a lokacin ita kuma ta je wajen korama, ta yi wanka, tana dawowa rike da hannun Jehan suka ratso ta wajen da suke yin sallah. Tin daga nesa ta zuba mashi idanu, yana cikin tsantsar natsuwa, kallonsa a gabansa in da zai sa goshinsa na sujjada, yana karatun Alqur'ani cikin tsantsa natsuwa. Gabaɗaya Arya rasa natsuwarta ta yi, ta dinga kallonsa har suka wucesu, sai da ta sake waigowa har ta kusa cin karo da itace. Jehan kuwa ta ce mata da fillanci ita ma zata yi sallah, dan ta iya, tana yi wajen fulanin can. Ta kwatantawa Arya game da nuna mata su Leo ta ce irinsa zata yi, Arya ta ce to su je cikin tanti su yi, Jehan ta ce zata yi alwala, Arya ta sake rakata bakin ruwa, ta jirata ta ɗauro cikakken alwala mai kyau, sannan ta fito suka koma cikin tantinsu, ta ɗauko mayafinta da Arya ta wanke mata, wanda ƴan fulani suka bata, ta yafa shi kafin ta tada sallah. Arya ta zuba mata ido tana kallonta, sai ta ji tana sha'awar addinin, musamman yadda taga Leo a cikin addinin, sai take jin zata iya bin wannan addini, addini mai natsuwa da haifar da kwanciyar hankali. Shiru ta yi tana tinanin yadda za'ayi ta koyi addini, ya za'ayi ta yi register, wajen waye zata yi? Dan ta ɗauka register ake yi a shiga. Tana zaune har Jehan ta idar da sallah, ta ware hannu ta yi addu'a sosai, sannan ta shafa game da miƙewa ta koma kusa da Arya ta zauna. Arya na son tambayarta game da addinin amma bata san da wani yare zasu yi magana ba tin da bata jin na Jehan ita ma bata jin nata, sai ta yi deciding ta fara koya mata turanci da kuma reading, wannan tunani yasa ta fara ƙoƙarin koyawa Jehan karatu da kuma turanci. Daidai wannan lokaci Angelina ta shigo ta ɗauki mouse ɗinta ta fita, kai tsaye tantin Zaynish ta koma, tana zuwa ta zauna a gaban laptop ɗinta, ta jona mouse kafin ta laluɓo number Aunty Ummie a wayarta. Bugu ɗaya tai mata Aunty Ummie ta ɗauka, cikin girmamawa Angelina ta ce. "Hello Aunty ina wuni"...... Aunty Ummie dake hospital tana bin layi ne ta amsa da. "Lafiya lou sister ɗita, ya aiki ya gida dasu mama?"...... Angelina tana murmushi ta amsa da. "Sunanan lafiya sun ce in gaisheki". Dik da Aunty Ummie bata jin daɗin jikinta hakan bai hana ta saki murmushi ba jin cewa iyayen Angelina na gaisheta, bata jin dadin jikinta haka ta daure ta biyewa Angelina suka dinga hira har lokacin da Angelie taga Zaynish zai shigo cikin tantin, da sauri ta cewa Aunty Ummie. "I will call you back Aunty". Bata jira amsarta ba ta katse kiran. Take ta haɗe natsuwanta kafin ya shigo. Yana shigowa a gefenta ya zauna game da kai hannunsa ya jawo laptop ɗinta, a natse ya hau duba abin da yawakana. Har around 3 suna tare, sai 3:30 ne Aunty Ummie ta kira numbersa. A natse ya fara bin wayar da kallo, ita dai tana ta kallonsa, watau natsuwar Zaynish daban take a cikin sauran sojojinsu bayan Leo, ko shekara goma zaka zauna da mutum biyun nan Leo da Zaysh ba zaka iya faɗar ainahin halinsu ba, Zaysh yana da kamewa da sirri matuƙa, zurfin cikin bala'i ne da shi, a