Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wata mace ta raɓesa har ya haɗa jiki da ita ba, lallai Seraphina ta wuci tinaninsa, miƙewa zaune ya yi, sai ya canza topic na hirar kafin ta jefa mashi wata maganar ta juya mashi ƙwaƙwalwa. Ƙarisa hayewa saman gadon ya yi tare da kwanciya da kyau, ya jawo pillow ya ɗaura a kan kirjinsa, yana binta da wani irin narkakken kallo mai narka zuciya ya ce. "Ina jin kamar ke na rumgume ba pillow ba, zan yi barci kada ki tasheni". Wani haɗaɗɗen murmushi ta saki wanda ya fito da dimple ɗinta sosai, har wushiryar dake tsakanin fararen hakwaranta tas ya bayyana. "Daddy kana feeling love a kaina kamar yadda nike ji a kanka dama?"....... Kai ya jinjina mata alamar. Da sauri ta dawo kusa da shi, ta haɗe hannayenta ta kama kumatunta, cikin shagwaɓa ta ce. "Daddy, let feel our love". "Sure?"...... Kai ta jinjina. "Let feel it daddy"....... Ɗan nisawa ya yi tare da ƙara ƙanƙame pillow ɗin a kirjinsa, kamar mai raɗa ya ce. "Give me some love words that will make my sleep more nice, idan na tashi zamu cigaba da hira, now I'm feeling sleeping, jiya ban yi barcin dare sosai ba". Kai ta jinjina tare da matsar da face ɗinta dab shi........ "Love you more my gentle chaos, a dik lokacin da ka ji kamar kana kaɗaici, remember that you have a beautiful wife, sister, baby, Cherry, beside you, ina tare da kai to make your smile more beauty, make your heart more peaceful, make your body more........". Fasa ƙarisawa ta yi, saboda tai mashi alƙawarin ba zata sake yin maganar da bata dace ba. To Tin da ta fara magana ya tsare ɗan bakinta da kallo, zuciyansa na ingiza shi da ya yi kissing ɗinta kawai, ya rabb, shi kaɗai yasan me yake ji a kanta, kome take yi ƙara kyau take yi, kome ta yi burge zuciyansa take yi, shirmenta abin so ne a garesa, kalamanta abin so ne a garesa, soyayyarta ya zame mashi jinin jiki. Matsawa ta yi ta ɗan sumbaci cheek ɗinsa tana faɗin. "Sleep well, make sure that i come into your dreams as your wife, ina kwance a saman kirjinka ina......". Still kame bakinta ta yi, ta fasa ƙarisa maganar. Slowly ya lumshe idanunsa yana jin wani irin daɗi a ransa, lallai Seraphina ta fara natsuwa, sau uku kenan yanzu tana kame bakinta taki ƙarisa magana saboda ya hanata, kai lallai ya ji daɗi sosai yau. Ganin ya lumshe idanu ne yasa ta tsaresa da kallo tana jin sabon sonsa yana shigarta. After like 5 mins slowly ya waro idanunsa kai tsaye a kan face ɗinta, in a sleeping voice ya ce. "Stop looking at me Cherry". One side smilling ta saki kafin ta ce. "Daddy ni da fuskan mijina zaka ce in daina kallonka?". Tana turo baki ta kai karshe. