Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Dedicated to all Aryan and Zayra'an fans.🫀♥️ E_____________ 59 & 60 DEATH OR LIFE. (DOL) Waɗan nan wasu magunguna ne da ake yi wa yara da sunan rigakafi, amma batu na gaskiya magunguna ne dake kashe garguwar jikin yara, tin yaro yana ƙarami zasu kashe mashi garkuwar jiki, hakan zai sanya jikinsa zata yi saurin karɓar kowacce irin cuta ce ta shigo, sannan jikinsa za yi wahalar karɓar magani. Kuga yaro yana ciwo ayi ta magani amma dik na banza, sai kuga kamar ba'a mashi komai, kuma ko sun girma jikinsu ba zai dinga karɓar magani ba, already an kashe masu garkuwar jiki tin suna yara, ba wanda zai zaci cewa maganin matsala ce, za'a ce rigakafi ne kawai, hmmmm bayan rigakafi babban cutarce a wajen. Al'ummar ƙasar Avaris sun gagara gane wani abu ɗaya, babu ta yadda za'ayi gwamnatinsu ta basu abu kyauta, kuma ta dinga binsu har gidaje da sunan yi masu, idan gaskiya ne a bisu gidaje ana raba masu kayan abinci da jari da ake cewa ana fitar masu mana, meyasa idan sun fitar da tallafin gwamnati sai dai su ce ka je ka cika form, ka bi layi, ka yi kaza, ka yi kaza?. Amma shi rigakafi za'a bisu har gida ne ana masu, har da rabawa yara sweet ko wani abin makamancin haka idan sun yi, kai mutanen cikin Avaris wani lokaci tamkar an toshe ƙwaƙwalwalensu, abin takaici sun kasa ganewa, wlh tallahi gwamnatinku ba zata taɓa binku in da kuke ta baku abin arziki ba, sai in cuta, cuta ce wannan za'a biku ko'ina a lallaɓaku, har kuɗi zasu raba maku dan ku yarda da su, da yake cutarku za'ayi, wlh dik wanda ya ci abin gwamnatin kyauta yasan akwai abin da zaka biya da shi, waɗan nan mutane nasa bada abu haka kawai, sai da babban dalili! Ku rubuta wannan ku ajiye. Ya rabb, ya ALLAH, ALLAH ka karkato da hankalin jama'ar annabi, ka ganar dasu! Musamman iyaye mata, sune ke bari anaiwa yara wannan gayyar tsiya, basu san cutar da rayuwar yaransu suke yi ba, da anyiwa yaro sau ɗaya shikenan an gama da garkuwar jikinsa, ya ALLAH ko shekara ɗari zai yi a duniya jikinsa ba zata dinga karɓar magani ba, sai dai ya samu sauki daga ALLAH, amma in bai da lafiya kun dinga kashe kuɗi a banza. Zubawa maganin idanu Leo ya yi, sai da ya karance rubutun jiki kaf, sun ɓoye ainahin manufar maganin da rubuce-rubuce na karya. Nisawa ya ɗan yi tare da zarar magani guda ya zura a cikin aljihunsa, ya sanya su Zaysh suka mayar da sauran a cikin kwali, da alama bincike zai yi a kan wanda ya ɗauka. Wucewa container gaba suka yi, a nan ma shi ya buɗe container. Ya rabb, Tramadol mai karfi sosai ne a cikin wannan container, waɗan da basu san me Tramadol ba, wani maganani ne da ake shigo da shi daga India, China, Pakistan, ana sayarwa da sunan maganin cuta, amma batu na gaskiya wannan magani yana haddasa lalacewar kwakwalwa, in kasha sosai yana sanya hauka, tashin hankali, mantuwa, ga sa jaraba sosai. Leo sai da ya ɗan girgiza ganin waɗan nan uban tulin kwalin Tramadol ɗin nan, katon container irin wannan cike da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buɗe container. Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al'umma ana kiransa da maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwandon sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fahimci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!. Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba. A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al'ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu, amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki. Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba ma a gwada su a asibiti ba, suna ɗauke da sinadarin da ke sa bugun zuciya su jawo bugun zuciya da sauri, mutuwar mazaje da yawa a sirrance ba tare da an san ainahin me ya kashesu ba, namiji zai mutu ba tare da yasan me ya kashesa ba, waɗan nan magunguna suna buɗe jijiyoyon namiji ne, ba karfi suke ƙara maka yadda kake tinani ba, buɗe jijiyoyinka suke yi, su bar iska ya shiga jikinka na wuce misali, su haifar maka da mutuwar gaba idan ka cigaba da sha, wlh suna sanya ciwon zuciya, saboda ita zuciyarka ba zata iya karɓar yadda jikinka zai buɗe lokaci guda ba, iskar dake shiga tana hura zuciyar take ta kumbura, idan namiji ya sha shi mai yawa a lokacin ma a take yake mutuwa. Sai ka ji masu sayarwa suna cewa baida side effects, sannu na ce, na ce sannu dan uban mutum!! Kai ni fa raina ɓaci yake in na ga ana cutar da bayin ALLAH, ina jin tamkar in zama namji irin sayyidina Ali!. Wannan magana ta maganin karfin maza ta tina mun da wani da ya mutu a hotel bayan shan man power, ya ALLAH, maza su yi ta mutuwa a rasa me yake kashesu, jahilan cikin al'umma su yi ta tallar man power ba tare da sanin ainahin dame ake yinsa ba, suna kashe al'umma cikin rashin sani da sunan wai su suna neman kuɗi. To hajiya Jummai, fatan idan kin gama karantawa in ma mijinki yana sha zaki taka mashi birki! Idan kinga wani naki zai sha ki taka mashi birki! Dan zallar cuta ce a ciki! Dan haka ki yi gaggawar takawa mijinki birki, ki tattara sauran power da kuke da shi ki kunshe mashi kayansa a wando! Idan kuwa kinƙi dakatar da shi to fa ɗan karfin da yake da shi ɗin zaku rasa, dan in yana da sauran shan ruwa a gaba bai mutu ba, to at the end abar tasa mutuwa zata yi ta daina aiki, kinga kuwa bai samu power ba wanda yake da shi kun rasata. Wata ma sai kuga ita ke sayawa mijin man power, su man power manya, zakuwa ki ga man power. Wlh mata tin wuri idan zaku tattara mazajenku ku turasu gudun motsa jiki da gym kullum dan su samo power ɗin asali is better for you, gym yana sanya jikin namiji ya yi karfi, dik wasu matattun jiyoyi zasu miƙe, yana ƙara girman gaban da kukewa haukar neman har kuke kai kanku ga halaƙar in da zaku rasa ɗan wanda kuke da shi. To maza, gym yana ƙara girman gaba da kuke so ɗin, ba sai kun sha man power ba zaku samu ingantaccen power da babu mix, sannan gym yana ware ƙasusuwan gaɓɓai yasa su yi kwari sosai, yana ƙara lafiya da daidaita zuciyar ɗan adam, kai in taƙaice maku kai da kanka in ka fara zaka ji jikinka ya canza, ya yi maka daɗi da sauransu. Mata ku tura mazanku gym ko dan su dinga ɗaukarku kamar ƴan baby suna jefawa gado kamar matan novel, da zarar yana gym komai girmanki zai ɗaukeki cak, to kashinsa ya yi kwari, amma yanzu kun kyalesa dik man gyaɗa da gishiri ya kashe dik wani karfin da yake da shi, ga wata musifa wai man power, ba dole a samu tangarɗa ba!. (Kuma mata masu shan hips and breasts enlargement yake kome? Ku jira, zan bangaɗo maku dame ake haɗasa, naku na nan tafe, ai nai alƙawarin sai fa na faɗi komai dake cutar da bayin ALLAH!) Container na gaba kuma maunguna ne irinsu diazepam, rohypnol, valium, magungunan bacci da kwantar da hankali a cewarsu, ana shigo da su da yawa ba bisa ƙa'ida ba, kuma ana bawa yara, mata, direbobi, musamman