haka yana cikin gidan nan, weeding 2 mins ku kawo shi nan". Yana rufe baki uku daga cikin yaran suka bazama waje dan nemosa. Ɗayan kuma ya cigaba da rike matan, shi kuma eagle ya hau kewaye room ɗin yana dube-dube. Har toilet ya buɗe ya leƙa babu kowa.
After two minutes sai ga waɗan nan yara nasa sun dawo da yar gudunsu mai kama da jungling. "Eagle babu kowa fa a cikin gidan nan, ita kaɗai ce".
Gabanta Eagle ya dawo ya tsaya. "Ina yake?!". Ya faɗa in a harsh way. Tana kokarin dawowa cikin hayyacinta na azabar ja mata gashi da suka yi ta sake rasa sauran hayyacin da ta yi ƙoƙarin tattarowa saboda marin da Eagle ɗin ya sake ɗauketa da shi. Taga-taga ta yi tin daga nan ta rasa hayyacinta.
Hannuna yasa ya damki gashin kanta da ɗayan yaronsa yake rike da shi, jijjigata da karfi da gashin ya yi kafin ya hankaɗeta ta tafi ta bugu da jikin bango ta yi baya-baya ta faɗi kasa. Takowa ya yi zuwa in da take, kafa yasa babu imani ba tausayi ya fara kai mata hamɓari a ciki da karfin gaske, ga wannan uban boot ɗin nasu mai balain tauri.
Matsawa kusa da shi dikka sauran yaran nasa suka yi suka yi mashi zube suna kallonsu. Hamɓari bana wasa ba yake kai mata a ciki, tin sautin kukanta haɗe da nishi yana fita da ɗan karfi-karfi har ya koma fita a hankali numfashinta na sama-sama. Sai da ya ga bakinta ya fara fitar da aman jini sannan ya duka ya sake damko gashin kanta, da shi ya sake ɗagata, ya hau janta har izuwa gaban mirron dake ɗakin.
Da karfi ya sake jijjigata kafin ya rotsa kanta a jikin mirror ɗin. Wani irin marayar kara ta saki mai ɗauke da nishin gaske. Jawota baya da gashin nata ya yi, take fuskarta ta yi damege, jini ta ko'ina yana ketowa ne, glass na mirror dik ya caccake mata fuska.
Ko kaɗan babu alamar Eagle zai tausaya mata, ya sake janta zuwa jikin bango, da karfi ya jijjiga kanta ya sake bugata da bangon, ji kake dum. A daidai wannan lokaci ko numfashi bata yi, jifa da ita a ƙasa ya yi, ta kwanta flat. Wannan shegiyar boot ɗin nasu yasa ya take mata wuya da shi.
Sai da ya ga alamar ta daina numfashi gabaɗaya, sannan ya zare kafarsa tare da ɗagowa ya kalli yaran nasa. "Nasan tabbas yana cikin gidan nan, dan ta yi mashi aiki, kuma ba zai iya gudu ba saboda yaranmu dake bakin kofa, dan haka ku sake bazama ciki, dik wata halitta mai rai dake ciki ku tabbatar kun kashesa koda kare ne, sannan dik wasu tankar gas dake gidan nan ku kunnata, in har bai fito da kansa ba to zai mutu a cikin wuta ne!!". With harsh voice ya yi magana, kuma cikin bada umarni.
Da okey suka amsa mashi kafin su bazama waje dan cika aiki. Shi kuma waje ya samu a saman gefen bed ya zauna tare da ciro wata waya yar karama irin wacce ake haɗata da tauraron ɗan adam, wayace da dik balain mutum bai isa ya bi diddiginka ba, sannan wayace da sam-sam ba'a isa a kiraka ba sai dai kai ka kira mutum, ita akewa labari da s-phone, dayawa daga cikin shugabannin manyan kasashe na duniya da ita suke amfani dan tana da mahaukacin tsaron gaske, gata yar karama tamkar nokia mai sim card guda ɗaya.