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a kan shafaffen cikinsa dake da guraye saboda gym da yake yi, in a sleeping voice ya sake cewa. "My cherry, I'm feeling hungry sosai, ban yi breakfast ba, dinner ɗin jiya ma ban ci ba". Yana magana yana lumshe idanunsa, watau sai da ya zo wajenta ya samu natsuwar iya gane ashe yana jin yunwa. Da sauri ta ɗaura hannunta a saman cikin nasa, daidai in da hannunsa yake, sai ta ce. "Daddy tashi in yi feeding ɗinka, bari in je in haɗa maka abinci a kitchen". Ta faɗa tare da yunkurawa zata miƙe, da alamar tausaya mashi sosai a kan fuskanta. Slowly ya riko hannunta cikin nasa, ɗan jawota ya yi, sai ta tafi gabaɗaya ta faɗo kansa, fuskokinsu yana saitin na juna, in a low way sosai ya ce. "Let me sleep first, idan na farka sai ki bani abincin a baki kin ji?". Kai ta jinjina alamar to ta gagara yin magana, saboda yadda ta kalli kwayar idanunsa dab ita ya rikita zuciyarta. Slowly ya saketa game da lumshe idanunsa, kafin wani ɗan lokaci ya yi barcin gaske mai daɗin da ya jima bai yi irinsa ba. Shiru ta zauna tana ta faman kallonsa, bata son matsawa daga kusa da shi ko kaɗan, tana ganin kamar rabasu za'ayi idan ta matsa, har da kwanciyar ruf da ciki, ta ɗaura kanta a saman kirjinsa, tana kallon face ɗinsa, a hankali barci ya ɗauketa ita ma. CRYSTAL PALACE, idan na kira sunan CRYSTAL PALACE a yayin da muke cikin CRYSTAL PALACE ɗin muna labari to ina nufin zuciyar CRYSTAL PALACE gabaɗaya ne, watau gidan MUHAMMAD HAIZA'AN, gidansa ne zuciyar CRYSTAL PALACE, gidan da ya fita daban a tsarin ginin cikin CRYSTAL PALACE ɗin, gidan da aka ware a waje daban, yana gefe can, wani shinfiɗaɗɗen titi da aka shinfiɗa wanda ya miƙe har cikin gidan kawai abin kallo ne, kun san dukiya tai kuka ba kaɗan ba, ya rabb, tin daga farkon titin nan jiga-jigan jami'an SSO ne suke shawagi, ko tsuntsuwa basa bari ta gifta ta sararin samaniyar gidan Haiza'an, lallai na shaida dik wani karfin iko ya kare a wannan waje. Zaku rantse da ALLAH dik jami'an dake US aka zuba a wannan gidan, wasu irin guards waɗan da ko fuskansu baka iya gani face idanunsu dake rikitar da zuciyar bawa su ke gadin gidan, ya kuke tinanin san da yake raye kenan? Wai a haka ya rasu ne wannan karfin ikon! Ya ALLAH. To mu yi tattaki zuwa cikin gidan dan mu ga meke going a ciki, ya tsarin gidan yake tin da na ce ya fita daban da tsarin sauran gine-ginen dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Jama'a ban taɓa tinanin za'a samu gidan da zai fi Black Tiger empire haɗuwa ba, sai ga CRYSTAL PALACE da kanta, ga kuma uwa uba zuciyar CRYSTAL PALACE watau gidan Haiza'an, ya ALLAH kai mana arziki mai albarka kawai. Siffar ginin gidan ya kasance irin ginin mediterranean ɗin nan ne ta gefe-gefe, daga ta gaban gidan kuwa zallar glass ne, girman gidan ya fi fili flot 20, saɓanin benayen CRYSTAL PALACE shi wannan gida yana da gate, an kewayesa ne, sai kun wuci gate uku manya-manyan masu cike da tsaro na ban mamaki kafin ku ƙarisa cikin gidan, sannan shi wannan hawa uku ne kawai. A gefe guda harabar gidan ga tampatsetsen lambu mai ɗauke da ƙananan arche, ƙananan ƙoramu ne da aka yi su dan ƙawata lambun, ga wasu irin fitillu da aka ƙawata lambun wanda ko dare ne zaku zaci rana ne saboda haskensu da ƙawarsu, uwa uba lambun da glass wall aka kewayesa, daga waje kana iya hango haɗuwarsa ta ciki, ya ALLAH, ga wasu kifaye orange and red da aka zuba cikin tampatsetsen glass suna ta yawo cikin ruwa, shi ma ya ƙara ƙawata lambun matuƙa, ga wasu flowers masu mugun kyau da ɗaukar