direbobi, za'a basu shi da sunan maganin hana barci, hakan na haifar da haɗasussuka a hanya, babban illar ce ga al'umma. Har kan Leo ya fara ciwo ganin waɗan nan ɓarna, amma ya daure suka je container na gaba. Suna buɗewa kwali-kwali na antibiotics ne a ciki, ana shigo da su suma ba bisa ƙaida ba, al'umma suna sha ba tare da sani ba. Kwayoyin suna cutar sosai, mutane su mutu cikin sauƙi, da ka yi zazzaɓi sai mutuwa. Time Leo ya duba a wayansa 2:30 ta yi. Cike da bada umarni ya ce su yi sauri gari ya kusa wayewa. Daga nan suka wuce container ta gaba. Suna buɗeta allurai ne dayawa a ciki, ai yana ɗaura idanunsa kan kwalaben alluran nan sai da ya ji gabansa ya faɗi. Soja da faɗuwar gaba ai kun san ba lafiya. Da yake basu da ishasshenlokaci a gurguje ya ɗauki alluran kwalba ɗaya ya zura a aljihunsa ya ce su mayar da saura su rufe tamkar ba'a taɓa taɓawa ba. Haka suka bi dik containers ɗin da suka buɗe, a kowani container sai Leo ya ɗauki abu ɗaya har suka isa kan miyagun kwayoyi, a nan ma ya ɗauki cocain ɗaya. Suka mayar da komai tamkar basu taɓa ba, sanna ya kwance karnikansa, ya ce Noor ya rike mashi ɗaya bari ya rike ɗaya, Noor ya ce. Shi wlh yana tsoron kare, basa haɗa hanya da kare, kada ku manta yana da cutar tsoro, tin ainahi haka yake da tsoron kare, kun gansa dai jarumi, wlh zai iya kama maciji, amma baya son kare ko kaɗan tamkar mai aljanu a kai. Miƙawa Zaynish igiyar karen Leo ya yi, ya karɓa ya rike, shi kuma ya riƙe ɗaya suka nufi hanyar komawa, yau ba barci akwai bincike kenan. Sun fara tafiya Vash ya karɓi igiyar karen hannun Leo dan ya taimaka mashi, saboda Leo ɗin ya fisu shan wahala, dik containers ɗin nan shi ya bubbuɗesu. Suna tafiya a hanya ne Vash ya ce. "Da mun cinnawa wajen wuta ai, komai ya ƙone su rasa shi"....... Nisawa Leo ya yi tare da cewa. "Ai bombing na wajen ba shi ne mafita ba, dakatar da masu aikata hakan ba shi ne ba, mu kama masu yi mu kashesu shi ne, idan har zaku rinƙa kama waɗan nan containers ɗin dik shime ne, in mun ƙona wasu waɗan nan yau, gobe zasu sake shigo da wasu, dan haka masu aikata hakan zamu raba da numfashinsu, shi ne ɓarna zata dakata!". Noor ya ce. "Gaskiya Avaris ta kai maƙura a wajen lalacewa"...... Leo ne ya amsa da. "A wannan case ɗin navy suna da babban kamisho, sun taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar ƙasar nan, kome za'a shigo da shi daga waje ta ruwa ne, me amfaninsu da ba zasu dakatar da ɓarna ba? Ko dai dama an ajiyesu a bakin ruwan ne dan su dinga kamun kifi ko suna zaman kirga jiragen ruwan da zasu shiga su fita?". Cike da takaici yai wannan magana, ya rasa meyasa yake jin tsananin kaunar kasar Avaris.... Ni kam na ce saboda ƙasar mahaifinka ne mana, ai jininka suna ciki, dole ka so ƙasar. Zaynish ne ya ce. "Amma idan navy suna da laifi kaso 40 cikin ɗari na lalacewar ƙasar to fa ministar of foreign affairs yana da kaso 55 cikin ɗari, ministan tsaro yana da 75 cikin ɗari, sai number ɗaya na ƙasan yana da 100 cikin 100!". Kai Leo ya jinjina, su Noor dik kai suka jinjina, a dake Leo ya ce. "Ni ban yarda wani soja ya bani umarni a kan rashin adalci in masa biyayya ba!"