Latsa botiran wayar ya yi for some minute da ba zasu gaza biyu ba kafin ya karata a kunnesa. Ba'a iya jin me ake faɗe on the other side, shi dai ya ce. "Done the work isn't means success for you, but for me......". Yana gama faɗin hakan ya kase kiran tare da mai da wayar cikin aljihunsa, sannan ya yunkura zai miƙe kenan yaran nasa suka shigo da gudu irin na shahararrun gangsters.
A gabansa suka tsaitsaya, cikin girmamawa suka ce. "Aiki ya cika, harta karen dake gidan nan bamu barshi da rai ba, sannan akwai gas har guda uku a kitchen na kasa, sai kuma fetur da muka sami a gen room three jarecan, shi ma mun bi ko'ina a gidan mun daddala shi, bamu bar wata alama ta makama da za'a iya gane ba wuta ce ta tashi ba!". Yadda suke magana cike da kwarewa a aiki, da alama sun jima a wanna harka sun kware.
Jinjina kai ya yi cikin nuna alamar yarda da aikinsu, sannan ya miƙe tsaye ya nufi bakin kofar fita. Sai da ya fita ta waje sannan ya ce. "Kuna sauka parlon kasa ku danna wuta". Yana gama faɗar hakan ya yi gaggawa wucewa.
Da sauri suka rufa mashi baya. Kamar yadda ya faɗa suna fitowa suka dannawa gidan wuta tare da yin gaggawar ficewa waje. Take ko'ina ya kama bal-bal-bal.
A jere suka fito waje, suna fitowa suka nufi wasu jiga-jigan motoci masu rai da lafiya bakake kirin dake can nesa da gidan. Motoci biyar ne cir, da gudu irin na gangstars suka karisa wajen motocin. Nan suka isko Eagle DA sauran yaransa a cikin motocin yana zaune, ciki suka shiga, da gudun gaske suka figi motocin nasu suka danna kan shararriyar titin dake shinfiɗe har barin unguwar.
Wutar kuwa ci take bal-bal-bal har sama wanda hakan ya yi sanadiyar farkawar al'umma daga barci. Nan fa aka fara ihun gobara-boraba, take suka kira fire service. Abinku da babban ƙasa cikin ƙanƙanin lokaci sai ga fire service guda uku manya-manya. Basu ɓata lokaci wajen ƙoƙarin kashe wutar ba, sai dai kuma ina, ta rigada ta kama over, har tana shalle ta capki makota. Wani gas da ya fashe wutar ta yi sama sai ga shi ta kama gidan dake kusa da su.
Hankalin jama'a ne ya kara tashi, kowa faɗi yake ina Dr Hushaima da ɗiyarta suke?. Nan fa hankalin al'umma ya kara tashi sosai, take aka kira hukumar cetar rai daga gobara, abin ku da manya kasashe ko mintuna biyar ba'ayi ba sai ga jami'an sun iso, wasu jiga-jigai da su, suna sanye da kayan karisa daga gobara mai ɗauke da chemicals da dama.
Ji kake dirim dim suna dirowa daga saman bayan motocinsu da wani mahaukacin gudu, hannunsu rike da wani talanki mai karfin gaske da zai taimaka wajen kare masu wutar. Kan kace me ga jeri gwanon motocin jiga-jigan sojoji, ƴan sanda da kuma hukumar CIA. A wannan rana dai wannan unguwa sun ga tashin hankali na kin karawa.
Da gudu jami'ai biyar suka kutsa cikin gidan, wutar nan kara ci take tamkar ana kara rurata, gabaɗaya fire service da suka zo tamkar basa yunkurin kasheta, saboda gaba take ci over.
Jami'an sun samu sun shiga tsakiyar harabar gidan, amma babu hanyar kutsawa ciki, saboda door ɗin parlo ya fi ko'ina kamawa da wuta, su Eagle sun san za'ayi yunkurin kawo taimako shiyasa yaransa suka fi zubawa jikin door fetur sosai, sun kware a iya aiki over shiyasa.