hankali, a bakin kofar lambun daga gefe an yi wasu flower da aka shukasu aka yi siffar sunan HAIZA'AN'S GARDEN da su, jama'a wlh lambun nan ya haɗu fiye da yadda kuke hasashensa a ranku, kuɗin da aka narƙa a wannan waje, kai kuɗin mahaikatan dake gyran lambum nan kawai jarin wani ɗan siyasa ne a Avaris!. A budget ake cire kuɗin masu aikin gyaran gidan Haiza'an, a shekara ake lissafi a cire kuɗin masu gyaran gidan, akwai mata akwai maza, kowa da aikinsa, kullum na ALLAH sai sun share ko'ina sun gyara tamkar yana raye............ Jama'a baku tunanin bayan mutuwar daddy Haiza'an akwai abin da ya faru kuwa?. A tsakiyar tampatsetsen harabar gidan akwai wani waterfall wall, architecture design of gunking zaki ne dake faman fesa ruwa daga bakinsa, ya wage baki sosai ruwa na zuba ta bakin nasa, a ƙasa an yi mashi round tamkar rijiya ruwan da yake zubarwa tana taruwa a wajen, daga can ƙasa akwai hanyar da ruwan yake sake komawa bakin zakin, ba karamin ƙara gyara gidan wannan design ɗin ya yi ba. Ga wasu shuke-shuken flowers a gefe guda da suka ƙarawa gidan haɗuwa. A gefen dama akwai guest suite, ɗakunan baki guda biyu tare da toilet da kayan more rayuwa a ciki. A gefen lambu akwai tangamemen garage na parkin motocin wanda tsab zai iya ɗauke motoci 30 ciff, gate na shiga garage ɗin automatic ne, da kansa yake buɗewa da rufewa, har yau akwai jiga-jigan motocin daddy guda biyar ciff a fake, tsadaddun motoci ne da suka haɗa da Maserati Levante Trofeo, Rolls-Royce Cullinan, Bugatti Chiron Super Sport, Mercedes-AMG G 63 sai wata mota mai tuƙa ƙanta, motocin dik an rufesu da car cover. Sannan akwai katafaren swimming pool a ta gefen ginin ba harabar gidan ba, a ɗan gefe aka ƙawata shi, yana ɗauke da sky blue ruwa mai balain kyau da ɗaukar hankali. A gefen pool akwai glass wall na tennis, basketball, filin wasanni na tennis da basketball har ma da football. A gaban zakin wani tampatsetsen baranda ne a wajen wanda babban parlo door yake kansa. Kai mu haura ground floor dan wlh ƙawartuwar harabar gidan nan ya zarce in iya faɗa maku shi lokaci guda, sai a hankali. Mu lula grand entrance hall, babban kofar shiga ground floor, kofar ya haɗu, ga kakkafar tsaro da idan ba mamallakan ginin ba babu wanda ya isa ƙetarawa izuwa ciki, ya fi kofofin CRYSTAL PALACE tsaro da amfani da kimiyar zamani. Kana shiga kofar akwai wani dogon corridor mai kyau wanda yake ɗauke da fitilar chandeliers a tsakiyar corridor ɗin daga sama, duk tsawon corridor din nan sai da chandeliers ɗin nan ya kusa kai ƙasa saboda tsawo da haɗuwarsa. Idan ka wuce corridor ɗin sai haɗaɗen automatic door, kana buɗesa da wani katafaren living room zaka fara cin karo, haɗuwar parlon nan ba zai faɗu ba, kusan za'a ce five in one ne parlon, dan haɗaɗɗun luntsuma-luntsumar sofa set kala biyar ne a cikin parlon, kowani set ya haɗu matuƙa. A cikin parlon akwai door da zai sadaku da tamgamemen mediterranean kitchen, kitchen ne mai siffa ra gargajiya, amma su gas na zamani ne a cikinsa, da alama daddy yana son gargajiya, dan a waje harahar gidan cikin wannan lambu akwai hut da