an dawo da darling ne.
A can kuwa, sister Lazy ta kawo drugs ɗin, har ƙasa ta tsugunna ta miƙo mashi, karɓa ya yi tare fitarwa ya duba. Ganin wanda ya buƙata ne ya ce mata. "You can go". Ya faɗa yana miƙewa, ya nufi gaban sofar da Zinta take bayan ya ɗauko mata robar ruwa daga freezer ɗinsa.
Tamkar sister Lazy zata haɗiyi zuciya ta mutu tsabar taƙaici, tana gani sai faman cewa Zinta sorry yake yi, yanzu ya kara sakar mata zuciyansa, tin da ya yi wasa da jikinta, ya ji ɗuminta, ya ji sa a duniyar Jupiter, daga nan ya sake narke mata.
Da kansa ya ɓalle drugs ɗin, sannan ya ɗagota ya zaunar, ya sanya mata drugs ɗin a baki, ya ɓalle bakin robar ruwan, ya bata. Tana ɗan shagwaɓe fuska ta karɓa, sai ce mata sorry yake yi. Bayan ta sha ya rufe ruwan, sai ya ce ta kwanta ta yi barci sai zuwa yamma, yau ba zata yi aikin komai ba. Sai da ya tabbatar ya kwantar da ita, sannan ya miƙe zai koma chair ɗinsa kenan sanyayyar muryarta ta katse shi da cewa.
"My oga, please our darling, jiya har mafarkinsa na yi, na yi mafarkin yana ta kuka yana son shan madara, please ka kaini wajensa ka ji?". Idanunta na ciccikowa da kwallah ta faɗa. Bata san darling yana can cikin mawuyacin hali ba, yana faɗa tsakanin rayuwa ko mutuwa, ALLAH ne kaɗai yasan kalar azaban da bawan ALLAHN nan yake ciki, cutar ta huda jikinsa sosai, wani lokaci har bleeding hancinsa yake yi, sun sanya shi cikin wani glass transparent haka, wanda suna iya ganinsa, ta nan suke bashi madara, dik wannan rikici nasa da kukan ya daina, ko motsin kirki baya yi, a iya kwana ɗaya kawai fa kenan.
Ya ALLAH me kuke tinani zai faru bayan kwanaki 5! Ya kuke tinanin wannan cuta zata yi wa al'ummar duniya? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun........ Ayi hakuri da abin da zan rubuta daga yanzu har gaba, ta yiwu yai maku daɗi ko akasin haka, amma dole zan rubuta! Dan labari ne kan halin da duniya take ciki! Burina in wayarwa da mutane kai, in farkar da kowa yasan halin da ake ciki, dan haka ku yi hakuri da abin da zaku ji kuma zaku ga na rubuta, nasan akwai tashin hankali da jefa zuƙata cikin damuwa har ma da kuka, saboda waɗan nan jarirai, jaririn da bai san komai ba, dole nasan hankula zasu tashi, amma ba yadda zan yi ne! Dole ku san me ake ciki, ku daure ku cigaba da karatu, zaku ci ribar karatun ko ba'a kanku ba, ko a kan ƴan uwa, kunga yanzu idan kun ji za'a cirewa wata mahaifa ai ko shawara ce zaku bata, idan yazamana dole za'a cire mata sai ku ce mata in an cire ta ɗauke kayanta ta koma da shi gida ta je ta binne. Wlh tashin hankalin dake cikin wannan duniya ta zarce bakin ɗan adam ya zayyano shi, wani fitinan idan kuka ji sai ku zaci ba gaskiya bane! Amma wlh abin da ya fi ɓarnar da su 3D suke yi yana iya faruwa a duniyar yau, fatanmu dai ALLAH ya karemu daga dikkan azzaluman nan, ya kawo mana karshen zalunci, ya bamu kwanciyar hankali da zaman lafiya, daga karshe ya bamu dacewa da lahira game da cikawa ta hanyar shahada.