Dik yadda waɗan nan jami'ai da jama'ar unguwa suka so cetar Dr Hushaima da yarta abin ya faskara, domin babu hanya, suna ji suna gani suka ja da baya dan wutar ta zarce yadda suke tinani. Tin karfe 5 na asuba ake abu ɗaya sai karfe 12 na rana suka samu damar iya kashe wutar, amma ya ci gidaje almost 10 zuwa sama. Gidan Dr Hushaima ko tsinke ba'a iya fitarwa ba, komai ya kone kurmus, gwara ma sauran gidajen akwai abubuwan da suka ɗan ragu, amma nata gidan abin ya munana sosai. Jama'a sai jimami suke yi, sunga balai yau.
Bayan lafawar gobar fire investigation, ATF sun halacci wajen domin binciken menene ya jawo wanna gobara mai karfi haka?. Sai dai iya bincikensu ya nuna masu cewa gas ce ta fashe, bayan ita basu samu wata makama ba. Jama'ar unguwa faɗi suke Dr Hushaima tana da balain kula, ya aka yi aka samu wanna matsala, amsar da mutane suka rasa kenan.
TO FARKO KENAN DAGA LITTAFIN ZAKUNA BIYAR, SHIN YAZATA KAYA? INA YAR DR? SHIN HAR DA ITA TA RASA RANTA NE? INA WANDA DR TA CETA? MEYASA DR TA ZAƁI TA RASA RANTA A KAN TA BUƊI BAKI TA FAƊI IN DA YAKE? MENENE ZAI BIYO BAYA BAYAN MUTUWA DR DA YARTA? MUJE ZUWA AKWAI KALLO NAN GABA KAƊAN.
SHIN MUTANE NE ZAKUNA BIYAR ƊIN? DABBOBI NE? WHY ZAKUNA BIYAR? BA ZAKI TAƁA SANIN ZAKUNA BIYAR BA HAR SAI KIN BIBIYI WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSA HAR KARSHE, KAMAR YADDA NA CE A FARKO, BA ZAN CE KOMAI BA, NA BARKU DA ALKALANCI.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA STAR LADY TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥
PRINCESS TEEMA
A-K-A
STAR LADY.
2-11-2025.🔥
E_____________2.
NEW YORK.🔥
Jami'an sun yi iya bincikensu amma ba su iya gano menene ya haddasa wannan gobara a cikin gidan ba, iya abunda suka sani kawai shine gas ne ya fashe.
Haka suka kwashi jiki suka bar gidan jama'a cike da jimami kowa ya koma bakin aikinsa. A gaskiya jama'a sunyi babbar rashi, domin dr mace ce wace kowa ya shaida tana da kyawawan ɗabi'u da kyawawan halaye, duk anguwan kowa yana alfahari da ita kuma kowa yana son kasancewa tare da ita, ko me dare in baka da lafiya ka kirata zata fita ta duba maka, bugu da kari abin hanunta bai rufe mata ido ba, kome ka tambaye ta zata baka kyauta in dai bai fi karfin ta ba, gaskiya jama'a sun ji babu daɗi sosai.
Haka unguwar yau ta kasance shiru, dik da dama suna kasancewa a cikin shirun babu hayaniya, amma na yau daban ne saboda mutuwar doctor da ƴarta.
9:00PM.
Agogon birnin new york ya sake bugawa, kasancewar unguwar ta manyan mutane ne sai ya zama kowa ya shiga gida, ga kuma mutuwar da ya faru sai ya kara sanyawa ko'ina yai tsit sosai, then akwai alamar ruwan sama a sararin samaniya, hadari bakin kiri, shi ya kara kora kowa gida........ A hankali sauti na wasu irin jiga-jigan motoci da suka amsa sunansu motoci ya fara ratsowa cikin unguwar, tun daga kan yanayin sautin kukansu zaka san motoci ne na manyan kai, ajere suka keto titin wannan unguwa suna tafiya a wani irin slow montion. Motoci ne guda biyar cip.