aka ƙawata har guda uku, sai dai bukkar ba'a kewayesu da komai ba face glass, samansu kuma exactly bukar da ake yi a ƙauye, cikin bukkokin kuma haɗaɗu kujeru ne na zama dan shaƙatawa, to da alama yana ɗan son gargajiya. Iya wannan kitchen ɗin ne a ground floor, sai wani haɗaɗɗen butterfly stair case da ya yi sama izuwa first floor, nan ma akwai babban parlo two in one, sai master suite, katafaren ɗaki mai ɗauke da babban balcony da ke kallon wajen harabar gidan da sauran cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Sai katafaren toilet mai ƙunshe da jacuzzi da shower mai ban sha'awa. Bayan master suite akwai luxury bedrooms guda uku, ɗaya ɗakin yara ne, biyun kuma ɗaya na matar gida, ɗaya kuma babu kowa a ciki sai kayan alatu da aka zuba. Kowanne ɗaki na da toilet haɗaɗɗe da balcony, ga furnitures made in Dubai masu matuƙar kyau da tsada. Bayansu akwai dining hall, shi ma dik glass wall ne, daga parlon first floor ɗin kana hango cikin dining hall ɗin, katan table da haɗaɗɗun chairs guda 24 ne a ciki, sai show glass da ake zuba cups and plates a cikin dining hall ɗin, ga haɗaɗen decorations, and daga cikin dining hall ɗin kana iya hango wannan haɗaɗɗen lambun na waje mai ɗaukar hankali. A gefen ɗakin daddy Haiza'an akwai family lounge, wani ɗaki ne na taron iyali tare da TV mai faɗi da sofas masu taushi. To mu haura last floor muga me a ciki, ni fa ina son in ga na ɗauko maku abubuwan da cigabansa bai zo mana Naija ba, dan ni a tinanina da yadda na ɗauki rubuta littafi ana rubuce-rubuce ne dan ƙaruwar al'umma da wayar masu da kai game da basu ilmin da ALLAH ya hore maka wanda su basu sani ba........Kazalika kuma makaranta a tinanina kuna karance-karance ne dan ku samu ƙarin ilimi, so bai kamata ace kuna karanta abin da muke da shi a Naija ba, abin da already kun san shi sai dai ayi ta maimaitawa, shiyasa dik rubuce-rubucena yake ketarawa ƙasashe, mu zaƙulo abubuwan da baku sani ba dan ku sani ku kara samun ilmi, kunga ko baku je ƙasashe ba kun san me yake wajen, wannan shi ne kun yi karatu mai riba, kun kara samun ilmi!. Last floor. Tampatsetsen gym room ne a wajen da aka ƙawata shi dan motsa jiki tare da kayan zamani, sai haɗaɗɗen cinema room dan kallon fina-finai mai ɗauke da fitillun chandelier da kujeru masu taushi dan zaman kallon film da family. Baya ga shi akwai haɗaɗen roof terrace a saman, wani ƙaramin filin shakatawa ne, tare da barbecue station da kujerun hutawa. And daddy yana da home office na musamman dan aiki, tare da shelves da table na zamani....... A can sama kololuwa wajen sauƙar madaidaiciyar private jet ɗin daddy ne, akwai haɗaɗɗen jirgin da kowa zai yi mafarkin mallaka a wajen an faka shi, jikin jirgin ɗauke yake da sunan MUHAMMAD HAIZA'AN da harafin larabci To nifa my people wannan lambu na daddy ya tafi dani, dan haka ko aiki ne su Lion su ɗaukeni a wannan lambu, dan gaskiya ina son rayuwa a cikinsa, ya haɗu ne. Jama'a ALLAH ya mana arziki mai albarka, ya bamu lahira mai kyau, amma gaskiya zuciyar CRYSTAL PALACE ta haɗu, haɗuwa fiye da tinani. ------------------------ Kwance Lion yake a saman bed ɗin daddynsa a master room ɗinsa, ya tada kai da laps na wani kyakkyawan mutum wanda kana ganinsa kasan jininsu ne, dan akwai kamanni ta jini a tsakaninsu. Mutumin na sanye da tail coat a jikinsa, yana rike da hannun Lion ɗin, ɗayan hannunsa kuma yana shafa haɗaɗɗen golden hair ɗin Lion cikin tausasawa da nuna tsantsan kauna. Wannan mutumi ba kowa bane face Hussain ɗin daddynsu, ɗan biyun mahaifinsu wanda shi ya reni su Lion ɗin, da Lion ya shiga damuwa ne ya zo gidan daddyn nasa, sai ya ƙira uncle ɗin nasa kan ya zo su haɗu, kun san da cewa uncle ɓoye kansa yake yi? Baya son duniya ta san yana raye, yanzu haka duniya dik sun ɗauka ya mutu ne. To meyasa yake ɓoye kansa? Ya aikata wani laifi ne?. Muje zuwa alƙalamina zai amsa masu. "Zayra'an!". Daddy ya faɗa yana riƙo hannunsa a cikin nasa da kyau, shiru Lion bai amsa mashi ba, da alama ya yi barci. Ɗayan hannunsa daddy yasa yana ɗan shafa kansa a hankali, slowly ya ɗago idanu ya fara bin room ɗin da kallo, komai yana nan yadda yake, babu abin da aka taɓa face gyaran da ake yi wa komai. Lokaci guda daddy ya ji tamkar Hassan ɗinsa yana raye, idanunsa na mashi kizo lokacin da dad ɗin Lion ya tsaya a gaban parlo, yana ɗaura necktie a wuyansa, cike da tsantsar kaunansu yake cewa. "Hussain ka tashi ka bar mun gida, ka bar mun yara cikin kewa da kaɗaici, ka je na sallameka, kuma kada ka sake zuwa sai na nemeka"...... Mom Lion tana sauƙowa ta ce. "Zaka koran mun ƙani a kanka yake zaune ne?". "Tuba nike ranki ya daɗe". Dad ya faɗa yana miƙa mata hannu kan ta bashi wayansa dake hannunta......... Rintse idanu daddy ya yi, wani dogon numfashi ya ja game da sauƙewa a hankali, ya fama ciwon dake ransa na tina rayuwar baya. Dawo da kallonsa a kan kyakkyawan fuskan Lion dake ta zuba barci ya yi, cikin barcin ma sai sauƙe ajiyar zuciya yake yi alamar ya fara samun peace of mind, ALLAH sarki, idan ya tina rayuwar iyayensa in bai zo ya ga second daddyn nasa ba baya samun natsuwa, ganinsa kawai shi ne kwanciyar hankalinsa, shiyasa ya gudu ya bar su Aryan tin asuba. "Ina sonka sosai Zayra'an, ina sonka fiye da kaina, ba wanda nike gani in ji daɗin rayuwata face kai da ƴan uwanka, ina rokon ALLAH ya bani ikon cika alkawarin dana ɗaukarwa ɗan uwana na kula daku". Ɗan motsawa Lion ya yi, hakan yasa ya zame hannunsa daga cikin na daddy, ya gyara kwanciyansa da kyau, ya cigaba da barcin da bai samu damar yi daren jiya ba........ Sake riƙo hannunsa gam daddy ya yi tamkar ance za'a rabasu ne, ya yi shiru yana ta kallon fuskan Lion. Slowly ya jingina kansa da jikin headboard na gadon, ya ɗan lumshe idanu cike da tinanika kala-kala. Barcin good 2h Lion ya yi, daddy na zaune bai motsa ba gudun kada ya tashesa. A hankali ya waro idanunsa da suke jajir saboda barcin bata ishe shi ba. Kai tsaye sai kan fuskan daddy..... "Dad". Ya furta yana miƙewa zaune, kallon farko ya zaci dad ɗinsa ne ba daddy ba. Slowly daddy ya yo ƙasa da kai yana faɗin. "Ka tashi?". Kai ya ɗan jinjina game da cewa. "What says the time?"...... Laluɓo waya daddy ya yi, ya kunna light ɗin screen.......... 