Jikin mace gabaɗaya kadara ce, mu mata muna ganin rayuwa a yanzu, tin da aka gano jikinmu kadarori ne shikenan, kowacce ta dage da addu'a, babu abin da ya fi karfin ALLAH, idan kika riki ALLAH dole a ganki a barki....... Magana ta karshe kuma shi ne ƙasar AVARIS ƙasa ce ta kirkira, babu ƙasar a zahiri, na kirkiri ƙasar ce saboda bana son in ɗaurawa wata ƙasa wani abin da ba shi ba, kunga yanzu ƙasa ta ce Avaris, dik ɓarnar da na ɗaura mata babu wani shugaban da ya isa ya fito ya ce na ɗaurawa ƙasarsa wani abin, sannan a bisa dokar ƙasa kuskure ne ka ɗaurawa wata ƙasa irin wannan abin kai tsaye, shiyasa na kirkiri tawa ƙasar, dan haka Avaris ƙasar kirkirace! Fatan kun gane kun kuma ɗauki haske?.
"My oga, please our darling, jiya har mafarkinsa na yi, na yi mafarkin yana ta kuka yana son shan madara, please ka kaini wajensa ka ji?"..... Jinjina mata kai ya ɗan yi. "Ki yi barci zuwa dare zan kaiki". Ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce ya koma wajen chair ɗinsa, lumshe idanunta ta yi, tana jin ciwon cikin na raguwa, har barci yai awon gaba da ita. Ita kuwa sister Maya tana can tana fama da jijjiga wani baby da yaki yin shiru, amma zuciyarta na can wajen tinanin Dr Kamal da abin da yai mata ɗazun, yadda ya jawota jikinsa, ya ALLAH, abin ya tsaya mata a zuciya, sai take jin tamkar ta sake komawa wajensa, dan bata gaji da kallonsa ba.
Wasa-wasa sonsa na shiga zuciyarta, watau 3D tantirai ne, sun iya sanyawa mutum soyayyarsu a rai cikin ƙanƙanin lokacin. A haka suka wuni yau, sister Maya ta yi ta fama da babys ɗin, hankalinta ya rabu kashi uku, tana fama da babys, tana tinanin Dr Kamal, tana kuma tinanin sister Zinta dake fama da ciwon ciki, bata san a wani hali take ciki ba, ta damu sosai tana son sani, ga shi ba damar ta je 3D side idan ba su suka nemeta ba.
Haka ya wuni sukuku, ta ɗauki wannan baby ta dire ta sake ɗaukar wani, kewan darling tamkar ya kasheta, har yamma around 5 daidai 3D suka sake dawowa dan duba lafiyar yaran, kun san basa amfani da ɓargon yaron da ya raunata ko bashi da lafiya, lafiyayyun yara suke amfani da su, shiyasa kuka ga suke yawan zuwa duba lafiyarsu, sau uku a rana suke zuwa dubasu, ko ɗan zazzaɓi yaro ya yi a take zasu ɗauki mataki, basa wasa da lafiyar jariran, dan su samu sinadaran da suke so kada su yi asara.
Kewaye suka dinga yi a cikin yaran, suka auna kowanne, suka tabbatar da suna lafiya, sannan suka nufi waje. Zasu fita ne Dr Kamal ya tsaya, sai ya dawo ciki, a kusa da ita ya tsaya, can ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "Akwai aikin da zamu yi yanzu, zuwa dare zan ganki". Ba tare da ya jira amsarta ba, ya juya ya bi bayansu Dr James.
Suna fita kai tsaye SECTION E suka nufa, zasu fara sarrafa ɓargon ƙashi da sinadaran jariran can dan yin magungunar da suke da buƙata. A tinaninku me dame suke yi da ɓargo da jinin jaririn? Magungunar me dame suke haɗawa? Wasu sinadaran suke haɗawa? Ina suke kai magungunan? Shin suna fitar da maganin ne ko kuwa ya suke yi da shi?. Alƙalamina zai warware maku komai tsab, ba zan rage komai ba, mu je zuwa.