Kai tsaye a ƙofar gate ɗin gidan dr suka paka, suna parking a tare aka buɗe kofofin motocin, kan ka ce me wasu irin jiga-jiga mutane madaka katti sun danno waje, dikkansu sanye suke da baƙar wando da kuma farar t-shirt a jikinsu, while sun ɗaura tail coat a saman T-shirt ɗin wacce ta kai masu har gwiwa. Da ka gansu ko ba a faɗa maka ba kasan wasu tawaga ne na daban, imma jami'ai ko kuma gangsters, mutane biyar ne suka fito a cikin motoci biyar, kowane daga nashi motan daban-daban.
Bawai iya su biyar ba ne a cikin motoci, a'a, akwai wasu sannan da drivers daban, dan dukansu daga back seat suka fito, cikin gidan dr suka wuce, a tare suke tafiya, in short a tare suke ɗaga kafa su kuma sauke, yadda kuka san kwararru kuma shahararrun gangster's, a haka suka shiga cikin gida.
Gabaɗaya mutanen unguwa suna cikin gida babu wanda ya san meke faruwa, saboda motocinsu ba irin motoci masu karan nan ba ne, mota ce da saita matsa kusa da kai zaka san tana zuwa, asali irin wannan motocin jami'an sirri sun fi amfani da ita ko kuma manyan gangsters da suka shahara a duniya, mota ce bata kowa ba.
Sun ɗauki a kalla minti 10 a cikin gidan dr kafin su fito a jere, ɗaya daga cikinsu hannunsa ɗauke da wata ƙatuwar abu kamar kwali aka nannaɗe, dikka sauran huɗu akwai abubuwan da suka rike a hannunsu, da alama daga cikin kayan doctor wa inda basu ƙone ba suka tattaro ko dai wani abin, dik yadda aka yi suna da alaka da ita ko makamancin haka. Cikin motocinsu suka koma, a jere suka bar unguwar kamar da suka shigo TO FA, TAFIYAR YANZU TA FARA FA WACECE DR? ME KUKE TINANIN ZAI FARU? SU WANENE WAƊAN NAN MUTANE? MU JE ZUWA DAI.
-------------------------------🔥
KASAR AVARIS.
Avaris kasa ce dake makotaka da Us a kudu ta tsakiya. Kasa ce wacce take da tarin tattalin arziki, kama daga kan man fetur, gold, red diamond, har da su uranion suna da shi, suna da tattalin arziki daga albarkatun kasa da ruwa fiye da yadda mutum yake zata. Kasa ce dake cin gashin kanta, kasa ce dake da karfin siyasa da soji, sai dai gabaɗaya mafiya yawa daga cikin states na kasan a lalace suke, ga fama da yunwa da talauci, dik da wannan tarin arziki da suke da shi, ƴan ta'addan sun hana wasu daga cikin yankunan kasan zaman lafiya, kidnappers, da ɓarayin fili dana ɓoye, cin hanci da rashawa, gurɓatattun shuwagabanni, a wasu yankunan ma ƴan'ta'addan sun fi gwamnati karfi, su ke juya gari har da karɓar haraji da sauransu, abu kamar shirin film, amma zallar gaskiya ce!! Amma mu kutsa cikin labarin zamu fahimci daga ina matsalar Avaris ta samo asali.
Eldoria State. Nan ne babban birnin kasar Avaris wanda suke ji da ita, birnine da ta ƙawatu matuƙa, domin a nan Diamon palace take, wato fadar shugaban kasar Avaris, birni ne na manyan alhazai mai ɗauke da dogayen gine-gine na alfarma, benayen da aka yi su high rise building masu design daban-daban, ga manya-manyan estate na gani na faɗa masu tsarin ginin turai, da su urban complex, glass towers, residential towers da dai sauransu. Wannan kasa tana da kyakkyawar alaƙa da turawan yamma, akan kasuwancin fili dana ɓoye, kai akwai fa abubuwa sosai sai mun kutsa ciki zaku gane karatun.