4:00 PM. Iska mai ɗimi daga bakinsa ya furzar game da miƙa hannu ya jawo nasa wayan. "Daddy let me call Aryan, nasan yanzu yana can ya damu da rashin sanin ina nike". Cikin zolaya daddy ya ce. "Sai yanzu ka tina da shi kaima ai"..... Shiru bai yi magana ba, ya fara laluɓar number Aryan, ya danna kira. Sai dai a lokacin dik suna barci a kan gadon Seraphina, wayar tana silent basu ji ma, message Lion ya rubuta mashi kan yana lafiya kuma yana dawowa yanzu. Wayoyinsu kusan a haɗe yake, sun saita shi ta yadda idan ya turawa ɗaya saƙo dikkansu saura ukun zasu samu saƙon. Yana tura masu ya zuro kyawawan kafafunsa ƙasan bed ɗin, jikinsa dik a mace ya miƙe tsaye, toilet ya nufa, da kallo uncle Hussain ya bisa har ya shige katafaren toilet ɗin daddynsa, ajiyar zuciya Uncle ya sauƙe game da gyarawa ya kwanta. After 2 hours, Lion ne tsaye a tsakiyar master room na daddyn nasa, yana sanya botiran tail coat na jikinsa, ya rabb, kayan sun zauna a jikinsa matuƙa, tamkar dan shi aka yi su, yai wa kaya mugun kyau, ya tara kitson kansa ya ɗaure, jade eyes ɗinsa sun ciza sosai, kyawawan soft lips ɗinsa sun ciza pink matuƙa, fuskansa ya yi very fresh sosai, ya ƙara kyau da cikar haiba da kamala. Uncle dake zaune a kan gado yana kallonsa ne ya ce. "Zayra'an please ka dawo gidan nan da zama, tsawon shekaru 10 kenan yanzu ina binka kaki yarda, meyasa baka son zama a nan ɗin?".. Shiru ya yi bai amsa ba, har Uncle Hussain ya fidda ran zai amsa mashi ma sai kuma ya ji in a low way ya ce. "Nothing, kawai bana son gidan ne". "Please, even because of Nirash, ku dawo ku raya gidan nan, ku sake raya ruhin Haiza'an ɗina, ku farfaɗo da gidan"....... Nan ma shiru for good 3 mins ya yi kafin ya ce. "Zaka dawo mu zauna a tare a nan ɗin?"....... Rass uncle Hussaini ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya daure da cewa. "Zan yi tinani, amma idan na aminta zan dawo mu zauna gabaɗaya zaka dawo?". Kai kawai ya jinjina ba tare da ya sake yin magana ba. Shiru uncle yai yana tinanin yadda zai dawo gidan su haɗe waje guda, da kuwa abin zai yi making sense. Katse mashi tinani Lion ya yi da cewa. "Bye uncle"....... "Bye my beloved son". ....... Daga haka bai sake magana ba ya fice waje, ya bar uncle, dik lokacin da yake so zai iya tafiya, shi dai ya koma benensu. Yana fitowa waje wasu karfin jami'an SSO suka nufosa da gudun gaske, hannu ya ɗaga masu tin ma basu ƙariso ba, baya son hayaniya da gayya, baya cikin wani good mood sosai. Sauƙowa kasar wannan baranta ya yi, ya nufi gate na fita, da kafa zai koma benensu ba sai ya ɗauki mota ba, dama da kafa ya zo. Kafin ya fito sai da ya sanya wannan haɗaɗɗen nose mask ɗin nasu a face ɗinsa, sannan ya fito ya nufi benensu, a cikin ransa yana jin kamar zai iya dawowa gidan nasu da zama. Dik in da ya zo ƙetarawa sai waɗan nan jiga-jigan jami'an sun kame tamkar basa numfashi sun sara mashi, bai ɗago ya kalli kowannensu ba, bai tanka kowannensu ba, ya wuce kai tsaye ya nufi benensu. ----------------------🔥 KHAIZA'ANS HOUSE. Sai da aka zubawa Rimsha ruwa 3 bottle kafin su samu