3D na fita sai ga sister Zinta ta shigo babys safe room ɗin. BABIES SAFE ROOM (BSR) na taƙaita maku dan rage wahalar ƙira, ku ce BSR kawai.
Ta warke garau, ta sha barci a office na Dr James har ta gode ALLAH, dama jiya bata samu damar yin wani barcin kirki ba, saboda murzanta da ya dinga yi, yau dai ta more, sai yanzu da zai fita ya tada ita, ya ce ta je ta yi wanka zata wastsake. Kafin ta fito wanka ta samu haɗaɗɗen mandi rice ya ajiye mata a wajen sofar da ta tashi, ga crispy chicken da lemun abarba mai mugun sanyi, ta yi mamakin ganin irin abinci, bata taɓa cin irinsa ba, ai ce mashi ta yi zata je ta ci da sister Maya, bai hanata ba, dan bashi da matsala da ƙawancensu, sai ya ce mata ta kula da kanta, anjuma zai zo ya ɗauketa su kwana a ɗakinsa.
Tana murmushi ta ce okey. Zata ɗauki kayan abinci ta ji an rungumota ta baya, ajiyar zuciya ta sauke tare da juyowa a hankali, ta faɗa jikinsa. Shafa lallausan gashin kanta ya fara yi izuwa gadon bayanta, ya ɗan sumbaci cheek ɗinta kafin ya saketa, ta ɗauki kayan abincin, ta nufi kofa tana waigosa, yana tsaye ya rungumo hannaye a kirji yana kallonta, har zata fita ta sake waigosa, da alama ita ma bata son rabuwa da shi.
Kashe mata ido ɗaya ya yi, hakan yasa ta fice tana murmushi......... Sister Maya na ganinta ta miƙe ta rungumeta tana tambayar lafiyarta. Tana murmushi ta fara bata labarin abin da ya faru bayan sun zauna a gefen gado, sosai Maya ta ji daɗi, sannan ta karɓi kayan abincin ta fito da shi.
Suka zuba a plate, sauran kuma suka baiwa sauran nurses dake faman baiwa babys madarar yamma. Sosai suka ci abincin, sai santi suke yi, haƙiƙa sun yabawa girkin, basu taɓa cin abu mai daɗinsa ba, har da lashe plate sister Maya ta yi, bai isheta ba, amma already sun baiwa sauran nurses sauran abincin, da zata ƙara.
Lemun abarba dake cikin botle suka ɗauko, haba daɗinsa da sanyinsa da ya ratsa masu wuya sister Maya har da rufe idanu, ta dinga santi sister Zinta na yi mata dariya, basu baiwa sauran nurses wannan lemun ba, dan ƙaramin bottle ɗaya ne daidai shan mutum ɗaya, dan haka suka shanye tas, kafin sister Maya ta tattare komai, kunsan malaman asibiti da tsabta, ta tsabtace ko'ina tsab kafin ta dawo suka zauna da sister Zinta a kan gado suna hira, sun bar crispy chicken ɗinsu, dan cikinsu kamar zai fashe saboda ƙoshi, sun sha bottle water, sai sister Maya ta ce su bar shi sai anjuma su ci, na'am da hakan suka yi.
Sister Maya ta bata labarin abin da Dr Kamal ya ce mata, sosai sister Zinta ta tayata murna, suka hau tsara yadda zasu kula da 3D har su samu soyayyarsu sosai!.
----------------------------🔥
CRYSTAL PALACE.
Da wani irin gudu ya shararo da motarsa kan titin dake cikin school ɗin izuwa parking lot, tin daga nesa ya hango Seraphina, Rimsha and Faryan suna tsaye suna magana, Seraphina ta ce ita ba zata shiga motarsu ba yau, bata jin daɗi, ta tsani ma ai mata mata magana, shi kuwa Faryan, lover boy, sai rarrashinta yake yi, ta kafe ita da kafa zata tafi, kuma karya take yi, yarinya har ta fara koyan karya.