-----------------------🔥
AZURE BARRACK. Babban barikin soji na birnin Eldoria.
Shinfidaɗɗen ginine wanda aka shinfiɗa tamkar ba za'a mutu ba, ka kai iya kallonka baka iya ganin karshen wannan gini saboda girmansa, gini ne dake ɗauke da Academys kala biyu bayan sansanin soja, sannan gini ne da sai mun kutsa ciki kawai zaku iya ganeta. Dik wasu manyan jami'an da suka shahara a manyan kasashe duniya ta sansu, to AZURE BARRACK ne ta kyankyashesu, daga ƙasashe da dama ana kawo manyan gifted jami'ai dan a horar da su, dik manyan jami'an manyan kasashen dake ji da kansu a nan ake horasu cikin sirri ba tare da sanin duniya ba!.
Katafaren gate ɗin farko na shiga. Gate ɗin dakakkiyar ƙarfe ce mai ƙarfi tare da tsarin tsaro na zamani mai matukar ban mamaki, akwai kamar CCTV mai karfin gani daga nesa kilomita 5, da na'urorin tantance mutane wato biometric scanner wanda in dai zaka gifta wannan gate ɗin to sai ta yi scanning ɗinka ta turawa ɗakin da jami'ai na musamman ke kallon shige da fice na Barrack ɗin. Akwai katafaren office a bakin gate ta ciki dan karin masu gadin da zasu tarbi masu shigowa!.
Mu kutsa ciki ta shinfiɗaɗɗiyar titin da ta miƙe tin daga gate na farko har izuwa can cikin Barrack ɗin, ta ko'ina ka juya a cikin barikin nan dakakkun jiga-jigan jami'ai ne ke shawagi, ga fuskokinsu sam babu kyan gani saboda yadda suka ɗaure tamau, suna wani muzurai tamkar ba mutane ba!.
Manya-manyan gine-gine ne masu balain kyau a cikin wannan bariki, har da upstairs masu matukar tsayi dan manyan jiga-jigan sojoji. Akwai babban parade ground, babban fili mai ɗaukar mutane da yawa dan horo da taruka. Filin ya kasance da tsananin kyau tare da alamomi dan sauƙaƙa atisaye. Ga abubuwan training daban-daban a cikin wannan waje.
Yankin da offices na jiga-jigan soja yake watau headquarters yana gefe guda cikin tsari da tsaruwa. Office ɗin The General Of The Army, watau shugaban dikkan sojoji kenan, daga kansa babu wata muƙami a soji, office ɗinsa babban gini ne mai ɗauke da offisoshi daban-daban dan manyan Generals na soji kamarsu Brigadier General, Lieutenant General, Major General, General, Colonel, Captain da dai sauransu. Kowani office cike yake da kayan more rayuwa dan jin daɗisu suma. Dik wanda bai san ya barikin soja take ba to yau zai sani.
Akwai katafaren Training Academy, watau makarantar horarwa. Babban gini mai cike da ɗakunan karatu, laboratories, da ɗakunan nazarin makamai. A gefe ga filin horar da dabarun yaki da training na jiki. Ga tsarin dijital dan koyarwa, akwai allunan zamani irinsu smartboards da na'urorin koyarwa ta yanar gizo kai tsaye.
Gefe guda akwai katafaren masaukin sojoji watau Barracks. Ƙayatattun ɗakuna masu tsabta da kyau, tare da kwanciyar kula ga sojoji ko ɗalibai na musamman masu bincike tamkar aljanu, yadda kuka san hostel haka Academy ɗinsu yake, ɓangaren mata daban ɓangaren maza daban, ga tsari mai kyau. Gidan kowane soja mai muƙami ba wai ɗalibai ba ya kasance tare da wutar lantarki, ruwan famfo, da tsarin ɗumama ko sanyaya wuri.