yanzu dik duniya mutane biyun nan kawai ya yarda dasu, team 1 nasu da Aunty Ummie, ko uncle ɗinsa bai yarda da shi ba, yana dai bashi girma, kuma dik duniya team 1 da Aunty Ummie kawai suke sanin me yake ciki, Aunty Ummie ma wani abin yana ɓoye mata, kamar yanzu da ya ɓoye mata suna daji, and ko su Leo wani abin yana ɓoye masu kamar yadda Leo ɗin ma yake ɓoye masu wani abin, kunga Leo ya ɓoye masu batun aikinsa na shi da Arya, baka isa iya gane ainahin zuƙatan mutane biyun nan ba, dik abin da ka ga ka sani a kansu to su suka yi ra'ayi suka faɗa maka, suna da banbanci wasu halaye, Leo yana da saurin fusata, Zaynish yana da hakurin sai ka turasa bango, Leo idan ya fusata ya yi faɗa komai ya wuce, Zaynish ba'a saran mumini sau biyu a rami ɗaya haka yake, in ka mashi sau ɗaya, ya hakura har ka turasa bango to fa ko waye kai zai zubaka a kwanton shara ne, dik basu da yawan magana, amma in suka fara magana Leo yana faɗar magana kai tsaye daga zuciyansa, ba ruwansa tai maka daɗi ko kar ta yi maka shi dai ya faɗa, ma'ana baya tauna magana, yana da ɗabiar IRON FIST na baka da wuta kuma baka da aljanna bare su ji shakkar mutum. Zaynish ba shakkar kowa yake ji ba, kawai dai ɗabia ce ta namu na ƴan Afrika, sai mun tauna magana muke yinta, dan haka baya magana kai tsaye, sai ya tauna, idan yaga faɗarta ya fi alkhairi zai faɗa, idan kuma ya ga faɗarta ba alkhairi bane yana fasawa. Dik suna da dogon nazari a kan abu, kuma in suka yi nazari suka yanke hukunci sai an sara masu, suna da mugun natsuwa, Zaynish yana da girmama nagaba da shi sosai, yana da ladabi, Leo baya ji guy ɗin nan, ya raina kowa, gani yake kowa a kasan shi yake, zaka iya nunawa Zaynish iko ya ɗauke kai ya rabu da kai, ka kuskura ka nunawa Leo iko in ta zo da tsautsayi sai dai wani ba kai ba, dikkansu idan suna son abu soyayyar gaskiya suka iya, basu iya rayuwar munafurci ba. Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar, ya katse kiran nata tare da shiga account ɗinsa, ya sayi kati na kamar 10k a kuɗin Naija, sannan ya bi kiran nata. Cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaiki"...... Daga ɗayan ɓangaren ta amsa da. "Wa'alaikumussalam"........ Wani irin natsuwa ya kara yi, cikin nuna kulawa ya ce. "Aunty Ummie lafiya na ji muryarki haka? Baki da lafiya ne?". "Eh to ina zazzaɓi ne, na zo asibiti a dubani, ba wani ciwo bane"..... Kai ya ɗan jinjina, sai kuma ya ce. "Ina yaya Faisal?"......... "Ya dawo jiya yana gida". Shiru ya ɗan yi, ya ɗan yi mamakin jin amsarta, sai kuma ya ce. "Yah Faisal yana gari kuma bai kaiki hospital ba, meyasa?"....... "Babu komai, jiya fa ya dawo da daddare, ya gaji yana barcin huce gajiya". Tin daga kan yanayin maganarta ya gane karya kawai ta yi mashi, saboda bata saba karya ba, in ta yi sai ya gane. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Bari in kirasa mu gaisa". Ya faɗi hakan ne dan ya fahimci gaskiyarta, baya son ya ce tai mashi karya saboda na ce maku yana da girmama manya,

Chapter 93 of 95