Uncle ne ya hure mata kunne, ya ce idan an tashi ta jira da kansa zai kaita gida, ya kasheta da kalaman kauna game da gift na chocolate har da heart design na pillow mai kyau da aka rubuta i love you blossom, ta sanya kyautar a cikin school back ɗinta, shi ne yake cewa da kafa zata tafi, da karfi da ya ji tana son koyar wasu ɗabi'u da ba nata ba.
Ai tin Aryan bai gama karisawa wajensu ba ya ɗauko wani face ya sanya a fuskansa, face ɗin da Seraphina ta fara saninsa da shi, dama suna da shi a cikin motocinsu saboda gudun ko ta kwana. Winter jacket ya ɗauko, ya sanya a saman kayansa tare da kashe motar ya fito.
Gabaɗaya kishi ta rufe mashi ido, ya manta Faryan ƙaninsa ne, yana zuwa ya damke mashi da karfi, yana son tambayarsa me ya haɗa shi da ita, amma yasan in dai ya yi magana sai Faryan ya gane, dan haka ya yi shiru bai yi magana ba.
Ƙoƙarin kwace kansa Faryan ya yi, amma ya gagara, dan damkar IRON FIST ba wasa ba, abu kuma ya haɗu da kishi, ai ba'a magana. Ihu Seraphina da Rimsha suka kurma a tare, hakan ya yi silar dawowansa hayyacinsa, da sauri ya saki Faryan, idanunsa sun yi jajir, Seraphina har ta fara ruwan hawaye, muryanta na rawa ta ce. "Daddy please ka kyalesa"...... Da yake ta ganesa tin da fuskan ta fara saninsa.
Wani irin damƙa yai wa hannunta, da karfi yaja sai wajen motarsa, ya buɗe marfin ya jefata ciki, bai sake bi ta kan kowa ba ya shiga gidan gaba, yana ganin Rimsha ta zo da gudu ta rike Faryan tana bashi hakuri. Tada motarsa ya yi, da gudun gaske ya bar school ɗin.
Ni kam na ce ALLAH ya taƙaita basu haɗu da uncle bama, da abin zata fi munana!.
Tana kuka jikinta na kerma, wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata, da karfi ya ce. "Will you shut up! I'm coming for you, bari mu koma gida, sai kin faɗa mun wanda ya baki izinin kula Faryan!".
Cak ta tsaya da kukan, ta tsai da idanunta a kansa, mamaki ne yakamata na yadda aka yi yasan sunan uncle Faryan ɗin Rimsha, to ai ita bata faɗa mashi ba, hasalima tin da ta haɗu da Faryan basu zauna sun yi hira ba, ko a ina ya san sunansa? Ta jefi kanta da tambayar da babu mai amsa mata, ya ALLAH watau jinin IRON FIST akwai barain, har ta gano ya kira sunan Faryan dik da damuwar da take ciki.
Ai yana parking a garage ɗinsu ta ɓalle door na motar, da gudu ta fita, kafin ya fito ta haye elevator zuwa hawansu, dole ya tsaya jiran elevator ɗin ya dawo ya ɗaukesa. Tana shiga parlonsu ta gudu bayan Madam ta ɓuya, tana kuka ta ce. "Mom kada ki bar daddy ya dakeni, na shiga ukuna".
Madam na ƙoƙarin yin magana sai ga shi ya shigo, har lokacin huci yake yi tamkar zai kama da wuta. A tsakiyar parlon ya tsaya, babu wasa tattare da kan fuskansa ya ce. "Come here!".
Jikinta na kerma sosai, hawaye sun gama wanke fuskarta, ta ƙanƙame Madam tana faɗin. "Mom please help me, don't let him go in with me"...... Madam ta gagara yin magana, dan ita kanta tsoron Aryan take ji, yana cikin kwanciyar hankali ma tsoro yake bata bare ace yana cikin fushi.