kanta ta farfaɗo, da kuka ta farfaɗo tana faɗin. "Abba yanzu uncle Aryan ɗin ne mijina?".... A lokacin Abba baya kusa, sun baro room ɗinsa da ita, Faryan ya ɗauke zuwa room ɗin Ammie. Rungumota Ammie ta yi, ta hau rarrashinta tana bata baki, sai dai ina Rimsha taki yin shiru, in short sai da ta ɗauki kwanaki uku tana wannan kuka na ta shiga uku, dik Abba bai san tana yi ba, a rana ta huɗu ne ta kama Monday, a wannan ranar da asuba Faryan ya ce ta shirya ya kaita school. Jin cewa aurenta ba zai hanata school bane yasa ta ɗan saki jiki, burinta dik ta je makaranta su haɗu da Seraphina ta faɗa mata abin da aka yi mata, dik tayi sanyi baiwar ALLAH, daga umm sai uhm-uhm ta zama, bata hira, ta takura kanta sosai, amma yau da zata je school har da ɗan murmushinta. Ta shirya tsab cikin uniform ɗinta, har ta rame uniform ɗin yai mata yawa. Faryan na tsaye a parlo ta fito rike da rucksack ɗinta, karɓa mata ya yi yana faɗin. "Mu je in kaiki da wuri, Abba na jirana zamu je mu ɗauki amaryar Yah Harleen". Kallonsa ta yi, muryarta a dashe sosai ta ce. "ALLAH yasa tana da kirki"....... Da amin ya amsa game da riko hannunta, suka nufi waje yana kara yi mata nasiha, yana tausan zuciyarta, yana faɗa mata kalamai masu daɗi, yana tunatar da ita ALLAH ya ce Annabi ya ce, a haka suka nufi school ni kuma na nufi DOL kafin mu dawo mu bisu school ɗin. --------------------🔥 D-O-L Nutso take yi a cikin ruwan cike da farinciki, yana tsoma gashin kanta can kasan ruwa tana ɗagosa ruwan dake biyo gashin ya ƙara wanke mata fuska, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba. Shi kuwa tamkar gunkin da aka sassaƙa haka yake tsaye a cikin ruwan ware kitson kansa dan ya wanke golden hair ɗinsa. Tsoma kanta ta yi cikin ruwan tana ɗan juyawa, ɗagowa da zata yi tana faman yin sama da kanta sai ji ta yi........... Likes comments and share fisabilillah. ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️ QUEEN OF SURPRISE ✍️🔥 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 PRINCESS TEEMA A-K-A STAR LADY. For more information 08161390581 Whatsapp me only. STEP 1🔥 2025-12-23.🔥 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️ E_____________ 61 & 62 Tsoma kanta ta yi cikin ruwan tana ɗan juyawa, ɗagowa da zata yi tana faman yin sama da kanta sai ji ta yi ta bugi mutum, a razane ta ɗago kai tana ƙoƙarin sharce ruwan face ɗinta ta ga wanene?. A lokacin ya saki gashin kansa yana warware kitson kalba ɗin, hakan yasa gashin gabaɗaya ta rufe mashi fuska bata iya ganin wanene ba. Wani irin razana ta yi, dik tinaninta aljani ne, bare yadda gashinsa ya rufe mashi fuska, ya ALLAH. Wani irin dukan uku-uku kirjinta ya fara yi, baya-baya ta fara ja. Daidai lokacin ya ɗan motsa kaman zai juya kamar kuma zai yi gaba, hakan ba karamin razanata ya yi ba, ta zaci damketa zai yi, ai take numfashinta ya ɗauke, ta yi gamo da aljani a cikin ruwa. Sulalewa ta yi zata faɗa cikin ruwan, daga ta cikin ruwan yasa hannu ya riko waist ɗinta, da yake ta suma sai ta tafi gabaɗaya saman buɗaɗɗen kirjinsa. Hannu yasa ya tattare gashin dake

Chapter 77 of 95