..... Dikkansu basu fahimcesa sosai ba, Vash ya ce. "Kana nufin ba zaka yi wa AZURE biyayya ba?". Kai ya jinjina. "Ba AZURE ba, dik duniya babu wanda ya isa in yi mashi biyayya kan cutar da al'umma! Wlh yadda na yi rantsuwa da ALLAH kafin in saka wannan kakin kan zan kare rayuka, dukiya, ƙasa bakiɗaya, to billahil lazi babu wani mahaluki da ya isa ya tilastani ya bani umarnin in yi shiru ana cutarwa! Sai dai a kasheni a kan haka, amma wlh dik masu ɓarna sai na dakatar da su, Navy sun yi alƙawarin kare bakin ruwa, ba zasu bar dik wata cutarwa ta ruwa ta shigo ƙasa ba, amma me muka kama yau? Ina suke da har suka bar hakan ke faruwa? Okey baa basu izini ba ko?". Cike da takaici ya kai karshen maganar. A yadda ya yi magana yasa su Zaynish sun ji lallai ko zasu mutu ba zasu marawa karya baya ba, lallai zasu aiki dan cika alƙawarin da suka ɗauka. Cike da taƙaici Zaynish ya ce. "Hakika ba zamu zama karnukan farautar manyanmu ba! Lallai ba zamu karɓi umarnin rufe bakinmu a lokacin da ake zalunci ba, ba shakka sai dai a kashemu amma a kan gaskiyanmu!!". Noor ya ce. "Dama ai mu mutuwa ba wata aba bace a wajenmu, sai da muka tabbatar cewa mutuwa ta fi takalmar sakawarmu sauƙi a wajenmu kafin mu yarda mu sanya wannan kaki, dan haka mu matattune dama, lallai zamu tsaya a kan gaskiya!". Vash ya ce. "Ba zamu taɓa bari a cigaba da cutar da al'umma ba, zamu zama sojoji na farko da suka fara gyarawa kowa zama a ƙasar nan!"....…. Leo ya ce. "Idan sun san wasu ai basu san wasu ba, ba zamu ki karɓar umarninsu ba, dan umarninsu doka ce, amma muna da damar yin abin da muke so a bayan idanunsu ba tare da sun sani ba ai, daga yau babu wani ɗan ta'adda da zamu sake kamawa mu mayar barrack, dik kashe shegu zaku yi". Zaynish da ya fito daga Afirka me bai sani ba? A ƙule ya ce. "Abinda ko mun sha wahala, mun je yaki, a yakin har mu rasa ƴan uwanmu sojoji, mu sha wahala mu kama ƴan ta'addan mun kaisu ma bayan kwanaki sakesu ake yi wahalarmu ta tashi a banza, dan haka ina tare da kai, dik a daji zamu kashesu kisa mafi walaƙanci, mu jefa gawarwakinsu cikin manyan tekuna, in mun koma mu ce dik sun gudu, that's all". Noor ya ce. "Wannan umarni da ƙananan sojoji basa samu yasa suke shan wahala, suna filin daka amma wai suna jiran manya daga sama su basu izinin harbi, sai su tsaya ayi ta harbinsu! Abin taƙaici, amma zamu gwada masu kwarewa a kan aiki, zamu canza hukumar soja na duniya bakiɗaya". Vash ne ya ce. "Ni wani kafurin ne ma ya kawo dokar idan kana filin daga ma sai ka nemi izinin harbi?"....... Zaynish ya ce. "Kafuran suna dayawa ai, amma zamu kafa tarihi a hukumar soja wanda ko mun mutu ƴan baya zasu yi amfani da salonmu, zamu canza hukumar soja a duniya bakiɗaya kamar yadda Noor ya ce, zamu bawa duniya mamaki, sai mun ɗara FIVE LION In Sha ALLAH". Leo ne ya ce. "FIVE LIONS, kai watau AZURE ta jima tana yaye gwarazan maza fa"......... Noor ne ya ce. "Ni fa ina ganin IRON FIST ma daga AZURE suka samu horo, dan wani lokaci aikinsu yana mun kama da namu fa".......... Vash ne ya amsa da. "Ban san meyasa nike son tarihin FIVE LIONS har cikin raina ba, sojojin da suka shiga tarihin duniya a lokacin baya, sojojin da suka bada mamaki". Leo ya ce. "Ina tinanin AZURE ta hora IRON FIST gaskiya, saboda nima irin aikin da suke yi yana bani mamaki, amma ni fa ina ji a jikina IRON FIST ba mugaye bane kamar yadda duniya ta ɗauka, kawai gwamnatin duniya ne ta nunasu matsayin azzalumai saboda suna rusa zaluncinsu"........ E mana, jama'a jinin IRON FIST yana magana, kaifin kwakwalwarsu gado ce, kun ji yana hasashen ba mugaye bane. Noor ya ce. "Ai manyan duniya zasu aikata fin haka ma, da zarar ra'ayinka ya sha banban da nasu to fa kai ne ɗan ta'adda kuma mugu, su kuma asalin ƴan ta'adda mugayen basa kiransu da hakan saboda ra'ayinsu iri ɗaya"...... Kai kawai Zaynish ya girgiza, daga nan bai sake yin magana ba, ya yi shiru, suka cigaba da hira suna tafiya, sai da suka kusa isa wajen tantunansu ne Noor ya ce. "Zaynish lafiya ka yi shiru?". Nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Babu komai bro". Noor bai yarda ba, ya matsa ya rike Zaynish tare da tsayar da shi suna fuskantar juna, suka dakata da tafiya, cike da kulawa ya ce. "Bro, now we're one family, bamu da iyaye da ƴan uwa a nan, bamu da kowa, why not ba zamu haɗa kanmu, mu rungumi juna ba?". Matsawa Vash ya yi, ya dafa kafaɗar Zaynish yana faɗin. "Ka faɗa mana damuwarka mu yi maganinta a tare"...... Baya Leo ya koma ya jingina da jikin wata bishiya yana kallonsu bai yi magana ba. Nisawa Zaynish ya yi kafin ya fara basu labarin yadda ƴan ta'adda suka kashe mashi dangi, iya shi da sister ɗinsa kawai suka rage, ya basu labarin komai bai rage ba. Sun yi matuƙar tausaya mashi, Noor ya rungumesa game da cewa. "As from today we're your family also, ba kai da Aunty Ummie bane kawai, akwai mu, we are brothers now! Zamu tsaya da kai dik wuya dik daɗi, promise that kaima kana tare damu"........ Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume Noor. "We're brothers now!". Matsawa Vash ma ya yi, suka rungumi juna. Shi dai Leo yana gefe yana kallonsu bai tanka ba....... Wani irin haushi karnukan hannunsu suka fara yi, hakan yasa Noor janye jikinsa a miliyan ya ja da baya, ya tsorata da kukan karen. Ɗago kai Leo ya yi yana faɗin. "Me yake damun karnikan?". Ya faɗa tare da kuna light ɗin hannunsa a kansu. Shiru Leo ya ɗan yi game da cewa su Noor su yi shiru, dan karnuka basa haushi banza, bare ma karnukan da aka baiwa horo irin wannan....... Tsit suka tsaya karnukan na cigaba da daka haushi. Lokacin guda cikin zafa Zaynish ya ture Leo tare da damke wukar da wani mutun ya zo ta baya zai daɓawa Leo ɗin. Take wuƙar ta fasa mashi tafin hannu dan bai sanya hand gloves ɗinsu na aiki ba, janye wuƙar baya mutumin ya yi, hakan yasa ta kara pasa tafin Zaynish. Kafin DOL su motsa sai ganin wasu jiga-jigan mutane huɗu suka yi sun bayyana kewaye da su, suna sanye da bakaken kaya na manyan ɓarayi, suna wani irin haki, da alama gudu sosai suka yi kafin su cim masu. Siririn tsaki Noor ya ja tare da cewa. "Ku zo da wuri mu baku a jikinku muna son komawa kafin gari ya waye"....... Zazzare wuƙaƙen hannunsu mutanen suka yi, miƙawa Vash igiyar karen hannunsa Zaynish ya yi, ya sanya hannu ya tsaga rigar jikinsa gida biyu, ya ɗaure hannunsa dake zubar da jini, har lokacin haske wata tamkar kamar rana yana haskasu. Komawa baya Vash ya yi ya jingina da jikin wani ƙaton dutse dake wajen, ya barwa mazajen AZURE filin su fafata shi kuma ya rike karnuka. Haɗe bayansu Zaynish, Noor and Leo suka yi suna kallon mutanen. Kansu mutane suka yi da wuƙaƙen, hakan yasa suka dare suka rabu. Wani irin faɗa suka fara gwabzawa na nuna banbanci kwarewa, sai dai sun yi mamaki ganin mutanen sun iya faɗa irin wanda ake koyawa sojoji. Mutane su huɗu, su kuma su uku haka suka fara gwabzawa. A tare mutane biyu suka yi kan Noor shi kaɗai, kaucewa wuƙar da suke ƙoƙarin caka mashi ya fara yi, while shi kuma Leo ya kwace wuƙar nasa mutumin ya jefar, sun fara faɗar hannu, wani punch Leo ya kai mashi a bayan kunne wanda yasa ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa. Ganin ya faɗi ne yasa ya daka tsalle, ya taka wani dutse dake kusa da Vash, ya ƙara tsalle game da juyawa ya daki ɗaya daga cikin masu kawowa Noor hari da wuƙa, a wuya ya dakesa da ƙafansa, sai ga mutumin ya faɗi ƙasa. Dafa shoulder ɗin Leo Noor ya yi, ya daka tsalle ya taƙa ɗayan mutumin a fuska da waɗan nan shaggun tauraran takalman nasu, baya-baya ya yi ya faɗi ƙasa. Dafe shoulder ɗin Noor Leo ma ya yi, ya daka tsalle tare da juyawa ya taka mutuminsa da ya taso yanzu yake ƙoƙarin nufosu, watau ya farfaɗo daga punch da ya sha...... Da karfi Leo ya riko waish ɗin Noor tare da ɗaga shi sama, Noor ɗin ya ware kafarsa ɗaya ya kaiwa mutumin da suke faɗa da Zaynish duka a gefen wuya, wannan duka ɗaya ba tashi Noor yai mashi, dan wannan shegen takalman nasu ya daki maƙogwaron mutumin wanda yasa ƙashin wajen ta ɓalle, kun san takalmansun nan ba karamar taurice da ita ba. Zaynish bai iya faɗa da mutumin sosai bane saboda yankar da suka mashi a hannu, so da hannu ɗaya yake faɗa shiyasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar ɗaga Noor ya daki mutumin. Yana sauke Noor ɗin ya yi tsale ya yi backtorn ya taka ɗayan mutumin da ya taso yanzu a kai sai da ya koma ya zube a ƙasa. Tsalle Noor ya yi ya taka tsakiyar bayan Leo dake duƙe, ya ware kafafunsa ya daki guy da ya sake miƙewa a ciki, hakan yasa guy ɗin ya sake komawa ƙasa, ya durƙusa kan gwiwinsa yana nishi sama-sama tamkar yana son sumewa ne. Dirowa ƙasa Noor ya yi, yana dirowa Leo ya miƙe tare da dafa shoulder ɗin Noor ɗin, ya daka tsalle tare da ware kafafunsa ya sake kaiwa guy ɗin dake durkushen wani mugun duka a gefen wuya da kafarsa, hakan yasa guy ɗin yanke jiki ya faɗi baya numfashi. Dirowa ƙasa Leo ya yi tare da fara karkaɗe hannunsa alamar sun gama da su dikka........ Vash ne ya cire bindigar dake wajensa yana faɗin. "Dik ku kashesu, ba za'a rasa mai sauran numfashi a cikinsu ba"........ Hannu Leo ya ɗaga masu game da cewa. "Ku kamasu mu koma da su sansani, ina zargin ta yadda aka yi suka iy faɗar sojoji, lallai ba ƴan ta'adda bane kawai!". Noor dake haki kaɗan-kaɗan ne ya ce. "Ina zargin navy ne!"...... A natse Zaynish ya amsa da. "Tabbas na zargi hakan nima"....... Vash ya ce. "Okey kenan Navy sun san da zaman filin da muka je yau kenan?". Leo dake ƙoƙarin zare belt na wandonsa ne ya amsa da. "Suna da sani mana, sun san komai, kawai sun mayar da kansu karnukan farautar manyan Avaris ne shiyasa basa ɗaukar mataki"..... Zaynish ya ce. "Okey, watau sun ga shigarmu wajen?"...... Kai Leo ya jinjina alamar yeah sun gani. Cike da takaici Zaysh ya ce. "Okey, Navy na gadin ɓarnar manya ƙasa ba wai su dakatar da ɓarnar ba, watau masu gadinsu suka mayar da jami'an?". Jinjina kai Leo ya yi alamar kwarai kuwa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina ake son ƴan Avaris su sanya ransu? A hukuma azzalumai, a shuwagabannin azzalumai, a makaranta azzalumai, a kasuwa azzalumai, a asibiti azzalumai, a koina azzalumai, ina suke son jama'a su sanya ransu? Wa suke son su kaiwa kukansu ya tsaya masu?".. A taƙaice Leo ya ce. "ALLAH, shi kaɗai zasu kaiwa kukansu kawai, amma basu da wata mafita, a ko'ina akwai gurɓatattu"....... Vash ya ce. "Basa tsoron mutuwa"........ Zaynish ya ja dogon tsaki game da cewa. "Sun manta akwai mutuwar ne ai, sun manta akwai ranar da zasu tsaya gaban ALLAH su zayyana dik abin da

Chapter 71 of 95