Daga gefe can kuma akwai Military Hospital. Babban asibiti mai ɗauke da dukkan kayan aiki tamkar a wajen barrack, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan tiyata, da ɗakin kulawa na musamman watau ICU. Likitoci da ma'aikata masu kwarewa amma dikkansu sojojine, kuma su ake yiwa lakabi da surgeon Brigadiers ko surgeon Generals, to su ne likitocin sojoji.
Sannan akwai sports complex, filin wasanni daban-daban kamar na kwallon kafa, kwando, da gudun tsere. Wurin motsa jiki watau gym na zamani tare da kayan zamani.
Sai uwa uba wajen obstacle course, filin ne da aka tsara dan gwaje-gwaje da horaswa na sojoji kamar hawan igiya, gudun duwatsu, da tsallake rami, ko shiga ruwan teku, daga jin wanna abin da na kirga nasan kun gane ya yanayin wajen yake, cike da duwatse, tsaunika, bishiyoyi da kuma teku a gefe, shi a can nesa da barrack ɗin yake, dik a ciki ne, amma yana da nisa da wajen da sojoji suke rayuwa.
Kada mu yi tuya mu manta da albasa, akwai mess hall, watau wajen cin abinci kenan. Babban ɗakin cin abinci mai iya ɗaukar mutane da yawa. Kayan more rayuwa kamar ɗakunan girki na zamani masu manya-manyan gas, da tsarin rarraba abinci cikin tsari da natsuwa.
Sannan akwai armory and tech hu, waje ne dan ajiya da gwajin makamai, kamar irin su drones na yaki haka da sauransu, nasan tin daga nan zaku gane girman wanna GIDAN SOJA ya wuci yadda na faɗa a bakina ko? Sannan a cikin armory tech hu akwai gefe da aka tanada dan bincike da kirkire-kirkiren kayan fasaha na soja. Ina daurewa ne in yo maku bayanin komai dan ba zan sake dogon bayani a kan Barrack ɗin ba, Sannan kusan yadda yake da kyau idan ina rubutu kan wani ɓangare ba sai na sake tsayawa dogon bayanin yadda yake ba.
Security control center, wannan ba sai na yi magana ba tin da na ce maku waje ne da ake yaye gifted jami'ai nasan kun san tsaron wajen ai ba'a magana.
Muleƙa senior officers quarters. Gidaje masu kyau tare da kayan more rayuwa ga manya-manyan mukaman soja. Harabar gidan kowani babban jami'i ta kasance mai tsabta da shuke-shuke masu kyau dan morewarsu suma, ba iya yaki kawai aka sansu da shi ba.
Lastly akwai recreation center, wajen nishaɗi a yayin hutun aiki, akwai irinsu sinima, ɗakin wasa na zamani, da wurin zama dan shakatawa a lokacin da ba lokacin aiki ba. Lambunan zamani da shuke-shuke masu kyau dan ƙara kyawun wuri, fitillu masu kyau a kowanne ɓangare dan inganta tsaro da kyau, wutar lantarki 24h ba ɗaukewa. Hanyoyi masu kyau da babu gargada, da alamomi na kwatance watau alamomin nambobi a kan titin. Dik wani barrack na kasashen ƙetare haka suke gwanin ban sha'awa da burgewa. Bari in yi tambaya! Shin ya barrack na kasarku take? Wani tsari aka yi wa sojojinku dan suma su ji daɗi kamar kowani ɗan kasa? Wani irin yanayi ake barinsu a ciki? Suda suka sadaukar da rayukansu saboda kare ƙasa, al'umma da dukiyansu, wani irin sakayya ake yi masu?. ALLAH YA TSARE MANA KU SOJOJINMU YA INGANTA AIKIN NAN NAKU!.