Daidai lokacin Aunty Safiyya da Suhana suka fito jin hayaniya a parlon. Ganin abin dake faruwa yasa suka yi saurin ƙarisowa........ Ran Aryan ya ƙara ɓaci, a fusace ya tako ya nufosu tamkar wani mayunwacin zaki. Ai yana ganin ya nufosu kuma Madam bata ce komai ba, sai ta saki Madam, da gudu ta diro ƙasa, tana ƙoƙarin watsawa da gudu ya damƙo gashin kan nan nata.
Sama ya ɗagata sai saman shoulder ɗinsa, su Aunty Safiyya sai kallonsu suke yi. Bai direta a ko'ina ba sai cikin room ɗinta, a tsakiya ya direta tare da fara ƙoƙarin yi mata magana.
Haba ganin bata da mafita ne, babu mai iya kwatarta a hannunsa ne yasa ta tuna abin da ta karanta a littafan can, yadda ake controlling fushin namiji, dan haka dole ta yi amfani da wannan dabara, dan wlh tana balain tsoron dukan Aryan, ta ji kamshin lahira ranar, bata son ko a mafarki ta ƙara jin even one slap from him.
Da sauri ta datse idanu, ta faɗo jikinsa, hot hug ta bashi game da saka mashi kukan shagwaɓa, tana goggoga kanta a saman lion chest ɗinsa..... Jimmmmm haka ya ji duniya ta tsaya mashi, omg, this kukan shagwaɓa melted his heart over, ga goga kanta a kirjinsa da take yi, ga shi she hugged him tightly, ai ɗauke wuta ya yi, zuciyansa na wani irin spark na shauƙin ƙaunarta....... 👀
Cikin kukan shagwaɓa ta ce. "I'm so so sorryyyyyyyyyy daddy, ba zan sake ba, for give me my gentle chaos"...... Oh God, this gal ta gama da daddy yau, wannan suna da ta kirasa my gentle chaos ya gama narka mashi fushin da ya ɗebo, fushin ya narke ya koma so da kaunarta sabo!. Bai san time da ya rungumeta tightly ba, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fushi ta gudu.
Da jin ya rungumeta ba karamar daɗi ta ji ba, ta ƙara shigewa jikinsa sosai. Shiru suka yi, shessheƙar kukan shagwaɓarta na tashi a hankali-hankali, yasa hannu yana ɗan shafa kanta izuwa kan bayanta. Gabaɗaya ya shige love mood, har ya manta cewa Campaion na IRON FIST yake!.
Sun ɗauki 10 mins a haka, slowly ya saketa, ya raba jikinsu, saman sofa ya koma ya zauna, ya jingina kansa shiru tamkar mai tinanin wani abin, ya ɗan lumshe idanunsa soyayyarta na kara ratsa shi sosai. Ganin haka yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da zuwa ta zauna a kusa da shi saman bed, tana kallon kyakkyawan face ɗinsa.
Ni kam na ce daddy fa ya yi mugun nisa a soyayyar Cherry bloom ɗin nan nasa, sai abin da muka gani, yanzu ita ke rike da ragamar zuciyansa, amma yarinta yasa ba zata gane cewa zata iya juya shi ba, ko Abba ba zai iya juya shi cikin sauƙi ba, amma ita zata iya a sauƙaƙe cikin kwanciyar hankali ma kuwa, amma ba zata gane hakan ba. To me kuke tinanin zai biyo baya? Ga su dai zaune shiru Cherry ta zuba mashi ido, idan ya wastsake ya dawo daga duniyar da ta jefasa me kuke tinani zai faru? Ƴar yarinya da ita tana son fin karfinmu, tasan komai, to thank God dai da bata fara aikata komai ɗin ba daddy ya farga!.
Tin da sun zauna shiru bari mu leƙa wani ɓangare, watakila kafin mu dawo shi ma daddy ya dawo daidai ya wastsake.
--------------------------
Zaune Abba yake a main parlo, yana rike da littafin The Franklin Scandal yana karantawa, hannunsa rike da gold scepter ɗinsa, ya miƙe kafafunsa saman lallausan throw pillow ɗin dake a gabansa, hankalinsa ya karkata kan littafin.
Cikin natsuwa Ammie ta sauƙo ƙasa, tana tafiya tana wuwwurga idanu in da zata gano Rimsha ya jikin Abba, dan tasan lokacin dawowarta daga school ya yi. A gefen Abba ta zauna tare da cewa. "Barka da hutawa ranka ya dade".
Abba gwani a izza da isa, kai tattijon nan akwai taƙama da nuna karfin iko game da fadanci, anya Abba ba jinin sarauta bane ba kuwa?....... Sai da ya ɗauki mintuna kafin ya rufe littafin hannunsa, a natse ya ce da Ammie. "Yauwa sannu da fitowa".
"Ban ga Rimsha ba". Ammie ta faɗa tana miƙa hannu ta karɓi sandar hannunsa, ta kwantar a ƙasa...... "Basu shigo ba ai".... Shiru Ammie ta ɗan yi, can kuma ta ce. "Nasan dik abin da ka yanke abu ne mai kyau, baka yanke abin da bai dace ba, kuma dik abin da ka yanke muna biyayya da kuma mubaya'a a garesa, amma a wannan karon ina neman alfarma dan ALLAH! ALLAH ya kara maka nisan kwana da lafiya".
Bai amsa ba, ya dai zuba mata idanu yana kallonta, tasan halinsa sarai, shirunsa ma magana ce, dan haka sai ta cigaba da cewa. "Dan ALLAH ka bar batun haɗa wannan aure na su Aryan da waɗan can yaran.....". Gagara karisawa ta yi saboda ɗan waro idanunsa a kanta da ya yi, mamaki ne ya kamasa jin yau karo na farko a gidansa ya yanke hukunci ake neman yi mashi katsalandan, abin da ba'a taɓa yi ba kenan.
"ALLAH ya baka hakuri, tuba nike". Ammie mace mai biyayya ta faɗa, sam ita bata son ai wa ɗanta auren dolen nan ne, dan ya ce mata baya so, sun yi waya jiya, ya faɗa mata muddin Abba yai wannan aure to ta sani kome ya biyo baya su suka ja, shi ya gama magana, baya son auren kuma ba zai yi ba! Idan aka matsa mashi ran kowa ba zai yi daɗi bane.
Ammie tasan waye Aryan fiye da yadda Abba ya sanshi, tasan baya magana biyu, lallai dik wacce aka aura mashi sai ta gwammaci da bata zo duniya bama, dan billahil lazi mancewa da cewa ita macece zai yi, dama can maza suke yi wa kallon mata, aikuwa yarinya zata ji a jikinta ne!.
Nisawa Abba ya yi, zai yi magana kenan sai suka ji ana knocking na parlo door ɗinsu. Wayansa dake gefensa Abba ya ɗauko, app na door ɗin ya shiga, akwai camera a jikin kofar ta baya, so idan kuka shiga cikin app ɗin zaku iya shiga Camera ku ga wanene yake knocking kuna daga zaune!...... Uhm duniya ta cigaba, ALLAH ka wadatamu da ire-iren waɗan nan cigaban a ƙasarmu.
Yana dubawa ya ga Aunty Luna tsaye a bakin door. Ai da sauri ya danna door control, options suka bayyana, sannan ya danna open. Take dik wasu locks na kofar ta buɗe, ta ɗan motsa ta buɗe kaɗan. Turowa Aunty Luna ta yi ta shigo. Tana shirye cikin shiga ta alfarma, tana shirye cikin black jean, white top and winter jacket wanda ya zo mata har gwiwa a saman kayan, ta yi matuƙar kyau sosai, tana da natsuwa da hankali.
Gaban Abba ta kariso, har ƙasa da durkutsa ta gaida shi cikin girmamawa, sannan ta ɗagawa Ammie ma gaisuwa. Dik da cewa Abba baya dariya, kai face ɗinsa ba zaku taɓa zatan yasan me murmushi ba, amma har cikin ransa ya ji matuƙar daɗin ganin Aunty Luna, a mutunce ya amsa gaisuwarta tare da ce mata ta zauna, ya nuna mata ƙasa saman carpet, dan shi Abba akwai izzar balai, idan yana saman kujera ba'a zama a sama kai tsaye.