------------------------🔥
Yau takama Monday, dubbannin sojoji ne suke shawagi a ko'ina, tamkar za'ayi yaƙin duniya ta uku, sai kai komo suke yi, kowanne ka ɗaga ido ka kalla ba zaka sake sha'awar kallonsa ba, dan sai hantar cikinka ta kaɗa, idanunsu jajir kamar wuta, sai wasu muzurai suke yi, ga jiga-jigan makamai rirrike a hannayensu.
A gefe guda kuma ga matasan sojojin da aka ɗauka cikin satin nan dan horarwa, kowani matashi yana shirye cikin kayansa masu balain kyau, dik sabbin matasan da suka zo suna tsaitsai ne a cikin tsakiyar assembly hall ɗinsu, kowani matashi ka ɗaga idanu ka kallah zaka gansa cike da tsantsar muradinsa na son wanna aiki game da kwarin gwiwa, dayawansu suna tsaye ne da abokansu, wasu zaka gansu group uku, wasu su huɗu a wajen, wasu ma su biyu, sai hira suke yi, kuma dikkansu suna sanye da p-cap na sojoji a kansu, kowa jinsa yake yi a sama yau, suna jin tamkar sun zama sojoji, dan dik wanda yake wajen burinsa kenan.
TO ALLAH yasa kuna da rabon haye atisaye ku zama sojojin da kuke fata, kuma ALLAH yasa aikin ya zame maku alkhairi har ku yi alfahari da shi!.
Lokaci guda dikkan sojojin hankalinsu ya tattare izuwa kan hanyar shigowa hall ɗin sakamakon karar sautin tsaro da suka ji yana tashi alamar an dinfaro hall ɗin. Kan ka ce me kuma sun jera line by line tamkar assembly a primary school, sai dai tsayuwarsu cikin jarumta da karfafa kai ne.
Wani kyakkyawan matashi fari tas da ba zai wuci 33 years haka bane ya shigo cikin hall ɗin, sanye yake cikin kakinsa, kana ganinsa kaga jarumi dakakken namiji, fuskansa babu annuri babu alamar wasa, kai tsaye kan stage dake hall ɗin ya nufa cikin takun dake nuna lallai jininsa a tafashe yake. Yana hawa ya furta attention babu wasa yana kara haɗe rai. Da karfi suka buga kafa ɗaya a ƙasa game da sara mashi, wannan ma yana daga cikin dokokin GIDAN SOJA da suka karanta kafin su zo nan.
CAPTAIN ONBISH CO shi ne sunan dake a gaban uniform ɗinsa.
Captain kallonsu ya fara yi one by one yana karawa kamar yana karantar wani abin a tattare da su kuma kamar yana karantar yanayinsu. A daidai wannan lokacin commander ya shigo, shi ma cikin jarumta da nuna kwarin jiki, amma shi zai iya kai 43 to 45 years haka. A saman stage ɗin shi ma ya zo ya tsaya yana kallon yadda matasan sojojin nan suke a tsaitsaye cikin ƙamewa, ya ji daɗi har cikin ransa, dan tin daga kan yanayin tsayuwarsu ya fahimci suna da zumman cinwa abin da suka sa a gaba. Hall ɗin nan gabaɗaya kewaye yake jiga-jigan sojoji jaruman gaske.
Captain ne ya ɗaga hannu ya sarawa Commander cikin girmamawa da kwarewa a aiki. Sara mashi Commander ma ya yi kafin ya juya ya fuskanci matasan nan, a take suma suka ɗaga hannu suka sara mashi, jinjina masu kai ya yi kafin cikin kakkaifar harshe ya ce. "Attention!". Kafa ɗaya suka sake bugawa a kasa da karfi tare da kara kamewa kam!.
"1, 2, 3 start". Commander ya sake faɗa cikin ɗaga muryar!.
Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA da suke yi a kowacce safiya kamar haka...... "We march through fire, through storm and rain, With steel in heart, we bear the pain. For land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, Through darkest nights, til battle's won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 95