Zama ta yi. Shiru ne ya ɗan biyo baya, sai kuma can ta ce. "Dama na zo ne in baka hakuri kan abin da ya faru, daddyna ma ya ce in baka hakuri, abin bai yi mana daɗi ba, bamu ji daɗin abin da grandpa ya yi ba"......... Still dai fuskan Abba babu fara'a ya amsa da. "Kada ki damu surukata, in kin je gida ki sanar da daddyn naki gobe da kaina ina kawo mashi sadaki".
Murmushi ne ya kubce mata, dan ita dai har ga ALLAH tana matuƙar son Harleen, tin da ta kyalla idanu ta ga haɗuwarsa, gabaɗaya ta rasa kanta, kai jinin Abba ba dai haɗuwa ba, ga iya ɗaukar wanka, kai Masha ALLAH kawai zamu ce.
Ta ɗan yi ƙasa da kai bata ce komai ba, ganin haka yasa Abba ya ce mata. "Ki je sama Harleen yana ɗakinsa, ku gaisa kafin ki koma ko?". Tamkar Abba yasan abin dake ranta, tana son ganinsa ne dama, amma ta rasa yadda zata faɗawa Abba, bata san meyasa dik rashin kunya irin nasu na European amma take matukar shakkar Abba, yai mata mugun kwarjini, ganin cikin idanunsa wannan ta gagara yi, to haka Aryan yake, wlh ba kowa yake iya ganin cikin idanunsa ba, bare Lion da Vir, kai IRIN FIST dikka zaku zaci jinin Abba ne su ɗin, akwai su da balain kwarjini, cika ido, sanyawa mutum zarra, izza, isa da taƙama, yadda kuka ga Abba da karfin halin aurar da yara ko ubansu bai so ba, haka IRON FIST suke da shegen nuna iko a koma inane!.
Miƙewa ta yi, ba kunya ta dinga zubawa Abba godiya, sai ta nufi sama. Ammie kam ta saki ido tana kallonsu, watau Ammie bata waye sosai bane, da sauran hijabin kunyarta in faɗa maku, amma Abba, ba dan wani abin ba, ba dan ina tsoron daddy Champion ba, da na ce Abba taƙadarin ɗan duniya ne! Amma ina tsoron Aryan, na yi shiru!.
Har ta haye sai kuma ta tsaya game da juyowa, bata iya kallon face ɗin Abba kai tsaye ba, tana facing Ammie ta ce. "Daddy ina ne room ɗinsa?"...... Abba dake kallonta ne ya amsa da. "Abba zaki kirani, room ɗinsa na side two daga parlon sama"...... Da okey ta amsa game da cewa thank you Abba tana murmusawan dake kara fito da kyanta.
Ta juya ta karisa cikin second parlo. Kai tsaye ta nufi room ɗinsa. Yana kwance saman bed, daga shi sai shorts and singlet, hannunsa rike da waya yana dannawa, ya rungumo pillow a kirji, while ya ɗaura kafafunsa a kan wasu pillows ɗin, da alama yana jin daɗin yanayin da yake a ciki.
A natse ta turo kofar ta shigo, sarai ya ji an turo kofa, amma ya zaci Faryan ne sai bai ɗago kai ba, dan yasan kofar ɗakinsu ai sai su kaɗai zasu iya buɗewa, dan haka bai zaci wata ce daga waje ba. Ita kuwa Abba ne ya buɗe mata kofar daga in da yake zaune a parlo, tin kan ta karisa ya danna open na side two doors, tana zuwa ta ga kofar a ɗan ture.
Karisowa ciki ta yi, ko kaɗan bai ɗaga ido ba, abin da ya kara burgeta da shi kenan, wannan miskilanci da izzar tasu! Ga ɗan banzan girman kai wai sun fi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 62 Chapter of 95